Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

SO NE... PART (1)
karar ringtone din waya na da ya cikamin kunne da kara
shine ya tasheni daga baccin da nake, nayi salati ga
fiyayyen halitta, sannan na tashi daga kwance na zauna,
sannan na mika hannuna a hankali na dauko waya na da
nufin na daga kiran da akemin, a lokacin ne kiran ya katse,
ban tsaya duba missed call din ba na ajiye wayar sannan
na tashi na fita daga daki naje nayi alwala sannan na dawo
na tayar da sallah.�Raka'a ta biyu da fara sallah wayata ta
sake daukar ringtone alamar ana kirana a wayar,wanda
bayan katsewar kiran ne bata kara ring ba har na idar da
sallah sannan nayi addu'o'i na shafa fatiha, a sannan ne na
mike naje na dauki wayar tawa sannan na duba missed call
domin naga wanene mai kirana da wannan sanyin
safiya.�Sabuwar lamba na gani wadda a iya tunanina ban
gane lambar ba, nan fa na fara tunanin wanene wannan mai
kiran da har yamin missed call guda 5, amsar da na kasa
baiwa kaina kenan, sannan na fara kokarin kiran lambar,
kirana ke da wuya naji ta shiga tana ring, sai da ta dan jima
sannan naji an daga kiran. �Shiru naji na dan lokaci ba
aimin magana ba, sai na fara yin sallama, da wata
sassanyar murya mai dadin sauraro naji an amsamin
sallamar tare da fadin ka tashi lafiya, cikin sanyin jiki na
amsa lafiya kalau sannan na tambaya wane ke kira? Sai
tace Fatima ce yaya ka kashe wayar zan kiraka domin inada
wata magana ne dakai, na amsa mata cikin sanyin jiki da
cewa to.�Na kashe kiran sannan na fara wani karamin
tunani a cikin zuciya ta, WACECE WANNAN ? amsar da na
gagara baiwa kaina kenan ina ta sakar zuci har ta sake
kirana, naji wayata na ringing.

No comments

Post a Comment