Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

Kannyood: Na shiga harkar fim ne domin wa’azi da fadakarwa – Inji sabuwar jaruma Amina Yola

Wata sabuwar fuska da ta bulla a masana’antar
Kannywood na fina-finan Hausa mai suna Amina Yola ta
bayyana sha’awar yin wa’azi da kuma fadakarwa ga
al’umma a matsayin muhimman dalilan da suka sa ta
tsunduma a harkar fim gadan-gadan.


Jarumar ta bayyana cewa ta dade tana muradin ganin
yadda zata iya bayar da tata gudummuwa ga cigaban
al’umma musamman yadda ta ke ganin yan fim din na yi
tun tana yarinya.
Matashiyar sabuwar fuskar ta bayyana cewa bata shiga
harkar fim ba sai da ta samu izinin yin hakan daga wajen
iyayenta, inda kuma ta kara da cewa harkar fim din harka
ce da ke da bukatar hakuri musamman ganin cewar ana
mu’amala da mutane da dama.
Haka ma dai jarumar ta bayyana shararriyar jaruma
Hadiza Gabon a matsayin wadda take so ta kwaikwaya
sannan kuma tace yanzu haka abun da ta sa a gaba
kenan.

No comments

Post a Comment