Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NE... PART (5)

Sakamakon kwanciya da tunanin Fatima da nayi a wannan
dare saida nayi mafarkinta, a cikin mafarkin nawa ne na
ganni tare da ita muna ta hirar soyayya, hakadai nayi tayi
har gari ya waye ban saniba, saida rana ta fito sannan na
farka daga baccin da nake.
In takaice muku haka muka shafe kwanaki da Fatima a
kullum sai ta kirani da safe da dare, bayan haka kullum sai
ta sakamin katin kira a wayata, idan na hanata sai tace to
amma har gobe ba zata fasa ba, hakan ya kara jefani cikin
tunani da kuma zargi a zuciyata, saboda haka sai na yanke
shawarar mu daina waya da Fatima, amma abin ya gagara.
Wata rana da safiya muna magana da Fatima sai naji wani
na mata magana cikin fada, sannan naji an katse kiran,
daga wannan rana lambar Fatima bata kara shiga ba, idan
na kira sai naji wayar a kashe, cikin yan kwanaki na fara
ramewa saboda na kamu da soyayyar Fatima wanda ni
kaina bansan lokacin ba.
Lokacin da nakai tsawon kwanaki bakwai banji muryar
Fatima ba sai na fara rashin lafiya, amma har zuwa
wannan lokaci ba wanda yasan me ke faruwa, inanan
kwance da bayan sallar la'asar ne naji wayata na ringing,
da na duba sai naga sabuwar lamba ake kirana da ita, na
daga wayar a hankali sannan na kara a kunne na.
Muryar Fatima naji tana kuka tare da cewa 'zuciyata na
cikin wani hali, rayuwata na cikin wahala, rashinka a gareni
tamkar ajaline a wajena, rashin jin muryarka kan sakani a
damuwa maras misaltuwa, yaya Abba inaso ka tabbatarmin
da cewa kanasona ta hanyar zuwa gidanmu gobe ban
yarda ka haura ba' kafin na yi wata magana tuni Fatima ta
fashe da kuka tare da kashe kiran.
A lokacin ne naji wani abu ya soki zuciyata, bansan lokacin
da na tashi na zauna ba, duk wani rashin lafiya da ke
damuna naji babu, sannan na fada kogin tunani, a sannan
ne na fara shirin zuwa garin Gashua, dake Jahar Yobe gobe
domin ganin wadda zata yayemin duk bakin cikina.


No comments

Post a Comment