Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLES

*** ETRAT PART ONE (1)***
.
Zaune nake a kan daya daga cikin manya-manyan kujerun da suka mamaye falona, wanda dagani kasan cewa gidan akwai ni'ima da hutu mara iyaka a cikinsa, ga wadata ta kowane fanni amma kana dubin mai gidan, wato ni zaka fuskanchi cewa ina cikin matsananciyar damuwa... Tunani nakeyi wane irin haline nasamu kaina a ciki? wanda nikaina nakasa gane bakin zaren abun!! nidai sunana ETRAT, mahaifina yanada hali dai-dai gwargwado tayanda zamu rufawa kanmu asiri. Inada k'ani guda daya Hammad, da yar autarmu Iffat, atak'aice nice firs born a gidanmu, nayi karatu daga prmry har zuwa secndy, bayan na kammala secondry, nanfa mahaifina yace dole aure zaimun, araina nakance naga yanda ake aure ba miji. Allah yayi min kira ta halitta, wacce duk namijin da ya kalleni nasan sai ya maimaita, ni ba doguwaba kuma ba gajeraba, inada matsakaicin tsawo gani yar duma duma dani, inada hips sosai wanda har asibiti naje inason su bani magani su rage girma, akace ba magani saidai ayimin aiki arage su, ana zaune k'alau ina naga kud'in ragiyar hips?
Tun daga nan ban k'ara zuwa asibiti zancen ragiyar hips ba, kirjina cike fam, kamar an girkasu gasu lukuta-lukuta, inada ido manya manya wayanda idan ka kalleka sai ka kauce, dan wai sexy ne injisu, wasu na cewa kamar nayi sha haka nake yi da idanuwana, abin yazamomin kamar al'ada lumshesun da nakeyi, amma ana cewa wai dagangan nakeyi, hancina dai dai ni, kai nidai badan kar inyi saboba, da sai nace ni dai na cika goman da ake cewa mutum dan tarane, sabida banida rangwame ko daya a halittar jikina, fagen gashi kuwa, nikaina bansan inda nayi gadon gashiba, sabida mamata da babana dukansu hausawan sokotone gaba da baya, haka Allah ya halicceni da gashi bak'i silk ga tsawo ga shegi ni farace amma ba irin mugun farinnan ba ataqaice dai wllhy inada kew sosai, wata baiwa da Allah yamun itace kwata- kwata bana warin zufa, kuma idan nasaka turare ajikina ko bashida tsada zakiga yadade ajikina bai bi iskaba, wanda hakan yakesaka bana saka turare sosai . Sai kiji ana "wane turare kika saka haka Eetrat??" basusan cewa jikinane keda wannan baiwarba, kuma gani da wata irin mahaukaciyar tsafta, ga k'yank'yami da yake damuna, idan guri bashida tsafta komi tsaftar abinchin sa, bazan iya chiba, ni kuma haka allah yayini....
Arayuwa na tsani samari, burina in auri tsoho mai shekaru masu yawa, atunanina yafi sanin darajar mace, bantaba kawo zancen saurayi arayuwataba, wanda har nakai shekara 18 amma ba wani dattijo dayazo neman aurena, duk samarine, hakan yakan bani haushi da takaici narasa miyasa wayanda nakeso basa sona, sai wani sarkin nachi waishi Mahbuob, shinefa yake biye dani baya barin kowa magana dani kuma shi bayamun magana, atunaninsa zansoshi baisan ni sai dattijo ba, nifa ko sa'ar babane ashirye nake da na aureshi. Mahbuob matashine dan kimanin shekara 29, Wanda ya kammala karatunsa, mahaifinsa yasamamasa aiki a airport, duk sati sai yazo gidansu gun iyayensa, ya gaidasu haka zaizo gun babana suyita tadi, har sai ya ganni sannan yatafi gidansu. Bai taba furtamin yanasonaba, kuma baigayawa mahaifinaba, amma duk unguwarmu kowa yasan cewa yanasona, wasu har matar Mahbuob suke cemin, ni kuma ko a jikina, dan nikam ko za'a mutu sai dattijo wanda yasan darajar mace......
.
Idan Mahbuub yazo, sai ya rabawa yaran unguwar kud, da kayan kwadayi, yace musu duk wanda sukaga ya min magana to sugayamishi, haka kuwa sukeyi, suna kai masa rahoton duk wani motsina, idan aka gaya masa wani yamin magana, zai nemi mutumin yamishi magana da lalama, yace yayi hak'uri wannan matarsace, yadaina yi mata magana, idan kuwa yagamaka bakajiba aka k'ara gayamasa kazo, to zai saka yaransa suyita jifanshi sai ya daina kulani, hakan yasa samarin gabaki daya suka daina zuwa gurina, nadawo banida kowa ba tsoho ba yaro, kuma shi Mahbuub din yak'i fitowa yayi maganar aurena.. Ranar wata assabar Mahbuub yazo gurin baba suna tad'i kamar yadda suka saba duk sati idan yazo hutu gida, yakanzo gurin baba, yauma haka nikuma nadawo daga islamiya kenan ina shiga gida sai Mahbuub yamike yace' "ni zan tafi baba" ashe duk yazo haka yakeyi, ina dawowa daga islamiya daya ganni sai yatashi yak'ara gaba, sai kuwa baba yace mishi "zauna inada magana dakai" ya zauna baba yace mishi "Wai miyasa Eetrat na dawowa daga makaranta, duk muhimmanchin maganar da muke, sai ka katseta, katashi katafi?? ko itace agogonka??"
Mahbuub ya sosa k'eyya azuciyarsa yace ashe har anganoshi!! "Aa'aa baba, kawai ina tunanin yarane sun dawo gida, zaka shiga gida kuyi tadi da iyalinka, shiyasa, wai kar na shiga hak'k'in ka dana iyalinka," sai baba yace, "Idan dai wannan ne to kayi zamanka bana shiga gida sai dab da magrib idan zanyi alwalal sallar magrib" yace "to baba" suna tsaka da tadi sai aka kira baba awaya yadan tashi yakoma gefe yana magana, Mahbuub haka yazauna sai ga iffat qanwata aguje an biyota, Eetrat ce ta biyota, wai ta yaga mata littafine ai kuwa iffat tayi jikin Mahbuub, Eetrat tabita Mahbuub ya riqe hannun Eetrat yana bata haquri, haka yaji wani yarr a jikinsa, sai lokacin Eetrat ta tuna cewa ba dan kwali akanta balle takalmi, kuma kayan jikintama sai ahankali, nan take kunya takamata, tajuya zata shiga gida aikuwa yak'i sakin hannunta, tajoyo ta mashi kallon na huqura zan shiga gidane. Tawani lumshe ido, bashiri ya saketa sabida yanda tayi da ido ya firgitashi ,nan fa baba yadawo yana tambayar lafiya, iffat zatayi magana kenan sai Mahbuub yace taje gida, shi yagayawa baba abinda ya faru baba yay dariya yace, "Ai haka iffat take da tsokana kamar me, Eetrat, din ma takusa aure naga wazata tsokana..!" ba shiri Mahbuub ya mik'e tsaye yace "WHAT!!!???"
Baba yace "lafiya kamar nagaymaka mutuwa" Sai lokacin mahbuub yadawo hayyachinsa yaga ashe har tsaye ya tashi, tuni kunya takamashi, ammfa idonshi sunyi tsuru-tsuru (kamar Jabo batada kud'i) baba yaso yagane cewa Mahbuub, Eetrat yakeso, amma baice komaiba, tunda yayi kusan shekara yana zuwa guri na baitaba gayamun ba, nandai baba yakawar da zancen azuciyansa, har aka fara kiran sallaar Magreeb, suka nufi masallaci dan gabatarda farali, amma fa hankalin mahbuub kwata kwata baya tare dashi..

No comments

Post a Comment