Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

Music:Abdul D One-Amarya

Sabuwar wakar Abdul d one wace yayiwa amarya
Wakar Aure kenan wace Abdul d one ya fara bugawa
Wakar gaskiya tayi dadi sosai inda acikinta zaku samu number Abdul d one.


A cikin wannan wakar ne akasa number mawaki Abdul d one sabi da masu bukatar a buga musu wakar aure.
To INA masoya Abdul D One ga dama tasamu kada kubari ta wuceku kuyi maza Ku dakko wannan wakar.



Read More »

NOBLE:AUREN FANSA!!! Na02

AUREN FANSA!!!
Na02
"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma
ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana
buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar,
idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan
kuma bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma
mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin
Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole
yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan
zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare,
gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce
d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito
parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani
American series, jin alamun shigowa yasa ta
kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera
yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa
tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa.
Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse
shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce
tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da
shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro
kaya."
Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi
yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun
rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai
kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma
bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa
basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi
don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in
nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai
na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana,
ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi
kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan
don ya fusata.
Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya
tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa
tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman
baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a
hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya
ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace
masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta.
Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai
lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office
d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko
yaji yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa
kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar
Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake
sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi
ya fice tare da sauran abokanan aikinsa
musulmai.
Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro
gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa
data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa
taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai
k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana
mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a
hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa
kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor
ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige
d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen
don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da
cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan
dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a
kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da
kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta
shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa
ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da
zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka
huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don
yaga lokacin sallar magriba ta gabato.
***
"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya
rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata
irin makekiyar kujera tana duba magazine da
glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga
ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya
haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta.
Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da
so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin
murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum
dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa
harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar
da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana
murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya
lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake
tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk
sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara
maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har
kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar
maka ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon,
kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana
doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa
sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo
muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah
wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce
fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban
goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da
larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna
Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara
fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi
kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...

Read More »

Kannywood: Rahama Sadau Tace Korarrata Da Akayi Ya Kaita Babban Matsayi A Duniya


Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta bayyana cewa korar da aka yi mata daga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ta daga ta zuwa mataki babba sannan kuma ta budo mata kofofi na alkairi.
Jarumar wacce ta bayyana haka a wata hira da tayi da jaridar Guardian inda ta bayyana cewa duk da dai abin bai yi mata dadi ma, hakan kuma ya kara haska ta a idon duniya.

“Kawai daga na taba wani a yayin gudanar da shiri sai ace na karya doka.
A tunanina koma mene kayi ai kai da ubangijin kane.
Duk abinda nake yi ai ina kokarin kiyaye hakkokin addinina da kuma al’adar yankin da na fito.
Saboda haka bana tunanin na cancanci hukuncin da aka yi mun a matsayin da nake.
Jarumar ta bada dan takaitaccen tarihin rayuwar ta ta baya inda ta bayyana cewar ta kasance tana sha’awa tare da yin rawa tun lokacin da take a matakin karatu na primary har ya zuwa matakin karatu na sakandire.
Ta kara da cewar ba’a irin kowanne film take fitowa ba inda ta bayyana cewar ta sha kin karbar roles da yawa da take ganin sun ci karo da al’adar yankin da ta fito.
Daga ciki akwai inda aka taba yi mata tayin ko zata iya fitowa a matsayin yar madigo(lesbian) wanda ita taki karba don kare mutuncinta.
An tambaye ta shin ko akwai bambanci a yanayin gudanar wasan kwaikwayo tsakanin Kannywood da Nollywood? Jarumar wacce ta fito a cikin wasu fina-finan Nollywood kamar su The Light Will Come, and Sons of the Caliphate.
Ta bayyana cewa kusan duk tsarin daya ne sai dai yan bambance-bambance da ba’a rasa ba ta bangaren al’ada da kuma yanayin mutanen gurin da ake gudanar da harkar wasan kwaikwayon.
Wannan shine dan abinda Arewamobile.com ta dan tsakuro muku daga cikin hirar da jaridar Guardian tayi da jaruma Rahama Sadau.
Read More »

Video: Akan Dalilin Dayasa Rarara Yayi Wakar – Malam Yaci Kudin Makamai

To dai nasan kowa yasan waye babban mawakin shiyasa Wanda akeji dashi a nageriya
Babban mawakin shiyasa dauda kahutu rarara Wanda kaf fadin kasar nan yayi fice a wakokin shiyasa
Wanda ya buga wakoki ba adadi na siyasa jam iyyu kala kala.


Inda mawakin kusan farkon hawan buhari ya dinga buga wakoki masu dadi da kuma aibata mutane.
Mawakin dai ya buga wata waka mai suna Malam Yaci Kudin Makamai Wanda kowa yake tunani ya bugata akan tsohon gomnan kano Malam Ibrahim Shekarau to ba haka abin yake ba
Tunda bashi kadaine malam ba acikin Wanda sukai handama da babakere akan kudin makamai Dan suna dayawa.
Ku sauke wannan bidiyon Dan Ku kalla.

                   DOWNLOAD VIDEO
Read More »

NOBLE:AUREN FANSA 01

AUREN FANSA 01

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM!
.
01
Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin
mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda
zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka,
don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma
tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka
fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga
bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar
tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa
cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye
6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali
har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke
kwance tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin
wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da
takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar
kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah
ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki
wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma
zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta
tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye
bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana
cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain
nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya
za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure
amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa
ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke
gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin
ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan
gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni
ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata
mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse
idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa,
tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma
yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin
haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin
kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba
Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai
hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce
sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka
zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole
sai kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya
baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har
akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa
da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya
cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki
idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai
baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata
yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa
sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba
tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi.
Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o,
kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta
ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na
manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa
nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe
amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare
shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya
kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake
Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi
murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta
gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga
d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.
D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana
fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi
kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo
parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon
tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas
sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu
a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka
har bacci ya sace sa.
Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da
ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm,
zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah,
bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin
Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya,
kiranta yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi
k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana
fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har
lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi
sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na
gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama
mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya
shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar
nauyi ya fice daga gidan.
Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce
gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina,
yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya
saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon
masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi
ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar
kullum sannan ta soko masa zancen da kullum
baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana
son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin
hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa
dai na k'asa.
Read More »

Notorious Female Armed Robbery Gang Leader Arrested In Imo State After Shoot Out With Police, One Dead

A famous armed robbery gang leader identified as Comfort Okon was arrested by the Imo State Police Command after a shootout with his gang who left one of her members dead.

Southeast News reports that Okon and his gang have been responsible for numerous robberies that have occurred in the state and other parts of southeastern Nigeria and have always escaped arrest for many years.

The post Notorious Female Armed Robbery Gang Leader Arrested In Imo State After Shoot Out With Police, One Dead (Photos) appeared first on Ngyab.

Get thousands of free final year project topics and materials sorted by subject to help with your research

Read More »

Rahama Sadau Ta Shiga Cikin Mata Uku Masu Tashe A Arewa


Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mata uku sa suka fi tashe a harkar fina-finai da nishadantarwa a yankin mu na arewacin Nigeria.

Jaridar Thisday ce dai ta wallafa sunaye gami da hotunan wadannan yan mata a shafinsu na instagram inda suka ayyana su a matsayin manya mata kuma masu tashe a bangaren nishadantarwa a arewa.

Wadannan shahararrun mata dai sune babbar mawakiyar nan Hadiza Blell wacce aka fi sani da suna Dija. Da kuma fitacciyar mai gabatar da shiri a gidan television wato Salma Phillips. Sai kuma jarumar wasan kwaikwayon Hausa Rahama Sadau.


Read More »

VIDEO : Korede Bello – My People Ft . Lil Kesh

VIDEO: Korede Bello – My People Ft. Lil Kesh
Korede Bello is here with another dope track titled My People featuring Lil Kesh. Along with the visual.
Enjoy!
Song Artiste

Song Title.                 Korede Bello – My
People Ft. Lil Kesh



Download Video Here
Read More »

Sabon Video : - Rahama Sadau Anrun Gumeta “A Cikin Film Din Day 1”

Wanna Ba Gaskiya Bane ‘Yan Uwa Duk A Cikin Film Ne, Yadda Suke Shiryar Da Film Kuma Idan Ka Duba Zakaga Jama’a Ke Kewaye Da Su.
Dan Allaj Jama’a Mu Daina Daukan Kita Jita Mutsaya Mufahimci Lamari Kamun Ka Aiwata.
Toh Jama’a Adade Anayi Sai Gaskiya Inji “Rahama Sadau ” A Cewarta Itafa Duk Masu Ce Ce Kuce Suyi Tayi, Muddin Ita Kan Gaskiyarta Take Wannan Sana”a Film Ba Wai Iskanci Takeyiba.



Haka Kuma Ta Kara Da Cewa ita Tanayin Nollywood Ne Don Sha’awa Ba Don Wani Abu Da Jama’a Ke Cece Kuce Akai Ba. Domin Idan Mutun Yace Ya Biye Jama’a To Hatta Kansa Bazai Mora Ba,
Wannan Shine Dan Gajeren Zance Daga Jarumar ‘Rahama Sadau’ Ku Dannah Kan Download Below Domin Sauke Video Zuwa Kan Wayoyin Ku.

     DOWNLOAD VIDEO HERE
Read More »

Kannywood: Yadda harkar fim ta maida ni mutunniyar kirki - Jaruma Halima Ibrahim

Dama dai masu iya magana sun ce abincin wani, gubar wani. Yayin da jama'a da dama ke ikirarin cewa harkar fina-finan Hausa ba abunda suke jazawa al'ummar Hausawa sai lalacewar tarbiyya, daya daga cikin jaruman mai suna Halima Ibrahim ta ce kwata-kwata ba haka bane.

Jaruma Halima Ibrahim a cikin wata fira da tayi da majiyar mu ta bayyana cewa ita dai kam harkar fim ma gyara mata tarbiyya tayi ta kuma maida ta mutunniyar kirki.


Jarumar da ta bayyana cewa yanzu haka ta fito a fina-finai akalla 20 ta kuma ce harkar fim itace ta koya mata hakuri, zama da mutane, da kuma kai zuciya ne sa da a da bata da su.

Jaruma Halima Ibrahim ta ci gaba da cewa ita yanzu har iyayen ta ma dai mamakin kyawawan halayen ta suke yi tun bayan shigar ta harkar fim din gadan-gadan.

Tun farko dai jarumar ta bayyana cewa ta dade tana sha'awar harkar ta fina-finan tun tana karama amma bata fito ta fadawa iyayen ta ba sai da ta kammala karatun ta na Digiri a jami'a.
Read More »