Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NA MANTA KOMAI Part 4

NA MANTA KOMAI Part 4
.
Haka take bacci a palo tana jiran mijinta, sai dai ta farka ta
ganta a d'akinta, tare da yaranta yau kwana biyu kenan.
Cikin dare ta farka ta kasa bacci ta tashi ta zauna, tana ta
kama tasha, ta dai rasa abunda ke mata dad'i, ta rasa gane
kan komai "to wai haka ake aure dama?" tambayar da ke ta
yi mata yawo ke nan cikin kanta, ta k'ara d'auko d'an littafin
nan data gani a kayanta ta k'ara karantawa, taga yanda ake
soyayyyah ake tarbar miji, a masa girki, kwalliya, uwa uba
kwanciya, amma ita ko k'eyarshi bata gani bare ta mishi
wani abu, a zuciyarta ta na ganin hadda laifinta, da take
bacci da wuri, kuma take tashi letti, dole ta dage ta rik'a
jiranshi har ya dawo komin tsawon dare, amma ace baka
magana da miji, ko ganinsa ma bakayi ta na ganin kamar
hakan ba dai dai bane,. Kodai akwai wani abu da bata sani
ba bayan wanda aka rubuta a littafin? Wata zuciyar ta raya
mata ta kwashi yaranta yau su kwana a dakin shi kawai,
amma kuma sai ta fasa, "to wai dama haka muke dashi, ni
kuma miyasa bana iya tuna komai ne? Mi yake shirin
faruwa dani ne? Kamar akwai abinda ya faru amma na kasa
tuna komai WAI MA YA SUNANA?" A haka tayi ta tunaninta
ta k'are tayi kukanta sannan bacci yayi gaba da ita. A haka
sai da Suhaila tayi sati d'aya bata ga mijinta ba, kullun itace
hidima da yaranta, gashi wani sonsu ta ke ji a ranta kamar
me, ta saba da su kamar hauka. Rannar da gari ya waye
suka shirya kamar kullun sai Surayya ta kama hannunta
tace "Mumy miyasa bakya son kaka Rabi?"
.
A ranta tace waye kaka Rabi kuma?" Ta tambaya, " To yau
kizo muje ki gaishe da, kullum ita take gaya mana ranar da
zakizo har kikazo, ko bakya sonta ne? Rukayyah ta
tambaya" da sauri Suhaila ta gyada kai, "ina sonta mana,
nama fiku sonta" oya muje ku rakani, "amma ku tsaya, a
cikinku wa zai gaya min idan naje gaidata da safe ya nake
ce mata?" Yaran suka kalli juna, suna murmushi su kace
"Mumy ai baki taba zuwa gurinta ba" nan ma kanta ya k'ara
kullewa, a ranta tace" ban taba zuwa gurinta ba? To ko bata
dad'e gidannan ba" yamutsa fuska tayi ta basar, "oya to ku
zo muje" ta rik'e hannun ko wacce suka tafi gun kaka Rabi.
Da yake sassan gidanta daban yake amma a jikin babban
gidan gonar ne, dan tace ita bata son bene, ina ruwan yar
tsohuwa Rabis. Suna shiga suka ruga suka rungumeta suna
kaka Rabi oyoyo suna dariya, tace "ni dai to kuyi a hankali
dai karku k'arasa ni kun sami Momy kun manta da kaka
ko?" ta fada tare da rungumesu, tana "fadin lale marhabin
da Momy, tare kuka zo? Shigo ciki mana keda gidanki,
bisimilla zauna ga kujera nan" haka kurum sai Suhailah taji
tana jin kunyar kaka Rabi, a ranta kuwa sai sak'e-sak'e
takeyi, "ko waye wannan kuma oho?"
.
Tunda tazo take jin sunanta, tama taba hangota sau d'aya
amma bata tab'a ganinta ba sai yau, sai kame kame take
sabida kayan jikinta, Kamar dai ya dace ace tasa kayan
traditional irin na jikin kaka Rabi, "to waima in dai nan take
zaune ai ya kamata ace ta tab'a zuwa gaisheta, kai tabbas
akwai wani abunda bata sani ba, to menene wannan abun?"
Dama ba wando da riga ta saba, ta mayar dasu kayanta
koda yaushe su take sawa, tsaki tayi a ranta tace "da ba
tazo dasuba, tun da dai tana kyautata zaton uwar mijinta ce
tunda 'ya'yanta suke ce mata kaka, " nikam na shiga uku,
na kasa gane komai! Ko mijin nawa ina yake oho? Kamar ta
tambayi kaka ina yake, sai ta tuna a littafin da ta karanta
ance a rik'a boye sirrin miji, wannan ma sirri ne sai ta fasa.
Haka ta zauna ta gaisheta cikin ladabi, "kaka tace Suhailah
ya jikin naki,kin samu sauk'i ko?" nan take gabanta ya fadi,
"ashe bani da lafiya ma?" Ta cigaba "Ahmad yace min kin
fadi ne baki ji dadi ba" shiyasa ma baki zo ba, kuma nace
zan lek'oki yace wai kina jin kunya ne da kin wartsake zaki
shigo, shi yasa baki ganni ba nima, jikin da sauk'i ko?" tayi
murmushi ta rufe fuska, cikin jin kunya tace "eh da sauk'i
sosai," ta dad'e a duk'e dago kan da zata yi sai taga kaka ta
d'auki waya ta kara a kunne tana magana, tashi tayi da
sauri ta fita, kaka tayi murmushi "ko ta d'auka sirri zanyi
yarinya mai kunya" Suhaila kuwa tana tafe tana sak'e sak'e,
lallai bata da lafiya, shi yasa take jinta kamar ba itaba, ta
tuna ko sunanta ta manta, idanuwanta suka cika da kwalla
ta shiga d'akinta ta k'ara bincike yan kayan da ke cikin
jakunkunanta biyu, nan ma bata ga komai ba da zai sa ta
tuna wani abu, ta k'ara bubbud'e duk wani wuri da take
tunanin zata ga wani abu sam bata ga komai ba, anan ta
k'ara fashewa da kuka, kuka sosai take har da sheshsheka,
to me ya Sameta?
.
Tana nan zaune tana kukanta taji yaranta na hawowa sama,
suna ta surutu, tayi sauri ta goge fuskarta, kamar zata
shige bayi ta wanke fuska, sai ta fasa, koda suka shigo tare
da Dady suka shigo, shima bata san sunanshi ba, in ba dan
taji kaka Rabi ta fada ba, idanunta suka k'ara cika da kwalla
ta mike tsaye, taso taje ta rungume shi, kamar yanda ta
gani a littafin data karanta, (kada yara su hanaka yiwa
mijinka soyayya) amma ta kasa, sai kawai tace "sannu da
zuwa" ya kalleta a karon farko tun bayan zuwanta gidanshi,
sabida a palo ma idan ya ganta tayi bacci d'aukar ta kawai
yakeyi ya kaita d'aki ya shinfidar dama wutar palo a kashe
take, baya wani kallon ta, gata da nauyi kuwa, amma haka
yake tallabota ya kawo daki, ta k'ara ramewa, ga idonta
cike da kwalla yayi jajir dashi, murmushi kawai yayi, a
ranshi yace "zaki k'are felek'en ki ne yarinya" amma da
mamaki wacce yaji labarinta shez always happy and active,
amma yanzu duk ta canja cikin sati d'aya, idan ma
saukowa tayi ai ya dace ta kawo kanta ne kawai, bawai ta
tsaya jan aji ba. Ya amsa ta sama sama "yauwa sannunki "
Matsowa tayi maimakon ta rungume mijin sai ta rungume
yaranta "Mumy wa ya dakeki kike kuka? Ko kaka Rabi ce?"
Tace, " no abune ya shige min ido yanzu, amma na hureshi"
ta dago ta kalli mijinta a karon farko bayan sati d'aya,
kamewa yayi, yace" kunga na kawoku gunta dama wasu
files nazo dauka, bye d'inku" suna murmushi suka d'aga
mai hannu "bye Da88dy" ya juya zai fita kenan tace "ina son
magana da kai" ya juyo ya kalleta, sai kuma ya cigaba da
tafiya sai da yakai k'ofa har ya fice sanan " yace ina zuwa"
.
Fitarshi da kamar minti biyar Nanny dinsu Auntie 'yar bak'a
tazo ta lallabasu, da k'yar suka yarda suka bar ta, 'yar
bak'a ta tafi dasu dan tayi masu wanka da shirin bacci
dama dare yayi, ga dukkan alamu Ahmad shi ya turo ta.
Fitarsu da kusan minti goma, sai ga Ahmad ya shigo d'akin
cikin k'ananan kaya bak'in wando da farar shirt, duk da
hankalinta a tashe yake, dan jinta take a rude, a ranta ta
yaba da shigarshi, da alama daga wanka ya fito, sai
k'amshi yake, ta dago kai ta dube shi tayi mashi murmushi
wanda ya kasa gane mi yake nufi, sai ya basar dai-dai
lokacin da yake shirin zama saman wata kujera da ya jawo
daga gaban mirror ya kawota gab da bakin gado kusa da
inda take zaune ya zauna, ya k'ura mata fararen idonsa,
bakinshi kamar ya shafa lipstick sai maik'o yake, sai ya
burgeta har cikin ranta, yace "miye maganarki?" yana tsotsa
minti a hankali, ta kauda kanta daga dubanshi ta tunzuro
baki kadan, wai ita ala dole shagwaba, dan a littafin data
karanta ance shagwaba tana sanya mace ta saye zuciyar
mijinta lokaci daya,namiji zai ga yanda kika k'ask'antar da
kanki gabanshi kina harkar yara, bare kuma shi dama namiji
kamar rak'umi yake a gun mace, idan baki iya sarrafashi ba
to kuwa zai zame miki kamar ingarmar doki da zai zo yafi
k'arfinki, dole sai ana hadawa da shagwaba da lallabawa, a
book din an kawo misalin yanda za'a rik'e miji a nuna mishi
fushi, ba wai da daure fuska da kunbure kunbure ba, da su
gaba ba, no da kissa da kisisina irin ta mata, an kawo
misalan yanda ake yiwa miji shagwaba da tasirin shagwaba
a gun miji, wanda sune Suhailah take jarrabawa. A sanyaye
a shagwabe take maganar, tace "nasan bani da lafiya,
amma ya kamata ai kayi mani bayani," yanda ta mishi
magana cikin sanyin murya, da yanda ta shagwabe masa
ya burgeshi, wanda yake ganin kamar gaba d'aya ta sauko
ta barwa Rabbana komai. Yace "wane irin bayani zan miki
kuma? Bayan kin san baki da lafiya mi zan miki?" Ido ta
dago ta mai wani kallof,, saida yawu suka sark'eshi, saida
yayi guntun tari, a ranshi yace "wato yarinyar nan ba
k'aramar 'yar rainin hankali bace" duk suka yi shiru na wani
lokaci sanna ta cigaba da cewa, "dama haka muke zama
tuntuni baka zama gida? Kuma bama magana?" Dariya yayi
sosai, ya kalleta, sama har k'asa ya girgiza kansa, sai kuma
ya d'aure "Please kada ki nemi ki bata min lokacina, inada
ayyukan da ya dace nayi, idan kin hada wani plan sai ki
nemo ni, but now, game is over for you" ya mik'e zai wuce
da sauri ta rik'e hannunsa, sokoko yayi yana kallon ta, ta
zaunar dashi ya kuwa zauna. "Zan maka tambaya uku
zuwa biyar duk lokacin da kake free sai ka bani amsa" "
.
please wacece ni? Miye sunana? Ina iyayena? Kuma inane
naje da yarana suke murnar dawowata?" Ta kalleshi sosai,
taci gaba "nifa ba abinda na sani a kan kaina, bare wani
nawa kai kanka ban san sunanka ba, amma nasan kai
mijina ne, tunda ga yaranmu nan da nake tunanin yan biyu
ne, suma da ace banga gashin kaina da nasu iri daya bane
wallhy da nace ba yaran mu bane, dan Allah duk lokacin da
kayi free ina jiran amsoshi na" ta mik'e da sauri zata nufi
hanyar bayi, dan kuka na neman subuce mata, rik'o hannun
ta yayi ya juyo fuskarta suka fuskanci juna "Thank God da
kika san cewa I am your husband, yanda kika gane cewa ni
mijinki ne, wannan ma ya zame miki assignment kije ki
gane amsar sauran tambayoyin ki" ya nunata da
hannu,"shame on u da kika yi failing game dinki ranar farko,
kin kasa winning duk zamanki smart girl," sauke kafada
yayi, but still you try, u can go on, may be next episode u
can win, but now u fail Zeroooo" ya fadi zero din yana zare
ido, yanzu muna 1-0. Ya kalleta kallon kinyi missing yace,
"zaki zama fa gud player but u need more & more training"
tsaye tayi tana kallon sa, gabaki daya ya k'ara batar da ita,
ya k'ara dagula mata lissafi, ya k'ara sata wani duhu bayan
wanda take ciki, ta yanda bata ma san ta inda zata kamo
lamarin ba. "kina iya wucewarki, ina jiran next episode" ya
fada yana murmushi juyawa yayi ya wuce abinshi, har ya
kai bakin k'ofa sai kuma ya tsaya yace "idan kin shirya wani
din ina d'aki na ki kirani, da kin bi nan corridor direct zai
kaiki d'aki na, dan nasan shima zaki ce baki san gurin ba"
ya juyo da kanshi da kafad'arshi ya kalleta, idan kuma kin
yarda game is over duka d'aya ne a gurina, ya wuce abin
shi duk da bata san ina zancen shi ya nufa ba ta sami kanta
da bashi amsa da cewa, "d game is not over, yanxu aka
fara ma" da k'arfi ta fad'a ta yanda zai jiyota. Murmushi
kawai yayi ya wuce abinshi, ya shiga d'aki yana tunanin
wannan yarinya, tama raina ma kanta wayo, dan ba shi ta
rainawa wayo ba, ya cije yatsa, ya naushi iska, "miyasa ban
biye mata bama? Da sai na bata amsa kamar yanda ta
buk'ata, dan kuwa zata yi dadin playing, dan zan ta winning
dinta ne, ko ba komai she's beautiful & she make me happy
today, in fact she make my day, kan gado ya fad'a yana ta
tunanin Suhaila da abinda ta mishi, yana ta murmushi,
mata akwai fi'ili, yana ganin fuskarta kamar ya santa,
musamman lokacin da ta mishi wannan shagwabar tata,
amma ya kasa tuno ina yasan ta, shi duk ya d'auka da
gaske game take dashi. Bai san seriously Suhaila tayi
loosing memory dinta bane.
.
********
Can gidan su Suhaila kuwa da suka jita shiru, sai suka yi
tunanin ko har yanzu bata huce bane game da irin auren da
akai mata, tunda ta nuna bata so, k'arshe ma tak'i bari
akaita ne, tayi fushi dasu, dan haka yasa ta kashe wayar ta,
dan duk wanda ya buga baya samunta, idan aka tambayi
Ahmad sai yace tana nan lafiya lau, mama ce ta damu akan
sai tayi waya da autarta, ta kuwa dami Ahmad akan ya kira
ya bata suyi magana! Ya kenan?

No comments

Post a Comment