Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NOBLE:AUREN FANSA!!! Na02

AUREN FANSA!!!
Na02
"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma
ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana
buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar,
idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan
kuma bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma
mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin
Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole
yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan
zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare,
gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce
d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito
parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani
American series, jin alamun shigowa yasa ta
kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera
yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa
tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa.
Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse
shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce
tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da
shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro
kaya."
Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi
yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun
rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai
kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma
bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa
basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi
don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in
nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai
na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana,
ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi
kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan
don ya fusata.
Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya
tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa
tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman
baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a
hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya
ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace
masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta.
Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai
lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office
d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko
yaji yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa
kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar
Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake
sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi
ya fice tare da sauran abokanan aikinsa
musulmai.
Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro
gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa
data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa
taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai
k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana
mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a
hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa
kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor
ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige
d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen
don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da
cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan
dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a
kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da
kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta
shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa
ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da
zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka
huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don
yaga lokacin sallar magriba ta gabato.
***
"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya
rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata
irin makekiyar kujera tana duba magazine da
glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga
ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya
haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta.
Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da
so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin
murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum
dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa
harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar
da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana
murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya
lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake
tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk
sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara
maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har
kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar
maka ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon,
kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana
doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa
sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo
muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah
wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce
fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban
goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da
larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna
Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara
fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi
kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...

No comments

Post a Comment