Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NOBLE:AUREN FANSA 01

AUREN FANSA 01

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM!
.
01
Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin
mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda
zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka,
don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma
tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka
fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga
bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar
tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa
cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye
6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali
har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke
kwance tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin
wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da
takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar
kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah
ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki
wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma
zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta
tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye
bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana
cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain
nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya
za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure
amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa
ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke
gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin
ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan
gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni
ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata
mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse
idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa,
tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma
yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin
haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin
kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba
Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai
hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce
sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka
zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole
sai kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya
baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har
akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa
da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya
cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki
idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai
baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata
yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa
sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba
tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi.
Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o,
kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta
ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na
manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa
nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe
amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare
shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya
kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake
Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi
murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta
gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga
d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.
D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana
fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi
kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo
parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon
tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas
sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu
a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka
har bacci ya sace sa.
Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da
ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm,
zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah,
bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin
Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya,
kiranta yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi
k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana
fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har
lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi
sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na
gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama
mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya
shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar
nauyi ya fice daga gidan.
Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce
gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina,
yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya
saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon
masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi
ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar
kullum sannan ta soko masa zancen da kullum
baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana
son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin
hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa
dai na k'asa.

No comments

Post a Comment