Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLES

*** ETRAT PART TWO (2)***
.
Yana sallah amma kwata -kwata hankalinsa baya tare dashi, dan kuwa da ace shi kadai yake sallan sai yayi demuwa fiye da goma, ba abinda yake mishi yawo akai sai lafazinda baba ya gayamasa ai "ETRAT TAKUSA AURE" nan yatuna da hannunta da yakama wani laushine dashi kaman auduga ga wani k'amshin turare dayaji tanayi wanda baitaba jin irin saba, idan na aureta na more gaskiya ina sonta, kai yau zan gayamata abinda ke zuciyana, haka yayita saqe-saqe a sallah nan take yace astaqfirullah..!!! miyasa baituna da wayannan abubuwaba sai yanzu, take yatuna ashe sallah akeyi yayi istiqfari yadawo hayyachinsa, yayita jiran liman yace allahu akbar yadago, daga sujada yaji shiru, ashe anqare sallah yanachan yana tunani, da ya gaji sai ya dago kai, koda ya duba sai yaga wasu har sun watse daga masallaci, yaduba yaga baba na lazimi kunyar duniya ta isheshi baisan lokacinda aka qare sallah ba, yanata tunani yadai san anyi raka'ar farko dashi sauran kuwa sai Allah. ya sallame yaje gun baba yace mishi zai tafi gida baba yace "bakada lafiya ne" yace " lafiya na k'alau baba" "To amma naga lokaci daya ka chanza" yace "lafiyata lau baba idan nayi sallah haka nake "(kaji bawan Allah) bayan kuwa firgichin jin za'ayiwa Etrat aurene, baba ya yarda da abinda yace sukayi sallama yatafi gida...
Etrat kuwa kunya ta isheta yau namiji yaganta ba hijabi, har ya rik'emata hannu wanda tun tana karama take zunbula hijabi, har data girma, sabida mazaunanta dasuke motsawa da kansu idan tana tafiya sai tak'ara saba saka hijabin har yazamo mata al'ada, yau shine namiji yaganta har ya riqke mata hannu kuma tarasa dalili idan ta tuna sai tayi murmushi maimakon ta tsaneshi, baba yashigo gida sai taji tanason taji labarin Mahbuub agurinsa, amma kunya takeji, wata zuciya nacewa tambaya wata nacewa aah haka har sukaje chin abinchi dare, sai ga Hammad yashigo yace " baba wai Mahbuub yana magana" mamaki ya cikawa baba ciki yanzu fa suka rabu ko yayi mantuwane? haka dai da waswasi ya fita ita kuwa Eetrat ji take kamar ta lek'a taganshi tadawo, karo na farko arayuwanta dataji cewa zata iya auren yaro idan dai Mahbuub ne, dan ya burgeta.... "Lafiya dai Mahbuub?" . firgigit yadawo yace "lafiya lau naje gidane wai sun dauka bazan dawoba, shine basu ijiyemin abinchiba, shine nazo nan kamin achinye inchi na iffat, sai Eetrat tadafa mata wani."
Baba yay murmushi yace to bismillah shigo.. babana dduk yanda kake dashi baya kawoka cikin gida, iyakachinku gofar gida, ko zaure amma Mahbuub dan gatan baba har cikin falon baba, dama duk tare muke chin abinchi dadare, anachi ana tadi bansan cewa yashigoba da sai na zunbula hijabi, amma ina saida nakawo tsakiyar falo naganshi suna chin abinchi da baba da iffat, dama naje kawo ruwa ne lokacin da ya shigo, kunya takamani gani dagani sai wata riga mai kamar bes sai wani shot nika, na rasa yanda zanyi bazan iya komawa ba, natsaya chus sai Hammad yace "Aunty kishogo mana." kamar an mini allura na zabura sai nawayance nace "Yau baqo mukayi?" iffat tace "Eeh, yaya Mahbuub ne" nashigo na zauna, bai dago kai ya kalleniba sannu kawai yacemin haka yasa na sake nachi abinchina, amma inata sake sake araina, nace dama karya yakeyi yakoramin samari amma gashi ko kallo ban isheshiba, kuma yaqi cewa yana sona, lokaci daya naji na tsaneshi kaman da.. Dago idon da zanyi in harareshi sai kawai muka hada ido, sai naga yay murmushi bansan lokachinda nima nay murmushiba, nakawar da kai take naji na k'oshi ..
Namike tsam zan tashi, mama tace "ina zaki?" nace "nagoshi " zatayi magana nayi mata wani iri da ido.. Ta tabe bakii batace komaiba, ina tashi shima yaji ya k'oshi haka dai dan kar agane ya rink'a tusawa, har suka kare, yayi godiya yakara gaba, yaso ya fadi abinda ke zuciyarshi, amma sai ya kasa ya haqura yatafi, ita kuwa Eetrat duk kunya ta isheta namiji yaganta wit out hijab...! Tun da safee sukaji sallamar bak'uwa ikon Allah!!! "Yau maman Ameer kece a gari!!!"
haka tace "wllhy nice" "Saukan yaushe?" tace yau satinsu biyu da da dawowa " kishigo daga chiki mana" murna gurin mama ba'a magana yau babbar aminiyarta ta dawo, "Bari inje in hada miki abin karyawa" maman Ameer tashiga d'aki, Maman iffat ne ta hada mata break fast dai dai aljihunsu, sunachi suna tadi maman Ameer k'awar Maman iffat ne sosai, wanda tun suna yan mata tare suke, da suka girma kowa tay aure ta kama gabanta, amma suna zumunchi sosai sai wannan tafiyar da sukayi Lebanon basu dawoba sai bayan shekara 7, sunyi missing din juna ba kadan ba, suna ta tadi bayan rabo nannefa maman Ameer tace "Ina Eetrat da hammad" . "Wallahy duk suna barchi ne, Kinsan yau Sunday ba skull," batamasan iffat ba wacce bata nan mama ta haifeta, sunsha labari sosai, chan saiga Eetrat ta taso daga bacci guraren qarfe goma na safee, Bayan tayi brush ta wanke fuska, taje zata gaida mamarta, ta tarar da bak'uuwa, ta dan ganeta, ta gaidata, suka gaisa bayan ta fita mamaki ya kamata, wannan Etrat ce ta girma haka koda nabarta shekaranta goma sha daya fa, mama tay dariya duniya kenan gatanan sai aure, nan maman Ameer ta gyara zama tace "An tsayar mata da miji ne" mama tacee " aah" nan maman Ameer ta kwashe da dariya suka tafa, tace "wllhy haka na riqa jin inzo giddannan akwai alkhairi, kamar Ana korani, haka na rik'a ji, shiyasa na danno sammako, ashe etrat rabon Ameer ce.." .
batasan randa ta rangada gudaba dan murna, muka shigo da gudu muma muji, Mama ta hararemu muka koma, Maman Ameer ta kirani nazo taqara kallona sama da qasa ta qara rangada guda, tace "Anyi angama kuma wllhy tayi" ni bangane komaiba Mama tace "Jeki ki hada muku abin karyawa" natafi chike da mamaki mama da maman Ameer suka kitse magana akan za'a hadani aure da Ameer Hussein, tuni baba ya amince sabida yasan iyayen sa suna da kirki sosai, kuma yasan barewa bazatayi gudu d'anta yayi rarrafeba.. Da maman ameer zata fi tace muzo muyi hoton tarihi aka dauki hotuna kala kala tanata murna nidai ba ace mun komai ba, kuma ban kuma tambayaba amma naga kowa cike da murna da farin ciki, bama kamar maman Ameer ba duk inda nayi idonta akaina, suka rabu da mama chike da shauqin junansu. babansu Ameer Hussain mai kudin gaskene sosai, wanda yake sana'ar saida gwalagwalai a Beirut babban city na qasar Lebanon, Ameer hussain shi kadai yake agurin iyayenshi, mamanshi saida ta haifi yara guda 8 bayan Ameer Hussein duk suna rasuwa sai ameer hussaini ya rayu, kuma shine babba, yasamu tarbiya sosai agurin iyayensa wanda aga bansu ya tashi sai dai kash ameer Hussein ..

No comments

Post a Comment