Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NOBLE'S:AUREN FANSA!!! NA 3

AUREN FANSA!!!
NA
03
***
Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da
maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi
6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna
mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya
dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya
amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma
cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe
idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin
hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in
wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My
sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a
lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka
yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka
amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira
ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa
kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan
na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai
ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi
min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan
raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici
yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne
kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har
ma ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu
haka ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu
sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann
ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata
tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike
buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na
bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a
siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi
sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da
d'an uwanshi.
Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya,
bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa
bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi
Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan
ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa
suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina
kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna
tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba
su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta
da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure
ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba.
Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah
ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba
haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa,
bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke
cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!
***
BAYAN 'YAN KWANAKI
Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka
yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da
Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita
unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A
hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke
su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky
doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an
mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta
yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini
ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta
zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki
tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa
masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai!
Kuma ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta
taka duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu
saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an
fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki
wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in
magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu
kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i
gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita
bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To
mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara
na gaji da zama da mace irinki wadda batasan
inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina
tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura
taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni
kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on
da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar
anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko
kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta
zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe
ta!!!"
                   

No comments

Post a Comment