Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NEH... PART (2)

Na danna maballin kira na wayata na daga kiran sannan na
kara wayar a kunne na, sai naji ance dani 'dan allah ina
magana ne da Abba?' mamaki ya kamani na amsa mata da
cewa eh shine sannan taci gaba da cewa 'tun daga lokacin
da na kalli hotonka naji kaunarka ta cikimin zuciyata, na
kasance kullum cikin begenka, hotonka ya kasance abin
kallona a koda yaushe, sai gashi kuma idan namaka
message a facebook chat naka baka mini reply, hakane ya
hanani sukuni na tsawon lokaci wanda har ta kai jiya da
dare na kasa barci saboda tunaninka, hakan ne yasa na
kasa jurewa har na kiraka a wannan lokaci domin na sanar
dakai abinda ke cikin zuciyata'.
A lokacin ne naji wani abu ya soki zuciyata wanda na kasa
gane menene, nayi shiru na dan lokaci, sannan nace da ita,
'naji duka uzirin ki, amma kiyi tunani cewa nifa sunanki
kawai na sani, ban taba ganinki ba sannan ban san inda
kike ba kuma nasan kema hakan ne, amma ya za'ai ki
tunkare ni da batun soyayya?'
Fatima ta danyi murmushi sannan cikin wata sassanyar
murya tace dani, 'yaya Abba ni ban damu da duk inda kake
ba, nidai burina ka amince da soyayyata, wallahi idan kaki
karbar soyayya ta zan fada mawuyacin hali, hotona kuma
zan turo maka tare da addrees nawa'
Na sake yin shiru ina tunani sannan nace da ita 'shikenan
zanyi tunani akai', haka mukai sallama da Fatima sannan
na kashe kira, na ajiye wayar a gefena sannan na zauna na
fara tunani a zuciyata ina jin abin kamar mafarki.
Karar message ne yasa na dawo dani daga dogon tunanin
da na fada, sannan na duba wayata sai naga message
guda biyu, na tsaya ina kallon wayar cikin sanyin jiki
sannan na saka hannuna na bude message na farko.

No comments

Post a Comment