Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NA MANTA KOMAI Part 5

NA MANTA KOMAI Part 5
.
Na H.M Jabo
.
Yana office amma tunani yake yi, ya zai tunkare ta, ko
kawai yaje ma ta da sunan game d'in ne shi ma? Idan ta ce
ba ta sani ba sai ya gaya mata, dan yana kunyar Mama,
"No I will not do that. Zanje kawai na ce mamanta za ta yi
waya da ita, duk shirmenta ai tasan maman ko?" jeeeem ya
yi, a ranshi ya ce "yarinyar nan fa ba k'aramar shedaniya
bace," tsaki ya ja "zanga dai yanda za ta bullo wa abin, sai
ni ma na san yanda zan bullo ma ta," ya tattara files ya fito,
ya kama hanyar gida yana yan sak'e-sak'e a hanya har ya
isa gida. Palo ya tarar da su ita da 'yar bak'a, ana koya ma
ta girki, dan black duk wani abu na chi to ta na gurin, sabida
tsabar kwad'ayinta, baiko kalle ta ba, ba ta ma san ya shigo
ba, sai ji ta yi ya ce "ki sameni a d'aki yanzux" taji mi ya
fada, haushin ta d'aya kar 'yar bak'a ta ji ta rainata, dan
akwaita da iyayin banza, bayan kamar minti biyar ta mik'e
ta wuce, d'akin ta shiga ta wuce toilet ta wanke
hannuwanta, ta fito da har zata chanza kaya, dan wani
3quarter na Jeans ne a jikinta, sai kuma 'yar figigiyar best,
gata 'yar lukuta da ita, ta tuna a book din nan ance "ba
kullum bane zaka rik'a budewa namiji jiki ba," tsaki tayi
"bayan ya gama gani na ma, miye ya rage wanda bai gani
ba tunda muna da yara har biyu," Turare ta fesa, mai sanyi
sosai, ta bude wardrobe za ta ciro riga sai kawai ta gan shi
ya shigo, ta juyo ta kalleshi, sai ta rufe wardrobe d'in, ta
fuske abinta, da sauri ya kauda kanshi, a ranshi yace "'yar
lukuta kawai amma ta had'u fa , a bayyane ya ce "dama
mama ce takeson magana dake, zaki iya tuna ta?" Gyada
masa kai tayi alamar NO, dariya taso kubce masa sai ya
dake, okay, " mama itace mamarki, gaisheta zakiyi cikin
tarbiya", " ya ake gaisuwa cikin tarbiya?, " ta tambaya,
dariya yayi amma badan yaso ba, dariyar ce taci k'arfinsa,
ya kuwa zauna kamar gaske, ya gaya mata yanda zata ce ,
ita ko harda maimaitawa tayi irin haka kake nufi ko? Gyada
mata kai kawai yayi, a ranshi yace " 'yar rainin wayo kawai,"
ya kira mama bayan sun gaisa yace mama ga autar ki, but
still fushi take dake, ya mik'a mata wayar, tayi d'an gefe da
kan wayar tace dashi "nice auta?" Yace "Eh, " " to kuma kace
na gaidata cikin ladabi, kuma kace mata ina fushi ya zanyi?"
Karbar wayar yayi ya kashe haushi ta bashi sosai, "malama
idan bazakiyi magana ba ki bari! Mahaifiyar kice kike yiwa
wannan shirmen ! Ke idan baki san darajarta ba ni na sani,
kada Allah yasa kiyi mata magana," a fusace ya mik'e, rik'e
masa hannu tayi, a shagwabe tace "kayi hak'uri zanyi
magana da ita kaji" tsaki yayi mara sauti ya dawo ya zauna,
ya fara dannawa, Wait Wait,ta dakatar dashi, " normal zanyi
magana da ita ko kuma cikin fushi? "
.
ya kalleta rai a bace" cikin fushi da ladabi" "yaya kenan?""
ban sani ba " mik'a mata wayar yayi, ta kara a kunne, sun
gaisa fushi fushi take maganar amma da ladabi kamar
yanda oganta ya umurceta, chan mama tace " ga suhail
zaku gaisa " zare ido tayi ta kalli Ahmad, a hankali tace
"waye suhail dan Allah " banza yayi da ita, suhail kuwa yana
chan yana zuba kamar kanya, matsowa tayi daf dashi ta
d'an bubbugashi, waye suhail, baiko motsaba yace "mata
d'an uwanki ne" sannan ta fara masa magana yanata
complain ta sharesu duk fushin ne takeyi dasu har yanzu,
ita kuwa sai aikin bada hak'uri takeyi ba tare da tasan miye
laifin nata ba suka k'are ya baiwa mama, nan mama ta
shiga mata nasiha akan tabi mijinta, ta na ta In sha Allah ba
abinda ta gane sai d'an yak'e da ta ke muvsu ta na cewa
sorry, Mama ba taji dad'in yanda 'yar tata take mata
magana ba, amma tasan su suka mata laifi, sun yi sallama
ta mik'a masa wayarsa " ki ijiye min a nan " ta ijiye har takai
k'ofa za ta fita saita waigo shi, karaf idonsa akanta yana
mata kallon kamar mayunwachin zakin da ya hango nama,
sauri ya yi ya janye idonsa, murmushi ta masa ba tare da
ya gani ba, ta fice abinta, a ranta tace ashe ma har yanzu
yana sona, kawai dan bani da lafiya ne. Chan ta sami 'yar
bak'a ta kusa kammala wa, sorry black na ijiyeki ke kadai..
.
"No ba komai ai kin je gun mijinki ne" kallon ta kawai tayi,
aranta tace "wannan black akwai bala'in shishshigi a gunta,
suka k'are aikin, ta fito zata d'aki kichibis suka yi da shi , "
Sorry " ta fad'a fuska a sake, bai kula taba ya gangara
k'asa ya wuce gun aikinsa.
.
*********
Alhaji Ibrahim ya shirya tafiya wani aiki a morocco, amma
yaga bazai iya tafiya baiga yarshi ba, musamman yanda
take fushi dashi, shiryawa yayi ya kamo hanya, saida ya iso
Abuja sannan ya kira Ahmad ya shaida mishi, yana gari,
Ahmdy cike da farin ciki ya tarbo Dady su ka wuce gida, sun
tarar da Suhaila, 'yar bak'a na koya mata yanda ake sinasir,
gidan ya had'e da k'amshi, Dady cike da farin ciki yau zai
had'u da 'yar autarsa, sunyi sallama, ta fito da sauri jin
maganar Ahmdy da rana tsaka. Sannu da dawowa, ta fad'a
ta kalli mutumin, lokaci d'aya ta gane shi, da yake ta tuna
wasu abubuwan da suka faru lokacin da take 'yar shekara
takwas haka, so ta gane Dady, cikin girmamawa ta
gaidashi, Dady yana ta jin d'ad'i, Ahmdy ya sami gu ya
zauna, a ranshi yace "wato yarinyar nan ta raina min wayo
ko?. Zaki gane Dady d'inki, dama ni nasan duk kissa ce ta
mata" Dady bari na shiga ciki, Ahmad ya barta da Dady
d'inta, nan fa ya fara mata maganar da sam bata san ina ya
nufaba, sai rudar da ita yakeyi yana bata hak'uri, "wai mi
suka min da suke bani hak'ur'i?". Haka ta k'are zaman ta
da rashin sanin kan zance na Dady har sukayi sallama,
Dady zai tafi, ta haura sama ta kira Ahmad sai kuma taji
olooo, dan ba zata iya shiga d'akinsa ba, sai ta dawo, "Dady
ka mishi waya inaga baya gida" "ke Ina wayar ki ?", "ta
b'ace ne Dady ", "ok". Ya kira Ahmad ya sauko suka yi
sallama ya wuce. Za ta haura sama ya janyota da k'arfi
saida ta fad'a jikinshi, " kin raina ma kanki wayo ko? Wato
ni ne baki sani ba, amma kin san iyayenki, miyasa baki iya
playing game ba?", kallon ta ya yi ido cikin ido sai kuma ya
saketa ya juya ya wuce dakinsa tsaye ta yi ta na kallon sa..
.
************
Yau da gobe Suhaila tayi wata daya a gidan Ahmdy, bata
ganinsa sam bare suyi game d'in da ya ke ce wa su yi, duk
tabi ta damu, komai na ta a hankali ta ke yinsa sabida ta
fahimci kamar ta MANTA KOMAI ne, abin duniya ya isheta,
ta yi kuka har ta barwa Allah, tun ta na shiga hanyarsa ya
na disgata har ta daina kula sa, harkar gabanta data
yaranta ta saka gaba, ba abinda ta rasa a gidan komai
normal. Ahmad kuwa a hankali sai yake ganin kamar
abinnan da gaske takeyi, sabida ya aunata a hanyoyi daban-
daban ba tareda ta sani ba kuma ya na ganin lallai kamar
da gaske ta manta komai, sai ya tuna lokacin da "sa" ya
wurgar da ita kanta ya fara bugun k'asa, may be kan ya
sami matsala ne tadan yi missing din wasu abubuwan,
yana son ya kaita asibiti gashi ta d'auke masa k'afa gaba
d'aya, d'an gaidashi da take duk ta daina, duk yabi ya
damu, shima k'arshe ya yanke shawarar zai kaita asibiti
kawai a duba ta. Da wuri ya dawo gida ya tarar da su ita da
yara su na wasan 'yar b'oye idan aka kama mutum shi
kenan, idan ba'a kama shi ba sai aje a goyashi, to kullun in
su ka yi, idan ita ta ci sai su ce 'Dady zai goyata", ana ta
tara goyon har yakai tara. "
.
yeeee Dady zo ka goya Mumy, tana bina bashin goyo hudu,
Rukayyah kuma tana binta biyar, dama munce kai za ka
biya ta," Surayya tace " Mumy zo Dady ya biyaki", "na yafee"
kawai tace musu ta wuce d'akin ta. Tana zaune bakin gado
ta tallabe kumatunta da kanta, sai ta ji shigowarsa, k'in
d'agawo tayi bare tamar magana, yazo kusa da ita, ya dad'e
yana kallon ta, sannan yayi magana "Suhailah, ki shirya
gobe muje hospital a miki check up," kamar bata ji shiba
haka tayi, tayi baya da kanta ta kwanta idonta a rufe, ya
tsura mata ido sosai, har cikin ransa yake jin yasan ta
amma ya kasa tunawa, ya gaji da tsayuwa sai kawai ya
wuce dakinsa, haka ya kwana yana addu'ar Allah yasa
abinda yake tunani bashi bane. Da safee bayan ya k'are
shiri yazo gunta, "ba nace zamu hospital ba?", "Bazan jeba" ,
haka kawai ta fad'a" murmushi yayi "haba maman twins"...
tun kamin ya fadi abinda zai fad'a ta karbeshi, "da gaske
yarana twins ne?", Fuskanta a washe, "idan mun dawo zan
miki bayani", ta turo baki" kaine Dady tun yaushe kasan
bani da lafiya amma kak'i kaini hospital", "kiyi hak'uri yanzu
zamu tafi", haka ya mata wayo ya lallab'a ta suka tafi,
bayan bincike da kwaje kwaje aka gano cewa ta sami
matsala a brain d'inta.
.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.! Hankalinsa ya tashi
matuk'a gashi iyayen ta satin nan zasu zo gunta kuma
zasuyi kwana biyu, tabbas baya son suzo su sameta haka,
za su ga sakacinsa, na rashin kula da lafiyarta, har fiye da
wata daya, kuma duk sanadiyar sa hakan ta faru. Likita ya
tabbatar masa da cewa idan ta sami natsuwa da kwanciyar
hankali a hankali komai zai dawo, daga asibiti direct gun
abokinsa ya wuce ya ce ya masa bucking zai kai madam
waje a dubata....

No comments

Post a Comment