Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLES

*** ETRAT PART FIVE (5)***
.
Lallai abinda najiyo gaskiyane aure za'amun tabbb...!! da wannan mishkilin mutum wanda ko gaisuwa bai iyaba za'ahadani aure, naja baya nakoma d'aki na fashe da kuka, ni wllhy bana son wannan mutumin gara Mahbuub sau dubu akanshi, nifa gaskiya bana sonshi, dayar zuciyar ai kya bari har amiki maganar aure sannan ki ce bakya sonsa idan aka ganki kina kuka mi zakice? wato labal kikayi kikaji sirrin iyayenki ko? nan take nay shuru kar asirina ya tonu haka naje nakwanta.... Da safeee natashi bayan nayi break fast baba ya ce yanada magana dani, nan gabana yafadi nasan cewa maganarce, haka jiki ba k'wari naje pallon Baba natararda Mama agun fuskanta a sake, nazauna gefen Baba yay murmushi yace "Etrat matar tsoho... "
sai naji kunya narufe fuskana da hannuwana Baba yay gyaran murya yace "dama dai maganar aurenkine ya matso, shine kuma mu munriga mun badake agurin yaron gidan alhaji labbo wato Ameer Hussein wanda kuka tattauna dashi jiya da yamma kuma ga dukkan alamu kun aminta da juna sabida mamarki tace kun kusa awa uku kuna magana wanda ya tabbatar mana da cewa kuna k'aunar juna, saidai jin ta bakinki ma yanada muhimmanchi" nanfa zuciyata bak'i k'irin araina nace wllhy Mahbuub nakeso ba wannan Ameer ba shirun da nayi naji Mama tana cewa.. "nagaya maka ta amince kawai sai ki fara sanar da qawayenki 20 may auren" araina nace nashiga uku bansan yanda zanyi da rayuwataba baba yace inje Allah yayi min albarka, jiki ba kwari na tashi naje daki sai sake sake nake, wai zanyi aure nan da sati daya Lallai ma, ahaka har bacci yay awon gaba dani harda mafarkin Mahbuub zaune acikin wani k'aramin dak'i yanata dariya nace mishi lafiya sai kawai ya rungumeni, nan take nafarka natina malamin islamiyan mu yace ,idan kay mafarkin kuka dariyane dariya kuma kuka, nace duk yanda akayi Mahbuub yana cikin wani hali nay mishi addua naci gaba da baccina....... Wasa wasa yaune daurin aurena inda tundaga kan wurin sarki, har bakin kofar rini anan unguwarmu mutanene ta ko ina, gaskiya naga jama'a rabon da naga taron jama'a irin haka tun auren ruqayyah da basasa shekara nawa da suka wuce sai aurena, ko ina zancen aurena ake yau andaura auren AMEER HUSSEIN & ETRAT Allah yasanya alkhairi ni kuwa duk wani tsimi da ake yiwa yarinya idan zatayi aure anmini shi, wanda kun dai san sokoto sarai basai na gayamukuba, yamma tayi aka daukeni aka kaini gidan mijina da yake nan GRA bayan kowa ya watse ba ango ba abokan ango chan sai naji an murda qofa.........
Aka murza k'ofan sai Naji maganar maza amma wani yare suke, sai naji sun kwashe da dariya sai dayan yace "Inaga fa nanne" suka k'ara murda k'ofa suka shigo su bakwaine harshi cikon na takwas hudu fararen fata hudu kuma bak'ak'e yan uwanmu, fuskata na chikin hijab nace araina dama yasan zaizo shine ya bari saida qawayena suka ,tafi nay tsaki araina... suka fara surutansu wani da yare wani da English haka dai suka gama shi dama bakandamiyarshice a hannunsa wato iPad.. yana abinda ya saba sun k'are surutansu suka kawo abinda sukazo dashi suka tashi yay musu rakiya naji lokacinda ya rufe k'ofa amma sai kuma banji tsoronda akace anajiba aranar farko ko miyasa oho? ban kara ganinsaba har bacci yay awon gaba dani.
Tofa gidan aure na nake yanzu gidan k'aton gaske sabida zai kai rabin kilo mtr ko wane bari hadda lanbune a gidan ga swimming pool agidan k'aton gaske ne, falon wani irin babba dashi, dakuna gasunan sunkai guda 10 kala kala abin dai sai wanda yagani, bazan iya tsayawa lissafawaba nidai ganinan aciki. Yau nake ganin ango gobe nake ganinsa shiru, nikuma ko za'a kasheni bansan haryar dakinsaba. nafito falo nafara yan lek'e lek'ena har na hango kitchen, nanfa nashiga na hada break fast amma ba ango ba labarinsa, saida na hada kwana sha daya sai dai inji k'arar mota da safe dakuma da yamma inji dawowar mota, amma bana sakashi a idona tun ina damuwa har na daina damuwa, Wata rana guraren 12 naji k'arae mota abin ya bani mamaki ya akai yadawo da wuri haka, koda bana ganinsa, amma nakan rage tsoro idan Naji cewa akwai mutum a gidan, sai kawai naji motsin mutane, na fito waje, na daga kai naga Umma da Abba da wata mata, nay musu sannu da zuwa na kawo musu abinchi, sabida kullum sai nay girki dashi na dare da narana, sai dai in baiwa masu gadi sabida ba chi yakeyiba yau kuwa iyayensa suka chinye abinchin. Hakadai mukay ta tad'i dasu har yamma, wannan matar zata koya min motane har in iya, naji dadi sosai dadi ya bani key din motar sabuwa ta zamani naji dadi ranar kamar me. hakadai muka hira dasu suka tafi. An bani waya, an kuma bani numbr sa idan inason abu nakan yi masa sms amma bai taba reply ba sai da nayi wata biyu aginnanan ban saka Ameer Hussain a idonaba, wannan wane irin aurene??
Ba miji nayi dana sanin aurensa inason fita sai dai ingayawa mamansa tagayamasa bantaba gigin fadawa kowa halinda nake cikiba ranar wata laraba natashi nayi duk abinda ya dace, niba miji ba sai kwalliya dan banida bambanchi da hauwa jabo. Nafito sai kawai nabi wata hanya wacce bantama bintaba, acikin gidana sai kuwa ga tarin key's a sakale a wani guri, nadauka na fara bud'e bud'e in bud'e wannan in bud'e wanchan, dakunane atsare duk sunyi k'ura ko ba komai tsabta tana da kew na gogesu na yini aiki aranar, nagama kenan sai naga wani labule ina dagawa sainaga...
Sainaga wani falo a hargitse, wanda ga dukkan alamu akwai mutun aciki, sai dai yanzu bayanan haka na gyara fallon na share tas komai nai arranging d'insa, yadawo kamar sauran dakuna, sauran kuwa nace sai gobe dan nagaji na kulle dakunanan na dawo sassana, nayi wanka na saka wasu kaya gasunan dai, na fito tas tas dani sai dai ba miji, bayan nadanyi bacci sai naji motsin mutum abayana nay balaeen tsorata watana biyu da kwana hudu bantaba ganinsa ba sai yau, hasalima bamu taba hada ido dashiba sai yau, fuskarsa a daure yafara min balaee " keee !!!
Waya aikeki dakina?? Wayace kitabin kaya?? Ke mahaukacciyar inace???" Tofa ranar farko da na fara hada ido da mijina wanda nake zamansa wata biyu da kwanaki... shima da masifa yafara min magana, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun., haka kawai nace araina sai naga ya juya har yakai k'ofa yadawo ya wani jawomin gashin kaina wanda yasa nayi wata irin k'ara, sabida zafin danaji yamun magana da ido alamar idan kika k'ara sai naci ubanki ya wurgani nafada akan hannun kujera wanda naji zafi sosai bansan lokacinda hawaye suka zubominba,
nay kukan dana sanin aikin dana aikata, waya aikeki, ke dadi miji hajiyan zabta, haka zuciyata ta mai mai tamin, gobema kik'ara! Nanfa wasu hawaye masu radadi suka zubomin, dan nikam nayi rashin sa'ar miji, arayuwa anya wannan yasan da zamana adunuyi ma kuwa?? Wannan kamar baisan miye aureba, haka nayi jinya ta kwana biyu har na warke, ranar haka najishi shida abokansa, da matar daya daga cikin abokan nasa sunata magana a fallo suna dariya ni kuwa ina bacci ihunsu ya tayar dani daga bacci, ina fitowa mukai ido biyu dashi abin mamaki say yay murmushi, wanda bantaba ganin irinsaba arayuwata, araina nace amma fa mijina ya had'u, sai dai ba kyan hali yace mun... "keee!! ga k'awanan namiki matar abokinace zata riga zuwa gidannan, sai kema kije gidanta," sai matar tace, "Bamaso ai kayi mai wuyar tunda ka kawoni gidanta, mu zamu shirya kammu," Dayan abokin yace min, "Hajiya amarya ana hutuwa, tin dazu mukazo yace kuna bacci bazai tayar dake ba." Nai Murmushi kawai. daga nanfa bai k'ara cewa komai ba, Nan mukaita labari da ita matar mai kirki da ita, khadija ana ce mata sista khadee. Na musu girki hadda Ameer Hussein ya bud'e ciki ya kwasa shima, munyi sabo da ita sosai har tana zolayata wai bawani bayani shine fa araina nace tabbb.!!
ni ko mijin banagani balle zancen ciki haka dai muka rabu mukai musanyar numbr, gobe sai naga mijina yazo da safee ina break fast yazauna shima yaci abinda na girka, ya bani mamaki sosai jiya da bak'i sukazo dgyar yaci abincin, yana farawa kuwa sai naga duk yafi dukansu chi, yauma gashi yazo yana chin abinchina, abin ya burgeni koda baya ko daga kai ya kalleni, mun kwashe wata daya kullum gida yake chin abinchi, sai ranar da gangan naki girgi, da rana wanda yadawo don chin abinchi, tun bakin k'ofa ya hango table din wayam, ya lek'a kicin yaga wayam, sai yazauna fallo sabida yana balaeen jin yunwa, kuma yanzu baya iya chin abinchin ko ina sai na gida, nafito kena sai nagansa zaune ko kallonsa banyiba, na wuce kitchen nahada tea mai kauri nazo d'ayar kujerar nazauna, yana kallon wani film da wani yare ,wanda bansan mi suke cewaba. Haka nazauna ina kallo nima, ina kurba tea na a hankali lokachi daya wani haushina ya kamashi.. ya zanzo gabanshi in zauna ina chin abinchi shi ko tea din inkawo mishi mana ya wane kalleni a wulak'ance, ya karbi kofin da tea aciki ya fasamun akai ya fashe akaina, sai jini nafashe da kuka ko kallona baiyiba, ina mik'ewa tsaye santsin tys din ya hade da tean da ya zube nafadi acikin glass dinda ya mutu tuni ya shige min jiki na gara ihu ba mai taimako sai Allah..

No comments

Post a Comment