Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NEH... PART (10)

A ranar dana cika kwana 2 a gidansu Fatima ne da safe
mahaifin Fatima ya saka Fatima da tazo ta kirani yanason
ganina, Fatima tazo ta sameni a masaukina ta sanar dani
cewa mahaifinta nason ganina yanzu, na amsa mata
sannan na tashi muka fito tare da ita muka taras da
mahaifin nata a falo yana zaune, Fatima ta shige cikin
dakinta nikuma na zauna daga gefe sannan na gaishe da
shi.
Bayan mun gama gaisawa ne ya danyi shiru zuwa wani
lokaci sannan ya dubeni yace dani 'malam Abba kana
wanne sana a ne?' na amsa masa da cewar a halin yanzu
bani da sana ar da nakeyi, ya danyi shiru sannan ya cemin
nagama karatu? Na amsa masa da cewar a'ah ina shekarar
karshe ta gama degree na watoh part 4 a Federal University
na garin nan amma kafin nan nayi diplomar computer a
College of Legal dake garin Nguru jahar nan ta Yobe, ya
cemin a gaskiya bazai bani auren yarsa ba indai har bana
wata sana'a, amma ya sanar dani cewa naje na kawo masa
takardu na na diplomar kafin na kammala degree nawa,
hakadai muka rabu akan zanje na kawo masa takarduna na
diplomar sannan nayi sallama dashi akan cewa zan koma
gida yau, ya kawo dubu goma yabani yace nayi kudin mota
dashi sannan ya kira Fatima domin tayimin rakiya zuwa
wajen da zan hau mota.
Haka muka fito nida Fatima muna hira, na sanar da ita
abinda mahaifinta ya sanar dani, Fatima tayi murna da
hakan har mukaje inda zamu rabu, bisa mamaki sai naga
Fatima na zubar da hawaye, cikin matukar damuwa nace
da ita 'Fatima menene dalilin da yasaki zub da hawaye
haka?' Fatima ta sa hannunta ta share hawayen dake
idanunta sannan ta kalleni tace dani 'yaya Abba a koda
yaushe kallonka ken debemin kewa maganganunka na
karamin kwarin gwiwa jin muryarka kan yayemin duk bakin
ciki na idan ina tare dakai nakan manta da duk wata
damuwa a zuciyata, amma sai gashi yau zamu rabu zaka
tafi ka barni cikin kadaici yaya Abba meyasa bazan zub da
hawaye ba?'
Cikin tausayi na dubi Fatima nace da ita 'Fatima kiyi hakuri
ki daina hawaye domin hakan na jefani cikin matukar
damuwa, ki sani cewa wannan rabuwar da zamuyi bawai
tana nufin mutuwa bane, sannan ki tuna da cewa watarana
saidai mu zauna dake zaman da rabuwarmu saidai mutuwa,
Fatima ki share hawayenki ki daina kuka, haka dai nai
tayiwa Fatima kalaman da zasu kwantar mata da hankali
har dai mukai sallama da ita muka rabu, sannan naje na
shiga mota ina ta tunanin Fatima.
A wannan rana sai da yamma ne na isa gida wanda kuma a
wannan rana ne na sanar da mahaifiyata duka abinda ya
faru tsakanina da Fatima, da farko ta nunamin damuwarta
a game da hakan amma daga bisani na rika kwantar mata
da hankalinta har ta amince da maganar.


No comments

Post a Comment