Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

Rahama Sadau Ta Shiga Cikin Mata Uku Masu Tashe A Arewa


Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mata uku sa suka fi tashe a harkar fina-finai da nishadantarwa a yankin mu na arewacin Nigeria.

Jaridar Thisday ce dai ta wallafa sunaye gami da hotunan wadannan yan mata a shafinsu na instagram inda suka ayyana su a matsayin manya mata kuma masu tashe a bangaren nishadantarwa a arewa.

Wadannan shahararrun mata dai sune babbar mawakiyar nan Hadiza Blell wacce aka fi sani da suna Dija. Da kuma fitacciyar mai gabatar da shiri a gidan television wato Salma Phillips. Sai kuma jarumar wasan kwaikwayon Hausa Rahama Sadau.


No comments

Post a Comment