Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NA MANTA KOMAI Part 6

NA MANTA KOMAI Part 6
.
Bayan sun kusa gida, ya tsaya ya yi musu siyayyah, gurin
bata ledar hannayensu suka had'u dana juna, saida yaji
wani iri, sun iso gida, ta wuce d'akinta, biyo bayanta ya yi
ba tare da ta sani ba , tana k'ok'arin cire kayan jikinta, ya
shigo d'akin, duk da cewa taji wani iri daya ganta ba wasu
tufafin, sai kuma tace mi zan boyewa mutumin da ya dad'e
da sanina hadda yaran mu biyu...
.
Ahmad kam yaji wani iri, yad'an sosa kai ya duk'ar da
kanshi k'asa dan yaji wani iri sosai, gashi ya dad'e ba mace
tun bayan rasuwar matarsa, ya zauna sai ya juya mata
baya dan yana gudun kar a samu matsala. Saida ta k'are
saka kaya ta na neman hanyar fita, Yace "Suhailah baki
tambayi result din hospital d'inki ba?" Tace "to ai na san
zaka gaya mani indai na in sani ne", ta d'an yi murmushi,
da alama ta d'an saki jikinta, ya ce "kin d'an samu accident
ne ki ka buga kanki, shine kuma ya ja maki wannan lost of
memory din, amma Dr. ya tabbatar mani da cewa zaki
koma normal cikin d'an lokaci kad'an, dan haka karki tada
hankalinki kinji?", ya fad'a yana kallon ta, "kinga yanzu
saboda haka ne na ke so in kai ki Holland dan a k'ara
dubaki, in sha Allah nan da kwana biyu zamu tafi," wasu
kwalla suka zubo daga idanuwanta, tasa bayan hannunta ta
goge, ta dago kai ta dubeshi ta ce "to na gode", harda
murmushin karfin hali, har ya mik'e zai fita tace "dan Allah
ka gaya mani wani abu about My self kila zan tuna,"
hakikanin gaskiya, tun lokacin da hannayensu suka had'u
ya farajin sha'awar da ya dad'e baiji irinta ba, kusan tun
rasuwar matarshi baya da lokacin mace, aikinshi kawai
yasa gaba da binciken abubuwan dake faruwa da wa'danda
suka faru a baya, ga addini ya rik'e hannu biyu , mafari
kenan Alhaji Ibrahim yayi sha'awar hadashi da Suhaila dan
Ahmdy akwai addini . "Zan gaya miki amma saida safe". Ya
tashi ya wuce dakinshi, amma kuma ogan naku ya kasa
sukuni, gashi an dad'e ba'a haduba, ya fito da niyyar ya
d'an kalli fuskarta ne kawai, amma sai ya isketa ido biyu,
yasan matarshice halaliyarshi, amma sai da yaddarta, da
kuma lafiyarta ya ke son ya kusanceta, kuma yanzu gashi
har tunani take wai ta haifa mashi yara, zayyi k'ok'ari ya
danne sha'awarshi har yaga ta dawo cikin hankalinta kafin
ya kusanceta a matsayin matarshi, alk'awarin da yayi ma
kanshi kenan To ko zai iya kuwa?? Har wata zuciya ta bashi
shawarar ya koma d'akinshi abunshi, amma sai ya kasa
yazo yace "to matsa mani na kwanta", zuciya d'aya tunda
gani take komai ya riga ya faru ta yaye bargo ta matsa
mashi ya zauna kusa da ita, ya kasa kwanciya sai ya jingina
da gadon, yace "to daga ina zan fara" ya fada yana
Murmushi, a lokaci d'aya ya jawo bargo ya lullube k'afarshi,
ta matsa kusa dashi sosai tace "babana shine wanda yazo
ko? mamana da k'anena sune wayanda nayi waya dasu ko?
To Ina da yayye?" ya yi dariya sosai yace "kinason family
da yawa kenan?", ta zaro ido "bani dasu ne?
.
Ko ba sune nawa ba", yadda tayi ya bashi dariya, kallonshi
take sosai ta cire bargon ma sama daga jikinta ta
lank'washe k'afafuwanta, ita hankalinta kwance da yar rigar
baccinta, shara shara, ya d'auke idonshi da kyar daga
kallon duk inda jikinta ya bayyana, dan kayan baccinta
kamar yar singleti ce da short wando rabin cinya gasu
shara-shara. Ahmad ya samu kanshi da rik'o hannunta,
kamar zata anshe sai kuma ta bar shi ya rike tunda
mijintane, ya yi murmushi ganin ta amince da hakan, ya ce
kina da yaya d'aya Ameen, kina da abokin haihuwa Suhail,
ke kuma sunanki Suhailah, ku twins ne," "laaa shi isa na
haifi twins", ya dai bata dan labarin da ya sani game da ita
da asalin babanta da mamanta, yana kauce ma duk wani
abunda zai sosa mashi rai, dan labarin family dinta ba a iya
rabashi da na family din shi, tace "to na ji na wa, saura na
ka, a ina mu ka hadu da kai, har mukayi aure?" Ya ji wani
rass gabanshi ua fad'i, yace "kibari zaki tuna a hankali, "Pls
ka gaya mini," ta wani langwabe kai ta matsa jikinsa sosai,
tare da d'an matse hannunshi da nata cikin shagwaba tana
wani farfar da ido, mutumin fa ya fara daukar zafi, ya na
jan nunfashi da k'arfi yana fitarwa, ya runtse idanuwanshi
yana neman natsuwa, ya bud'e bayan d'an lokaci kad'an
yace "mun had'u tun da dad'ewa bayan nan mun k'ara
haduwa a bikin su Al- Ameen sai daga baya kuma mukayi
aure," tace "yauwax", ta k'ara matse mishi hannu, "to wayafi
son wani ni da kai?", bai amsa tambayar ba ,saboda ya
aureta ne dan mahaifinta ya ba shi ita, "yaranmu yan biyune
ko,? D'azu kace min maman twins haka kake kirana
dama?",yace kin cika tambaya, tace "da banida yawan
tambata hala?", Ya daga mata kai, dan ya riga ya d'au zafi
ko magana baya son yi, ta ce ''to na daina", ya ce "ya akayi
baki mance da sallah ba?", ya tambayeta dan ya ji tana ce
ma yaran su zo su yi sallah, tace "wallahi ban sani ba," to
Ina son ki natsu kiji abunda zan gaya maki, "Suhailaa you
are a Doctor," ai sai ta mik'e kan gado tana tsalle da rawa,
shiyasa taga wani k'aton littafi a cikin kayanta wai shi
"internal medicine," duk sadda ta samu lokaci tana
karantashi, data natsu ya kamo hannunta yana magana a
hankali kamar baya so, yace "bani son kowa yasan kin
samu wannan matsalar dan kar ya jawo maki matsala a
gaba, dan haka kar ki gaya wa kowa, kinji?", gobe zamu kira
su mama ki k'ara gaishesu kuma kiyi masu sallama, jibi
zamu tafi", tace "to In sha Allah ba wanda zai ji....
.
Suhaila yarinya ce mai ban sha'awa, bare kuma yanzu da ta
ke cike da farin ciki ganin mijinta ya dawo mata, kawai sai
ya ji ta rungumeshi ta ce na gode, shima ya rungume ta
yana shak'ar k'amshinta da ya bai baye ko ina cikin d'akin.
a hankali ya ke neman natsuwa, amma tana neman ta rikita
mashi lissafi, ya runtse idanuwanshi. Dai-dai kunnenshi ta
ce "wane suna nake kiranka dashi, Ahmad haka nake
kiranka ko?" Dak'er ya daure cikin natsuwa ya ce "sai ya ce
sunana kenan ai," ta ce "amma nima haka nake kiranka
dashi?" "No" ya fada ya na d'an murmushi. "To ya nake
kiran ka dashi?" Ta tambaya. "kar ki damu za ki tuna yanda
kike kirana". "Ok, yanzu tell me about you," tana k'ok'arin ta
tashi zaune daga d'an kwantawar da tayi a jikinsa, aranshi
yavce wannan yarinya akwai jaraba, ta k'ara gyara
zamanta tana kallonshi. "To....."
.
Ya katseta, ya ce aa, ya isa haka, ki kwanta kiyi bacci dare
yayi sosai,da kanshi ya gyara mata kwanciya, ya lullubeta,
ya mik'e zai tafi, har zai tafi ta rik'o hannunshi, "please ka
kwanta dani, ko dan banida lafiya kake guduna ko kuma
dama ba tare muke kwana ba!? "Innalillahi! Wannan
yarinyar so take ta kasheni" abunda ya fad'a kenan a
zuciyarshi, ta jawoshi tare da matsa mashi, inda zai kwanta
kusa da ita, "oya zo ka kwanta" haka ya samu kansa da
kwanciya inda ta matsa mashi. Tunani ya ke ya san fita da
ita zuwa k'asar Holland bazai masa wuya ba, dan yasan
can sosai, visa ma ba zaya sha wuyar samu ba tunda ya
zauna can ya dad'e, kuma ya na da mutane da yawa acan.
Bawan Allah Ahmad sai gaf da asuba bacci yayi awon gaba
dashi, dak'er ya tashi yayi sallah, Sannan ya tashi Suhailah,
itakam duk da tajita daban kamar ba ta saba da irin hakan
ba da suka kwanta ya rungumeta, amma tayi bacci mai
dad'i, ta bar shi akan dan ta manta komai ne yasa ta ke jin
hakan, suna had'a ido ta masa murmushi, itakam gani take
kamar ta fishi sonsa, amma so take ta danne har ya gaya
mata gaskiya wayafi son wani ita dashi. Tayi alwala tayi
sallah, ta nemi guri ta kwanta amma sai taga Ahmad zaune
yanata lazimi, tadan matso kusa dashi, tace "nima ina
wannan zaman bayan salla asuba ada!?" Yayi mata
murmushi, sai ta kanne masa ido, yayi sauri ya kawar da
ganinsa gareta, yace "wani lokaci kinayi wani lokaci kuma
bakya yi," tace "heheeeee irin yaune banayi dan kuwa bacci
zanyi, ta dubeshi, ka mini addu'a na haifi namiji, tunda
inada mata har biyu," baice mata komaiba, hasali ma kasa
lazimin yayi dan sai hada masa zafi takeyi, tazo gefensa ta
kwanta.!
.
***********
Rannar ya dawo gida da wuri, ba kamar da ba, da sai tayi
bacci, yanda Ahmad ke son yaransu ya birgeta sosai, taji ta
k'ara sonsa tunda yanason yaranta, yau kam duk tare
sukaci abinci rana da ita dashi da yaran su, yaran sam
sukak'i yadda su ci su kad'ai, wai sai sunci abinci tare da ita
a plate d'aya ganin Ahmad na murmushi yasa ta biye masu,
suka cinye har suka k'ara, bayan sun k'are 'yar bak'a ta
kwashe yaran da kwanuka, bayan sun gama tayi masu
shirin bacci, ita kuma Suhaila ta gyara inda sukaci abincin
har Ahmad d'in na tayata, sai abin ya burgeta, aranta tace,
"kilama ada haka mukeyi, Ashe dai mijina ya had'u, yauma
sau biyu hannunsu na haduwa, garin wanke kwanuka, inda
suhaila kejin wani irin sak'on da bata saba jiba na mata
yawo a kowace kafa ta jijiyoyin jikinta, batajin dad'in hakan,
sai taji kamar ta bar mashi aikin kawai. Wajen bacci ma
haka yaran suka nace su da Dady zasu kwana, ba wayonda
ba'a musuba amma sukak'i yarda. Haka Suhailah tayi ta
juyi ita adai a gado ta kasa bacci, dan ta saba tun randa
tazo tare suke kwana da yaranta sai jiya da sukaje asibiti
suka kwana da Ahmad, yanzu gashi ba yaran ba uban,
tsaki tayi ta juya har ta fara bacci. Can cikin dare taji an
bude kofar d'akinta an shigo har taji dadi a zatonta su
Surayya ne, murmushin dake fuskarta tuni ya bace ganin
Ahmad har ya karaso gaban gadonta, nan suka tsaya suna
kallon kallo, na dan wani lokaci sannan ya zauna daga
gefen gadon, tuni ta gyara zamanta ta matsa dayan gefen
gado, yace "miye haka kuma!? Da sauri ta k'irk'iro
murmushi tace "laaa ba komai, zo ka zauna ta na k'ok'arin
janyo hannunsa.......

No comments

Post a Comment