Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLES

*** ETRAT PART 8 and 9***
.
Yaji bari yay hugn d'inta, nanma yakasa, yariga ya rude yarasa tantance miyakeji ajikinsa wanda ga dukkan alamu sha'awace ta motsa, nan dai yakai hannunsa ya rik'e hannunta amamakin sa sai kawai yaji tarik'e hannunsa gam, har tana murmushi wanda ya bashi damar kai dayan hannunsa yana zagayawaa akan labbanta nan ma ga mamakinsa yaga tai murmushi, shima yai murmushi aransa yace ta hak'ura tayafemin kenan.. Kai gaskiya yarinyar nan tanada kirki, dama mata haka suke da rahama.? baisan kuwa ita mafarki takeyiba, wai ta auri Mahbuub suna soyayyah...!! lokaci daya na bud'e idonna cike da jindadi sai kawai naga mutum agabanna ya rik'e mini hannu, wani sabon tsanarshi naji ya kamani, na kwace hannuna, na tashi zaune, na dalla masa harara, ya duk'ar da kansa sabida kunya, Lallai dole yaji kunya idan yasanta, sabida ya musgunamata, bance dashi komaiba nabi ta gefensa na wuce, naje nayi brush nayi wanka tafito tas, ga mamakina sai naji k'amshin abinchi, koda na fito sai naga Ameer yana hada break fast sai k'amshi ke tashi, abin ya dauremin kai azatona, ko ruwan zafi baisan yanda ake dafawaba, amma gashi sai k'amshi ke tashi, naso inshiga kitchen in hada nawa brk fast d'in, sai kuma naji bazan iya jerawa dashi guri dayaba, kawai bari idan yafito sai inshiga in had'a, ina zaune ina kallo na yana fitowa nikuma natashi nashiga kitchen sai yacemin "kee...." sabida har yanzu baisan sunanaba "kefanahadawa break fast..! sabida Dr yace kina hutawa,"
.
ko kallonsa ban yiba haka nashiga kitchen nafara hada abin karyawana yana tsaye yana kallona har nak'are nazauna inachi yana kallona duk sai naji wani iri, naso intashi sai kawai naji bari inshare karma yaga nadamu dashi, har na chinye naje kitchen nay wanke wanke nadawo nachi gaba da kallona, shi kuwa yananan zaune sai bina yake da ido, duk inda nayi yana biye dani da ido, ranar ko ruwa banga yashaba, haka ya yini yadan bani tausayi kadan ammafa tsanarsa tana nan cikin raina, wajen qarfe goma naga gabaki daya kalanshi yachanza ya rame yayi wani zuru zuru dashi, yabani tausayi sai nay dabara nazo da kayan tea na ijeye akan table dinda yake gabanshi wai ina nufin yasha amma ni bazan cemasa yashaba, kawai ni nahada nawane nasha ko motsi baiyiba yabani tausayi sosai dan kuwa har yarame ko azumi mutum yay yana buda baki, amma gashi har shadayan dare yayi baichi komaiba, nakasa cemaca yatashi yasha haka natashi nashiga daki nay kwanciyata, har bacci yay awon gaba dani dasafee anan natarar dashi kwance yana bacci nadubeshi yay balaeen bani tausayi sabida nasan baichi komaiba, but ya zanyi in bashi abinchi sabida ko bakomai musulumi ne dan uwana.... (Hmmmmm... wallahi mata akwaimu da tausayi) sabida lokaci daya zuciyata ta karaya bawai dan Ina sonsa ba, aah kawai dai nasan baichi abinchi ba, anan nafara tunanin yazanyi nace yachi abinchi, shiru kusan minti biyar sai natafi kitchen na fara hada masa break fast wanda zai rik'e masa chiki sosai, nan danan na hada abinchi kala kala nazo na ajiye narasa yanda zanyi intayar dashi sai na daure naje ta duk'a kenan na dago hannu zata tabashi sai ya tashi mukayi ido biyu
.
Ya bude ido kunya ta kamata lokachi daya tarasa yanda zatayi, sai Allah yakai idonta akan phone d'inta, sai tawayance ta'dauki wayanta ta k'ara gaba, shi kuwa ya d'auka dama wayan zata d'auka, yatashi tsaye sai jikinsa yafara bari bashiri yadawo yazauna, yunwa yakeji sosai ga kuma abinchi agabanshi yatashi dagyar yana dafa garu, yaje yay brush yadawo, sabida shi ko ganintan da yakeyi yanasa ya k'oshi yazo ya zauna yasan abinchi banashibane, saboda tace ko zai mutu bazatay masa girkiba, haka yazauna abin duniya duk yabi ya dameshi sai saqe saqe yakeyi. Tana chin abinchinta sai sukay ido hudu yay balaeen bata tausayee sai tace masa "bisimillah" ba musu ba kunya yazo yafarachi, har suka k'are, yay godiya ko kallonsa batayiba, dama tausayani irin nata. Tun daga ranar dai tana girki dashi, sai dai yana shan wulak'anchi da kallon banza da harara, kai duk abinda zai fusatashi tanayi amma shi ko ajikinsa. Kumma haka yana chin abinchinta kullum.. Aka samu sati d'aya, taga kamar neman shiri yakeyi, ita kuma hanyar rabuwa dashi take nema, sai ta dauki matakin daina zama falo aikuwa haka yafi komi azaba agurinsa, sabida zai iya hak'urin rashin abinchi, amma bazai iya hak'urin da rashin ganintaba, ya sameta ya ya gaya mata bazai iya haqurin rashin ganintaba ta gaya masa magana mai zafi saida yayi jaaa dan kishin da yaji lokacinda tay maganar Mahbuub... Tun daga ranar bata fitowa saidai ta dugyre masa abinci ta wuce abunta, yanda ta ijiye abinchi haka take tarar dashi baichiba, sai kuma abun yana damunta, kwana biyu da fara boyewarta, ranar sai ta fito falo dan tun safee bataji mostinsaba, koda tazo taganshi akwance kaman yay bacci, har lokacin sallah azzahar yay bai tashiba, bata kuma tayar dashiba, lokacin la'asar ma shiru kakeji, abin yabata mamaki sabida tasan yana balaeen kula da sallah, da duk wani abu da yashafi addininsa.
.
Akayi Magreeb shima shiru ba sallah ba zancen chin abinchi, tarasa yanda zatayi tatayar dashi abinda ya daure mata kai shine, kwanciya ko motsi bayyiba ballantana ya juya, sai kawai tayanke hukunchin tayar dashi yay sallah tazo takira sunansa ahankali, taji shiru, tak'ara kiransa haka ma shiru, sai ta dan bubbugashi nan ma shiru nan da nan sai taji matsananchin tsoro ta bubbugashi da sauri ina fa baya mosti nan danan ta girgizashi iya qarfinta amma shiru ta kwantsa ihu ba wanda zai jita agidan datake kuma bata iya daukarsa tuni tafita aguje bako takalmi ta kira mai gadi sukazo sukaga baya motsi, haka akaishi asibiti tay balaeen rudewa haka suka isa asibiti aka bashi gado likita ya dubashi iya dubawansa amma lallai bashida rai.... tuni tasanar da iyayensu duk sun hallara lokaci daya tafita hayyachinta dayan bangaren zuciyarta yace mata idan ya mutu sai ki auri Mahbuub masoyinki kinga kun rabu lafiya.. dak'arfi tace "NOOOOOOOOO....
...!!!" Wanda duk akayo kanta, lafiya? tak'ara fashewa da kuka, sabida tasan duk abinda yasameshi itace sabida ya taba gayamata cewa..... "Duk abinda zaki mini ko horo da yunya, harara, idan ma zaki iya kadakeni zan iya jurewa amma bazan iya jure rashin ganinkiba, sabida ganinki yafiye mini chin abinchi, kece abinchin ruhina, kuma wllhy gaskiya nake gaya miki, bazan iya chin abinchiba matsawar bansakaki a idonava, kinfi komai muhimmanchi agurina," a lokacin na dalla mishi harara da kuma tsaki nace mishi "Sai dai kamutu kuwa bazaka ganniba idan ka mutu sai na auri masoyina Mahbuub......."
.
tak'ara fasheawa da kuka tabbas nice, sabida yagayamin amma bankiyayeba kamar mahaukaciya tafara surutai tana nina jawo..! wllhy nice..! ku yafeeni wllhy nice..!! Duk abinda ya sameshi nice. Sunrasa gane mi take nufi tabbas tashiga rudani sabida yanzu ta tuna kwananshi uku baici abinchiba tabbas ita tace sillar duk abinda ya sameshi dai dai nan Dr yafito yace musu sai dai kuyi haquri Allah yayi masa cikawa haka kikaji ta lau tafadi nan koda rai ko mutuwa.....
.
Umma mahaifiyar Ameer, tayo kaina tana kuka tana, "Shikenan ya mutu..!! shikadai Allah yabani aduniya, kuma kin kasheshi," nanfa Umma ta ci gaba da rera wani matsanancin kuka, ta rud'e gaba d'aya. "Shikenan narasa dan'a, dama shikadai Allah ya rayamin, Ashe rabon ni zan kasheshi da kaina ne, nida nai masa aure kuma nasan bayason mace a rayuwarsa, yar nan har yasaka miki doka miyasa kika taka dokar.? kince kece? ya kikay kika kasheshe kitashi kiyi magana...!!" Amma nima lokacin na riga na suma, dak'yar aka janye Umma daga jikina wanda ga dukkan alamu ta samu tabuwar hankali, aka kaini d'aki dagyar na farfado daga dogon suman da nayi, ina bud'e ido nace "ina yaya As meer?"
.
kowa sai kallona yake natashi zaune nafara ihu, sai an kaini gun yaya Ameer, nanfa akarasa yanda za'ay dani, aka yiwa Dr. magana akan ya nunamin gawar Ameer Hussein, yace sai nayi shiru, haka nai shiru, aka saka min wasu kaya nabi bayan Dr. naganshi kwance tunda nake bantaba ganin gawaba sai yau, gawar ma ta mijina, wanda nice sanadiyar mutuwar shi, na daure nay shiru dama Dr. yace mini idan nay kuka zan fita, tuni na natsu naje gunsa na tsaya Ina kallon sa, na bud'e fuskarsa da aka rufe da wani mayafi green, na kalleshi rana ta farko da naji sonsa ya shiga raina, amma ba amfani tunda na kasheshi..! na kama hannunsa ahankali na rik'e gam, amma abin mamaki ba sanyi ajikinsa, wanda a islamiyanmu ance mana gawa tanada sanyi idan ta dauki d'an lokaci, amma shi sai zafi naji ajikinsa, na kallesa Lallai nay asara koba komai zaman aure yafi zaman zawarchi, amma yazanyi tunda na riga na kasheshi, lokaci daya wasu zafafan hawaye suka saukomin da natuna da sista khadee yanda take soyayyah damijinta wanda nay alk'awarin duk lokacinda muka shirya sai namishi soyayyah wacce tafi wacce sista khadee takeyi da angonta, amma ina mijina ya zama gawa, wasu zafafan hawaye suka sauka a idona ahankali na janye mayafin da aka rufe masa jiki yanada singlet ikon Allah arayuwa inason miji mai gashin k'irji gashi nasamu amma nakasheshi..!! Ahankali na dora kaina akan k'irjinsa ina zubar da hawaye, amma ba sauti, na k'ara matse hannunsa iya k'arfina, nayi minti biyar ahaka sai naji kamar zuciyarsa tana bugawa kadan kadan nay balaeen tsorata da naji ya motsa hannunsa dana rik'e, dama gawa na motsi..?? Idan ma kasheni zaiyi to yakasheni in huta...
.
sai naga likitochi sun shigo aguje ashe har sungani a dakinsu ceawa yana nunfashi tuni aka kada ni waje, amma kuma sai naji kukana ya tsaya kawai son ganinsa nakeyi. Umma dai tanachan ba lafiya anmata allurar barchi, nan dai na zauna ina tunaninsa lallai na cutar dakai Ameer, koda kai ka koyamin tsanarka, kai ka koyamin ki'yayyar ka. Dr. Ne yafito yace mungode Allah ranshi yadawo, dama dogon suma ne sai dai jikinsa yayi wk sosai, so sai ankula dashi anan nay hamdala, angayawa kowa Ameer ya dawo amma kuma baya iya magana sai dai motsi da kai da yakeyi. Bayan kwana d'aya aka bamu izinin zuwa ganinsa, munshiga mu biyar iyayensa da nawa iyayen da kuma ni muna zuwa duk yay ma kowa murmushi amma ni ko kallona baiyiba, nanda nan nasha jinin jikina, duk naji natsani kaina sai ya buda baki kaman zaiyi magana ina dago kai naga ya tsuramun idoo ko gyabtasu bayayi, har sai da na tsargu sai naji ance. ET...! ETR...!! ETRAT...!!! Tabbas Ameer ne ya kirani wanda bantabajin yakira sunanaba sai yau.....
.
Nazo da sauri zan matso gunsa sai naga Umma tatareni, tace "bazaki zo kashemin d'aba tunda Allah yasa bai mutuba ak'ara gaba da mugayen halaye...!! Ki fita ki bace mun dagani" haka naji maganar kamar saukar aradu yadago hannu irin inje gunsa, amma umma ta hana naja na tsaya sai kuma kuka ya subuchemin haka na juya na fita bansan ina zan nufaba gidan ubana zanje? ko gidan mijina? Haka naita saka a raina tabbas nasan yanzu ina son Ameer sosai, wanda nima bansan yanda nakejin abun arainaba, sai su Hauwa Jabo da suka san dadin soyayyah da zafinta, haka dai na yanke shawarar tafiya gidan mijina idan ma yasakenine sai maje gidan mu, haka kuwa na wuce cike da bak'in ciki. Iyayena suna gun amma basu cemata komaiba, tunda basusan miyake faruwaba, saima hak'uri da suke bata. K'awata sista khadee tazo duba Ameer asibiti wanda bata tarar daniba, taje gida tanamun fada yazan bar mijina indawo gida nanuna mata cewa nazo daukar kayan mune nan dai nasamu narabu da uwar iyayi sista khadee.. hardai ameer yay kwana uku banje na dubashi ba Amma zuciyata tana Chan tare dasu. Acan kuwa ya matsa shi sai an kirani, Umma kuwa ta hana yace shiko sai an sallameshi. Haka aka salleshi yanata jin dad'i ga mamakinsa sai yaga an wuce dashi gidansu, ba gidansaba, yaso yay magana sai yay shiru suna isa gida su mama sukayi Allah yak'ara lafiya suka tafi gida, Umma kuwa nan tafara balaee wllhy sai ya sakeni, Ya tambayi dalilin hakan Umma tace sabida tanason takashe min kai...
.
Yai murmushi nan yagayamata abinda yafaru tun farkon auren mu har zuwa yau, Umma tay shiru , lallai tayi saurin son yanke hukunchi batare da binchikeba, bayan annabi ya umurcemu da kada Ku rik'a yanke hukunci da gaggawa ba tare da bincike ba, tay danasanin abinda ta aykata sosai, wanda har kuka saida tayi, sabida giyar son kai data kwasheta, kuma Lallai Etrat tayi hak'urin zama da Ameer, wanda ba yarinyar da zata iyayin irinsa batare da ta fallasashiba, nan dai tai mishi fada sosai kuma tace sai tarabasu idan baiyi hankaliba, suka tafi dashi da ita chan gidansa, suka tarar dani a falo na zauna naci uban tagumi, daganina kasan ina cikin tashin hankali, naji tsoron ganin Umma, amma kuma naji dad'in ganin mijina wanda ya warke sai dai akwai rama kadan tare dashi nan muka gaisa da Umma a tsorace, itama tagane hakan, nan dai Umma tay ta bani hak'uri akan abinda tamun a asibiti, kuma tace " Ameer yafadamin duk chutarki da yayi Ai da ki da kin masa fiye dahaka Wllhy, Amma yanzu kina free, idan zaki zauna dashi to shikenan, idan kuma bakyaso wllhy zan saka ya sakeki sabida cutar tayi yawa idan kuma zaki iya zama dashi to zabi nakine." tabbb nan naga Ameer Hussein yana gumi tabbas inason mijina, amma ina tsoron halin maza nay shiru nan dai Umma takatse min tunani tace ke muke jira nace Umma gaskiya.

No comments

Post a Comment