Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NEH... PART (6)

Wahe gari da sassafe na tashi sannan na shirya kayana set
2 a cikin karamar jaka ta, nayi sallama da iyayena akan
zanyi tafiya, amma ban fadi gaskiyar wajen da zanjeni ba,
karfe goma na safiya motarmu ta tashi zuwa garin Gashua.
Da misalin karfe daya na rana na sauka a garin Gashua,
sannan na hau mashin ya kaini anguwarsu Sabon Gari
kamar yadda Fatima ta sanar dani, a nan kofar gidansu aka
saukeni, wanda a nan take naji wani tsoro ya cika zuciya ta,
sannan naji karaya a zuciya ta akan soyayyata da Fatima,
ba komaine ya jawo hakan ba sai yanayin gidan su da na
gani, gidan ya kasance babba ne wanda kana ganinsa kaga
gidan da arziki ya zauna, nayi duba naga cewar duk layin
ba gidan da ya kaishi kayatuwa, hakan ne yasa na ji tsoro
ya sake baibayeni wanda ban san na menene ba.
Ina tsaye a wajen ina tunani saida na shafe a kalla yakai
mintuna goma, a lokacin ne na dauki wayata na kira Fatima
a tsohuwar lambarta da na sani sai naji wayar a rufe, hakan
yasa na sake fadawa cikin wata damuwa, sai na sake kiran
wayar da ta kirani da ita jiya, itama sai naji wayar a rufe,
nanfa na tsaya ina tunanin abin yi, wata zuciyar na cemin
na hakura kawai na koma gida, amma hakan nake ganin
bazan iya ba domin ko wacce irin wahala zansha sai naga
Fatima.
A daidai wannan lokacin ne na tunkari kofar gidan kai tsaye
tare da cire duk wata fargaba daga cikin zuciyata, ina zuwa
kofar giddan na buga a hankali, sai naga mai gadi ya bude
ya leko, yana ganina yace dani ya akai? Nace masa nazo
wajen Fatima ne, sai yace dani wanene kai kuma menene ya
kawoka wajenta, kafin na kara wata magana sai naji
muryar Fatima tana cewa 'bako na ne ka bude masa kofa
ya shigo' mai gadi ya amsa mata ''to ranki ya dade''
Alokacin ne na tsaya ina kallon Fatima ko kau da idona
banayi, sai da ta kalleni tace dani 'barka da zuwa ya
masoyina abin kaunata, nasan kasha wahalar hanya yanzu
ka shigo ka huta'
Muka shiga ta kaini wani bangare daban na cikin gidan
wanda dama anyishi ne saboda baki, ta je ta kawomin ruwa
na roba sannan da kayan marmari kala-kala, har zuwa
wannan lokaci nidai ban mata magana ba, bayan na dan
sha ruwa kadan muka zauna da ita muka fara hira irin ta
masoyan juna, ana cikin haka ne sai ga mahaifin Fatima ya
shigo....


No comments

Post a Comment