Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

Nigeria: ''Muna cikin wani hali a sansanin Bakassi''

Kun san halin da 'yan gudun hijirar Najeriya
a Bakassi ke ciki?


Wasu 'yan Najeriya fiye da 300 na can suna zaman gudun
hijira cikin wani yanayi da suka ce mawuyaci ne a jihar
Kuros Ribas, a yanzu haka.
Sun samu kansu a cikin irin wannan hali ne bayan da suka
tsere da kyar daga tsibirin na Bakassi , wanda Najeriyar ta
mika wa kasar Kamaru a shekarun baya.
Masu gudun hijirar dai sun yi zargin cewa an kashe
wasunsu da dama da suka hada da maza da mata, kuma
an lalata masu gidaje da kadarori masu dimbin yawa a wani
hari da jami'an tsaron kasar ta Kamaru suka kai masu.
Hakan ta wakana ne ga resu sakamakon rashin biyan wani
haraji da suka ce an tsawwala masu.
Wata 'yar gudun hijirar mai suna Mary Joseph da ta zo da
tsohon ciki, ta shaida wa BBC cewa a yanzu tana da 'ya 'ya
10.
To sai dai har zuwa yanzu bata da kome a hannunta.
Mata da dama ne ke ta haihuwa a wannan sansani ba tare
da wata kulawar da ta dace ba.
'' Hatta ruwan sha babu ballantana maganar abinci, babu
kuma kudin saye''.
Mr Linus Asuko masunci ne kuma daya daga cikin 'yan
gudun hijirar ya bayyana cewa yanzu ba su da komai, ga
shi kuma gwamnatin Nijeriya ba ta yi musu komai ba,
mutane na mutuwa.
Ya kuma ce '' Muna bukatar agajin gaggawa, muna bukatar
tabarmi, da abinci, da magunguna, da gidan sauro, da
kayan abinci, sannna a taimaka wa matan da ke haihuwa a
wannan sansani.
Yan gudun hijira dai na fuskantar matsaloli daban-daban da
suka hada da na rashin kudaden biyan bukatunsu, da
wuraren kwanciya, da abinci da magunguna.
Sai dai hukumomi a jihar ta Kuros Ribas sun ce suna
kokarin tantance 'yan gudun hijirar, da matsalolinsu, ta
yadda nan ba da jimawa ba za a taimaka musu.

No comments

Post a Comment