Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLES

*** ETRAT PART 3 and 4 ***
.
Kash Ameer Hussein mushkiline har na bala'ee, wanda ko magana idan yayi zaki iya lissafa haruffa nawa ne amaganar tashi, fuskarshi adaure take, baya shiga harkar kowa sai ta gabanshi, kai ko dariya bayayi sai murmushi, shima wa iyayensa yakeyi awajee baya ko murmushin, duk wanda yayiwa murmushi to yagodewa allah.. Tun yanada shekara 8 aka kaishi qasar Cyprus karatu inda kowa yasan k'asar akwai tsadar rayuwa, sabida kasar da sunsan yanda zasuyi ko numfashi idan kayi sai ka biya su, haka komai tsada a qasar ammafa qasar kaje kagani ta hadu sosai wllhy... Anan ya girma gurin wani abokon babanshi, yayi prmry yayi secondary har yashiga AUM babbar jamiar gasar ce, anan yayi karatun shi har yayi mastered dinshi, dayake allah yayishi mai hazak'a sai yayi saurin kammala karuntunshi yana da shekara 31... Ameer Hussein ba abinda yatsana arayuwarshi kamar mace, bai taba daukar mace a matsayin Abu mai darajaba, Sam batada daraja, haka yake ganinsu kamar bayi, sai yazamo kwata-kwata bayason mace ko abokiya mace baitaba yiba balle yayi tunanin aure, ikon Allah Ameer Hussain dai ya tsani mata wllhy.... Shidai kawai karatu, skull mate, course mate, musulmai, da arna farare da bak'ak'a, son nuna mishi k'auna, amma baitaba amincewa da ko dayaba, karkuyi tunanin ko mace ta taba yimasa wani abu aah..!!
.
Wanda yasa ya tsani mata, ko d'aya, kawai ya tsani matane arayuwansa. h Haka ya k'are karatunsa ya dawo gun iyayensa, Lebanon yay shekara biyu dasu achan, har suka dawo gida Nigeria sokoto. Ameer Hussein kullum bashida aiki sai danne danbe da Ipad d'insa, wacce inajin tafi mace muhimmanchi agurinsa, shidai haka rayuwarsa take kuma baya shiga harkar kowa kuma bayason ashiga tashi... Sai dai matsalanshi daya akwai k'azanta da take damunsa, bawai ta tufafiba aah. ta gurin zama idan kahadu dashi ahanya yana k'amshi bazakayi tunanin zai kwana a inda yake kwanaba, dan hargisti da yamutsewar gurin wannan akan wannan wancan akan wannan.. tofa kunji tsabtar tsula inji ba sakwakwace.....
.
** ** ** ** ** ** ** ** ** ** **
.
Maman ameer tadawo gida cike da farin ciki da murnar tayiwa Ameer d'inta mata, tasamu alhaji labbo mahaifin Ameer tagayamasa, yaji dad'i sosai musamman dayaji cewa yarinyar yar gidan wayee, kuma dama bayason yar boko wacce tayi zurfi da karatu yafison yar daidai wacce zata iya hak'uri da Ameer hussein, Maman Ameer tanuna masa hotunan da suka dauka tare da Eetrat, nanfa alhaji labbo yaqara jin dadi da samun suruka kyakyawa kamar Eetrat. murna agurinsu ba'a magana, yinin ranar gaba daya magana daya akeyi, ya auren zai kasance, suna jiran sarkin mishkilan duniya yazo sugayamishi suji abinda zaice, sunsan sai sunyi dagyar amma kuma zai amince duk da hakan. Bayan sallar esha sukaji karar matarshi yadawo daga office yana tafe yana danna iPad a hannu har yana karo da fridge a fallo sannan yadaga kai yay murmushi...(laaaaa dama maza sunada dimple ne??)
.
Ammafa wllhy Ameer hussain hadadden guy ne ta kowane janibi babanshi sak ya biyo, saidai shi black ne amma yanada haske kamar irin black American dinnan haka yake. Gashinshi Wanda ya kwanta lub akanshi, haka gashin yake ko ina ajikinshi musamman a qirjinsa gashida faffadan qirji atak'aice dai Ameer Hussein yakai iya inda namiji yake kaiwa sai dai mishkilanchinsa yayi yawa..... "Sannu umma sannu abbah" haka yagaida iyayensa yana murmushi yazo yayi musu kiss a fuska al ada dai ta turawa, zai wuce daki Alhaji abbanshi ya kirashi yadawo ya zauna, ananfa abbah yafara yi mishi maganar aure ya bushe da dariya budan bakiin da zaiyi sai yace.....
.
"Wallahi abba kuna bani dariya da mamaki, ni mizanyi da mace???" ya wani ya tsina fuska irin maganar da ake mishi sam batada muhimmanchi a gurinsa.. abba yaci gaba da magana, "nidai dan Allah bamuce kaje ka nemo mataba ga wannan yarinyar mamanka ta nema maka, sai ka aureta," Abbah dai yayi iya k'ok'arrinshi na fahimtar da Ameer amma yak'i fahimtuwa, nanfa Umma ta daka mishi tsawa tuni ya natsu, ba shiri Ameer hussain ya amince, nanfa suka fara murna Umma taso yaga pic din Eetrat amma ina yak'ara gaba abinshi, Umma takamoshi ta rungumeshi tana saka masa albarka tana murna........
.
Mahbuub daren nan kasa bacchi yayi dagyar yasamu yayi bacci gashi gobe sunada buki a famly d'insu kuma dole yazamana yananan sabida haka bazai samu yazo gidansu Eetrat ba haka yayi juyayinsa, Monday yakoma aikinsa yamatsu sati ya zaqayo a yazo kawai ya gabatarda kansa a gurin Eetrat.... Nimq kuwa daren haka nayi tafama da tunani na rasa miyake damuna nida nake bacci qarfe 9 na dare yau gani har kusan asuba ko gezau, kuma narasa gane mi ya hanani bacci, dak'yar nasamu nayi baccin sai mafarkin Mahbuub, anan nagane cewa fa guy din ya shiga rainane amma ba yanda zanayi tunda baya sona, fadawa duniya kawai yayi. D safee naso nayi tadinsa a gida sai mukayi bak'uwa Maman Ameer wacce tasa namanta da Mahbuub, koda yake ni bansan zancen Ameer Hussein ba kwata-kwata tunda bawanda yagayamin su biyu sukayi shawaransu basu gayaminba.... Nidai araina nagane cewa inason Mahbuub amma kuma ina jin tsoron yanda naga yazo gidammu ko kallona baiyiba, kuma ya bazawa duniya cewa yana sona ni banga so annanba, naga kullum Umma da mama sai sunyi waya idan tana wayar sai ta koremu karmuji mitake cewa, dai dai da rana daya bankawo cewa maganar aurena sukeyiba, nikuwa gashi sai begen Mahbuub nake a zuciyana....
..
Ranar assabar kamar kullum Mahbuub yazo gun baba sun fara firarsu da suka saba baba yadauki mahbuub abokin shawaranshi sabida yanada hankali sosan gaske suna magana sai baba yace mishi "Mahbuub inason muyi wata magana nae" yaji dadi yadauka baba ya gane yanason Eetrat ne yasosa qeya yace " inaji baba!," " dama maganar auren qanwarkane ya matso..." "Ina zuwa baba wace qanwar tawa?" baba yay murmushi yace "Eetrat mana" " ETRAT baba?" kikaji..... Kikaji shiru lokaci daya, Mahbuub ya fashe da kuka baba yana lafiya mahbuub?? yay shiru yasake fashewa da kuka baba yarasa gane miyake faruwa sai tambaya yake amma ba amsa sai yanzu Mahbuub yagane kuskurensa na k'in furtawa Etrat kalmarr SO... sai kawai duniya ya fadawa maimakon wacce yakeson yagayamata amma yak'i fada, wauta yayi? ko hauka? ko ma miye Dai yayi danasanin aikata wannan wautar. baba yana tambayar sa nanne dai Mahbuub ya fayyacewa baba abinda ke cikin zuciyarsa...
.
Baba yay shiru ko ba komai Mahbuub yanada kirki kuma iyayensa masu mutunchine ,amma kuma yaza'ay ya warware Alk'awarin da yayi, gashi har ankusa saka rana, baba ya tausayawa Mahbuub, amma ba yanda ya iya, Ya dubi Mahbuub yace "Miyasa baka fadaba Mahbuub?" yace "sabida ba matana bane, da Etrat matanane da tun lokachinda nake fama da sonta na furtamata amma sai na ijiye abun araina wannda yanzu nagane hikimar Allah ta rashi furtawan..." haka dai Mahbuub yatafi da jimamin rashin samun biyan buk'atarsa, amma fa yanason Etrat sosai, kuma yana kishi da duk mijin da zai aureta.. baba yashiga gida yafadawa Mama abinda yafaru, Mama tayi jimami sosai, kuma ta tausayamasa ana maganar sai na shigo naji abinda suke fada bance komaiba, amma banji zancen wai an mini wani mijinba, na dauka Baba yabi ra'ayinane na sai tsoho, amma kuma baba baisan inason mahbuub ba ?? gaskiya nidai da anmishi magana ace ya turo haka naita sak'e-sak'e araina, har suka tafi suka barni, bansan sun tafiba..... ashe so yakan hana bacci zancen da na rik'a yi Kenan a zuciyanta, amma fa naji haushin hukunchinda Baba yayanke batareda ya tambayeniba, haka na hak'ura amma fa abun na rain....... Ameer Hussein har ya manta da zancen wata yarinya wacce ko sunanta baisaniba, kuma bayama son yasan sunanta, Umma ce tashigo da fara'arta tasamu Ameer yanata game a iPad d'insa, Umma taje kusa dashi tazauna yay murmushi " sannu umma.!"
.
tace yauwa tay shiru chan tafara magana "dama zancen Etrat ne, shine muka yanke shawaran gobe lahadi da k'arfe goma na safee zamuje kagaida iyayen rarinyar, kai kuma sai Ku gaisa da yarinyar." baice komaiba kuma baidago kai ya kalletaba tace "kanaji na kuwa?" yace "Eh Umma Allah yakaimu, goben" tayi mamakin amsar dayabata, amma sai tashare tasaka mishi albarka tak'ara gaba, yaci gaba da danna iPad d'insa, Umma takira Mama tagayamata gobe zasuzo harda Ameer, Mama tay murna sosai tagayawa Baba aka fara shirye shirye, nidai kawai ancemini zasuyi bak'i amma bansan gurinaza'azoba, andai kawo mani sababbin d'inki wani material less ne ,akayi dinki mai kew wanda dagani zai kamani sai wata qaramar sarqa mai kew nidau sai kallonsu kakeyi......
.
***
.
Kallonsu nakeyi abun bai bani mamakiba sai da naji cewa wai harda Abban Ameer za'azo, to amma miye had'in zuwan abban ameer da bani sababbin dinki?? Haka dai na gaji da sak'e- sak'ena araina, kuma ban sami amsaba.... anyi aiki sosai wanda aka share gidan ko ina aka yi girki kala-kala nidai pizza kawai hada musu,da kuma shawarma drink wanda akeyi da shinkafa, kwakwa,da madara yanda na had'a shi, Bayan na jik'a farar shinkafa, sai kuma na d'ora daya akan wuta, ta dahu kamar tuwo, na sauketa ta hada da jikak'k'iyar shinkafar da kwa-kwa, na markad'e, na tace, na samu sugar da madara na saka, aka saka a fridge, gaskiya yay dadi sosai nima nasani, mun kammala duk wani abu na tarbar bak'i bak'inmu kawai muke jira......
.
"Wai ina Ameer yake ne" inji abba, Umma " yana ciki yana shiryawa" "OK mudan jirasi kinsan mutumin naki mishkiline," shiru kakejii har sukai minti goma zaune abba yace "bari indubasa ingayamasa yay sauri" bude qofan keda wuya sukaga ameer kwance yana shara bacci abin ya bashi mamaki sosai yaje gun Umma " dama baki gaya masa cewa karfe goma zamu tafiba.? tace "Wallahy nagayamasa" Abba yace "To ai kuwa yana chan yana bacci abinshi," Umma ta fusata da sauri ta miqe Abba yace "dakata malama lallabashi zakiyi sai yayi fushi muje muga yanda bamaso a gun.!" haka sukaje suka tasheshi cikin kulawa da wayo irin na manya aka lallabashi ya tashi dayaga ran mahaifansa ya bachi kawai hak'uri kawai sukayi suka share, sai yayi sauri shima ya fara shiri. kwata kwata Ameer yamanta da zancen zuwa gurin wata mata, aransa yay dariya (wai mata!) a tsanake ya shirya dan kar ya k'ara bata musu rai, abinda ya tsana kenan arayuwarsa ganin bachin ran mahaifansa abinda ya burgesu shine tufafinsa yasa na k'asarsa Nigeria, wanda rabonshi dasu tun sallar layya ai kuwa yafito tas dashi ya kafa hula yafesa turare yay kew abinshi ya dauki bakandamiyarshi wato iPad, Yafito cikin minti ashirin yak'ara basu hakuri, sunata mamaki, ko ya sauko ne, shi yay driving din mota har suka isa kofar rini unguwar mu..... Nayi wanka nasaka kayanda aka kawomin, dama ni ba ma'abociyar kwalliya bace amma kayan sun fitar dani sosai, ga qaramar sarqan nan da na saka haka dai nafito kaman wata amarya, mazau nan nan nawa kuwa sun fito tsab atakaice dai nayi kew sosai nikaina naji haka ajikina.....
.
Misalin qarfe 11 da rabi bak'inmu suka iso, Umma tashigo ciki su Abba da Ameer suka wuce sashen Abba, nanfa su Umma da Mama suka fara tad'i abinsu, ni kuma na fita na basu guri, zuwa 12 akace afito aci abinci, nanfa aka kwasa akayi fallon Baba, aka bajee chan-chan na hango Ameer Hussein zaune amma kanshi ak'asa yana abinda yasaba da iPad d'insa, nidama bansanshi so banyi k'ok'arin gaisheshi ba, fuskar shi na gefe mu kuma muna waccan barayin Ameer baici komaiba sai pizzan dana had'a, da kuma shawarma drink, koda bansanshiba naji dad'in abinchina daya chi, kuma su kadai yachi aka k'are chin abinchi ayanda ya mik'e bai waigoba kawai gaba ya k'ara bandamu dasanin ko wayeba..na kashe kwanukan naje na kanke, mukaje sallah, na idar da sallah kenan ina lazimina dana saba sai kawai ga Iffat, "wai Auntie kije inji Mama" natashi naje tace insaka powder fuskana yayi wani iri na k'ara goga powder a fuskata nazo kije fallon abbanku kina da bak'o inji Mama.
.
Nace "bak'o Mama?" tace "Eh kije yana jiranki" abin yabani mamaki ni ba saurayiba balle inyi tunanin ko yazo gurina ne, araina nace ko tsohon da nake nemane nasamu araina nace tab.!! Haka naje pallon babana. Ntarar da mutum zaune yana danna iPad, ko game yakeyi oho nay sallama ya amsamin batare da ya dago kai ya dubeniba, na kuwa sha hijabina abina, nazauna a dayar kujeran gefen sa daga yamma, yanda nazauna haka nake zaune kusan awa daya bai dago ya kalleniba haushi yakamani sosai wai wannan shine baqon nawa ko kuma yaya??
.
har zan mishi magana, sai kawai guntuwar sarautar mu ta mata ta motsa, kawai sai na share shi, ai kuwa haka muka share awa uku bai dago kai ya kalleniba ni kuma ban mishi maganaba sai danne danne yake da ipad, can sai ga Iffat a guje ta fada jikinshi, "Yaya Ameer wai akawo maka wani abu zakachi?" nan natuna dako ruwa ban bashiba ko shiyasa yak'o yimin magana? yay murmushi yace "Ya sunanki ?" tace "Iffat shunana" yaja kumatunta yana murmushi, nanne naga ikon Allah, dama maza suna da dimple ne sai yau nagani, yace ki kawo min ruwa idan akwai sauran pizza akawo min, ta tafi dagudu ya bita da murmushi ahakan ya sake duk'ar da kansa ya chi gaba da aikinsa, aka kawo masa pizza wacce na ijiyewa kainace sabida ban chiba, kuma na wahala gurin girkawa, haka ya chinye ta tass. ko mai bai rageba naso inchi pizzar nan amma wannan sarkin shurun ya chinye, na hak'ura dan dole, yana chinyewa naga ya mik'e ya wuce abinshi, ko sallama babu amma wannan mutum anya gurina yazo kuwa...?
.
oho. nidai naje cikin gida nachi gaba da shirye shiyen abinchin dare haka dai bakinmu suka kammala abinda zasuyi akayi bankwana naji ana cewa 20 ga may din yayi, nace mi za ayi 20 may kuma,? nace koma miye yau dai 12 may ne zamu gani har suka tafi wanda akace bak'onane bai daga kai ya kalleniba. Nafito daga kitchen naji mama tana cema Baba "Anya niko aurennan baiyi kusaba 20 ga wannan watan, fa? ba fa wani shiri da muka yi ita kanta yarinyar bamu saniba ko tana sonshi.?" sai Abba yace "nasan Etrat zata soshi kincemunfa awansu sama da uku suna magana, idan kuwa bata sonshi bazasu shafe awa uku.suna maganaba!!"

No comments

Post a Comment