Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NEH... PART (7)

Da shigowar mahaifin Fatima na durkusa na gaishe dashi,
ya amsa sannan ya dubi Fatima yace da ita wanene
wannan? Fatima ta amsa masa da cewa 'bako na ne daga
Damaturu' mahaifin Fatima ya sake kallona da wani irin
kallo mai dauke da alamar tambaya sannan ya kalli Fatima
yace da ita 'ki sameni a cikin gida' ta amsa da 'to' sannan
ya fita ya barmu a zaune da ita, nan dai mukai shiru ni da
Fatima har tsawon dakika tamanin babu wanda ya kara ma
wani magana, a wannan lokacin ne Fatima ta tashi ta shiga
cikin gida domin amsa kiran nasa.
Da shigar ta ta taras da mahaifin nata tare da mahaifiyarta
a zaune a falo, shikuma mahaifin nata yana tsaye cikin
fushi ya dubi Fatima yace da ita 'a matsayina na mahaifinki
na zabar miki mijin aure kin ce bakisonsa, na barki akan
cewa ki kawomin wanda kikeso kuma kinje kin kawomin
wani kaskantacce wanda bashi da komai bashi da sana'a
kicemin shi zaki aura ko, to inaso ki sani indai har ina raye
to bazan taba bari ki aureshi ba' Fatima ta fashe da kuka
tare da fadawa kan mahaifiyarta tana cewar 'indai ba ta
sameni a matsayin mijinta to saidai wani ya auri gawar ta'.
Mahaifin Fatima yasa aka kirani wajen sannan ya dubeni ya
mikomin wata takarda tare da cewa 'wannan check ne na
banki kaje ka rubuta duk adadin kudin da kakeso ka cire
amma inaso kada ka sake kula 'ya ta da maganar
soyayya'.
Na sunkuyar da kaina kasa sannan na dago a lokacin da
hawaye ke zuba a ido na nace dashi 'kayi hakuri indai akan
wannan maganar ne na hakura zan rabu da 'yar ka kuma in
sha allahu bazaka sake ganina a gidanka ba, kudi kuma ka
bar abinka nagode' nan take na tashi na dauki kayana na
fito daga gidansu Fatima idona cike da kwalla, zuciyata cike
da tunani da bakin cikin rabuwa da Fatima,
Da fitowata ban zame ko ina ba sai tashar mota anan naje
domin shiga mota zuwa Damaturu, a cikin dare na sauka a
cikin Damaturu na karasa gida naje na kwanta domin na
danyi barci amma sai abin ya gagara, haka nayi ta tunanin
Fatima har gari ya waye ban ko rintsa ba sai hawaye ke ta
fita daga idanuna.


No comments

Post a Comment