Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

NA MANTA KOMAI Part 2 & 3

NA MANTA KOMAI Part 2 & 3
.
Na H.m Jamo
.
GIDAN SU SUHAILA.
Aunty Rukayyah ce ta shigo d'akin ta na ta fad'a "Waike
Suhailah mi yake damunki ne? Ace tunda aka fara hidimar
aurenki ba ruwanki da komai, ba ruwanki da kowa! To
malama ba damu zakiyi fushiba da Dadyn ki za kiyi fushi,
shida kike ganin ya miki shishigi a rayuwa, ta qara so cikin
d'akin wai ma kina ina ne inata magana kinyi banza dani.?"
Turus tayi ganin ba Suhailah ba labarin ta, ta ja guntun
tsaki, ta lek'a bayi nan ma ba ta nan, "Ina yarinyar nan ta
shiga ne!?" Ta fito tsakar gida tana tambayar mutane ko
akwai wanda yaganta!? amma kowa yace rabonshi da ita
tun jiya, wasu kuma suce tun da asuba, nan da nan aka
bazama neman Amarya, amma bata ba labarin ta, aka kira
Dady akan ba Amarya fa kada a d'aura Aure, Dady yayi
murmushi, yace "Aure kam ba fashi sai an d'aura." Ahmad
ne yazo ya sami Dady, yace su kwantar da hankalin su
yasan gunda take, bayan d'aura Aure zaije ya d'auketa ya
wuce da ita, kawai a had'a mata kayan ta, sannan hankalin
danginta ya d'an kwanta, bayan d'aura Aure Ahmad yaje ya
d'auketa gunda tayi da Yusuf, tun lokacin da ta bude k'ofa
ta fara gudu ne ya kira Su ya sheda masu cewa ya ganta
kuma Suna tare lafiya lau. Sunji haushi, duk da cewa dama
ba wanda zai rakata Abujar amma sun so ko yar hud'uba ce
a mata harma yanda kan Suhaila yake rawa, amma hakan
bai samuba kuma ta kashe wayarta.. Bayan ya d'auketa sai
ya wucee da ita Abuja..
.
***********
Yana isa yayi parking din motar ya fito abinshi ya shige
gidan gonarshi. Amfi minti talatin da tsayawarshi, masu aiki
sun kwashe yan kayan Suhailah dake cikin motar, amma ita
Suhaila bata fitoba, a ranshi yace "wai yarinyar nan mi take
nufi ne??" ya koma wajen motar ya sa k'afa ya d'an shureta,
amma maimakon ta tashi sai ta qara juyawa tana
murmushi, ta cigaba da baccinta.
.
kilan Suhaila taci gaba da mafarkinta ne.... Tsaki yayi
aranshi yace "kyaji dashi yarinya kin riga kin zama matata"
komawar shi yayi cikin gida, yaje yayi wankanshi da ruwa
masu d'imi, yaji jikinsa yad'an warware da gajiyar tuk'i
yasamu guri ya kwanta sai bacci.!! Sai k'arfe biyu ya farka,
ya tashi ya lek'a d'akinta da ko ina amma bata ba labarin
ta, tsaki yaja wato har yanzu tana cikin motar kenan, ya
gane bata da niyar shigowa ciki, yaje gun motar ya kuwa
hangota tanata bacci abinta, bai ma tsaya bata lokacinshi
ba wajen tada ta, kawai d'auko ta yayi ya kaita d'akinta da
yasa aka gyara mata cikin d'akunan dake sama, ya ajiyeta,
a ranshi yace " Hmmm.!! mata akwai fi'ili ita kuma nata
borin kunyar haka take yinsa" .... Yayi d'an guntun tsaki
chikin ranshi ya kashe wutar d'akin ya wuce abinshi... Duk
da kasan cewar gurin gidan gona ne, gidan ya tsaru fiye da
tunaninku masu karatu, "ni kaina M. Jabo dana shiga gidan
saida naji kamar ace gidan J.S d'inane, habawa da zamu
soye a gurin ba kad'an ba dan zaiyi d'ad'in soyewa.."
Ahmad mutunne mai tsari, gaban shi da bayan shi, yadda
yake a tsare physically, haka duk wata harka tashi take a
tsare, haka mazauninshi abinshi gwanin burgewa...
.
YANDA ABIN YAKE AKAN YUSUF.
Bayan fitowar Yusuf daga wajen Suhaila, bai tsaya ko inaba
sai wajen Ahmad, ya gaya mashi duk yadda sukayi da ita,
abunda bai gaya mashiba kawai shine ya rungume ta, for
the first time (a karon farko)duk tsawon rayuwarsu, sanin
Ahmad ne da halinsa yasa ko giyar wake ya zuk'a bazai
furta ma Ahmad hakan ba.. Wannan sirrinshi ne har
kabarinshi sai ku masu karatu da ni Jabo yar gane-gane
dana gano... Ahmad yayi murmushi chikin ransa, yayi ma
Yusuf godiya ya dafa kafad'arshi ya wuce abinshi, aranshi
yake cewa "wannan yarinya daban mamaki take," ya karbi
makullen motar, amma bai tafiba a lokacin sai da aka
d'aura Aure akayi reception, mutane suka fara watsewa
Sannan ya kama hanya, Yusuf har ya fara jin Ahmad ya
bashi haushi a lokacin... Ya za'ayi ya ijiyeta awa sama da
biyu, bayan ya gaya mishi tana chan tana jira, tsaki yaja,
"duk nina janyo mata ai," duk da dai yasan bashida yadda
zayyi dashi tunda Kudin da Ahmad ya bashi duk rayuwarshi
ba wanda ya taba bashi su, duk akan ya kula mashi da duk
wani moves din Suhailah .....!!!
****************
Washe gari da Suhailah ta tashi daga bacci, ta tashi da
matsanancin ciwon kai, kuma duk inda ta juya jikinta ciwo
yake mata, tana Wash! Wash!! haka ta tashi dak'er ta
zauna, ta kalli nan ta kalli chan, bata gane ina take ba sam,
jeem tayi, ta dan girgiza kanta, amma bata gane komai ba,
ta ta shi ta rik'a tura k'ofofin da suke d'akin har ta gane
bandaki ta tura kai ciki, nanma kalle kalle ta rik'ayi sai kuma
ta tsaya kunne kunne, a ranta tanajin kamar akwai abinda
akeyi a gurinnan Amma bata gane ko miyeba, kuma tanajin
kamar akwai abinda ya dace tayi yanzunnan amma bata iya
tuna miye, lokacin taji cikin ta na k'ugi alamar yunwa takeji
kamar ta mutu, ta mik'e tsaye, ta nufi k'ofa kenan zata
bude idonta ya kai ga mirror d'in d'akin,duk abunnan sai
yanzu ta kula da fuskarta a mirror, ta kalli kanta sosai,nan
take gabanta ya fad'i tsoro ya kamata,ta tambayi kanta ta
madubi, ko Wacece wannan....." who are you..."abun
mamaki abun tsoro, ta kasa ba kanta amsa, ai kuwa sai ta
sa ihu, k'walla ne ke kwarara daga idanuwanta sabida
kukan da take baji ba gani......
.
Can cikin bacci Ahmad yaji ihunta, Ahmad da sauri ya fito
daga d'akinshi, a dai-dai lokacin da yayanshi Surayya da
Rukayyah suka fito daga nasu d'akin, suka iso inda yake
kowacce ta kama hannu d'aya Suna murje ido alamun
yanzu suka tashi daga bacci, had'e da murmushi a
fuskarsu, suna murnar ganin Dadyn su, dan jiya koda ya iso
sunyi bacci, suna isa dai-dai k'ofar d'akin Suhailah ta bud'e
k'ofar ta fito tana yan hawaye, daganinta duk a tsorace
take, yara kuwa da ganinta sai suka hau tsalle suna murna,
da sauri suka je suka rungume ta, suna "oyoyo Mumy!!!
oyoyo Mumy!!! " nan da nan Suhaila cikin dubara ta goge
k'wallan idonta.
.
Yaran sun bata sha'awa, ta d'anyi murmushi ta rungume su
itama, ita kam gaskiya tayi mata yawa, yanxu ita take da
way'annan yaran k'yawawa haka,..??? Rukayya ta juya
tace "Dady yaushe ka kawo mana Momy....??" yace "jiya
kuna bacci tazo..." Suhailah a aranta tace "Idan way'annan
y'ay'anane, kenan wannan shine mijinna...?" ta saki baki
tana kallon su ba tare da tasan takamaiman gaskiyar
abunda takeji ba, ta k'ara d'ago kai ta kalleshi aranta tace
"amma mijina fa ya had'u gaskiya, y'ay'anmu kuma masha
Allah, kamar y'ay'an larabawa" koda yake, itama Ba daga
bayaba wajen kyau... Yaran basu ko wanke baki ba suka ce
" Momy yunwa mukeji kuma Momy ke zaki bamu abinci,"
haka suka ja ta suna murna zuwa dinning table, da basu
kaita gurin ba, da batasan ko inane dinning table ba, kamin
su k'arasa Dady yace "kunyi brush kuwa??" Surayya tace "
no Dady, yanzu muka tashi," " maza ku wuce a muku
brush," "Dady mu Momy zata mana," suka fada suna kallon
Suhailah, sai ga wata mata ta fito, ta duk'a har k'asa ta
gaida Suhaila, ta amsa a sake, suka mak'ale ma Suhaila ala
dole ita zata musu, yace " kunsan dai ba zakuci abinci ba
sai kunyi brush" suka turo baki na shagwaba "Momy muje
ki rakamu" haka suka ja Suhaila tana kallo aka musu brush
sun k'i yarda a musu wanka, sannan suka fito, suna rik'e da
hannun ta, cike da nishadi.
.
Suka k'arasa ta bubbuda abincin, ta zuba musu dankali da
Egg tana basu Suna bata, itadai ci take amma bakinta wani
iri take jinsa tunda batayi brush ba, sukaci suka k'oshi
sannan sukace "Momy yau ke zaki mana wanka." haka
suka jata har bayin dakinsu, tace " kowa yayi wanka mu
gani kun iya wanka" ai kuwa suka fara wanka suna wasa da
ruwa, abin nema ya samu, saida suka gaji suka ce "mun
k'are suka fito, oya kowa ya shirya mu gani, suka shafa mai
kamar yanda sukaga nany dinsu tana musu, suka shirya
kansu tsaf cikin wando da riga mai kama da irin wanda ta
sanya, purple riga da black jeans. Momy kayan mu irin
d'aya da naki, Suhaila kam dadi take ta ji wai tanada 'ya'ya,
har biyu, yan mata dasu, aranta tace " kenan kullan haka
nake musu wanka na shiryasu? Gasu kyawawa dasu, tayi
murmushi, kyaufa yayi, har cikin zuciyarta takejin sonsu,
itakam har ta mance da ciwon da jikinta yake yi, duk da
yayi tsami sosai, kuma da d'an tabo a hannunta, ta kula
yaran akwai mai kula dasu, da kuma wata tsohuwa da ta
hango a gidan, amma batasan ko wacece wannan tsohuwar
ba. Rannar haka suka wuni tare da y'ay'anta, cike take da
nishadi, da ta d'auki Rukayya, sai Surayya ma tace sai ta
d'auketa, haka sukayi bacci a jikinta suna kallo a palo, ta
rasa gane komai itakam. Nanny dinsu tazo ta kwashe su ta
kai su d'akinsu, ta manta sam da ciwon da kanta da jikinta
keyi, sai da tayi shirin bacci sai tace bari tayi wanka itama,
ta shiga toilet itama tayi wanka, kamar yanda y'ay'an ta
sukayi, ta fito ta shafa mai, ta saka tufafi har a lokacin dai
ba ta jinta dai-dai ta kwanta ta fara tunanin wacece ita
haka!!!........
.
Ta kwanta sai juyi take, amma ba abinda yake zo mata, duk
tunanin duniya tayishi amma bata tuna komai akan kanta,
iyakanta abinda ya faru da ita yau take iya tunawa, yaranta
mijinta sai wankan da sukayi, juyi take tana baiwa
k'wak'walwarta wahala, Amma shiru, dagyar ta tuna wasu
abubuwan da tun tana shekara goma suka faru, daga nan
bata k'ara tuna komaiba. tashi tayi ta shiga dube- dube a
d'akin nata, ta bud'e wannan ta bud'e wan chan, anan taga
wasu littafai, ta dauko, abin mamaki sai taga tana iya
karanta wa, littafin da yafi jan hankalinta shine KULA DA
MIJINKI yanda ake kula da mijine, ta d'auko ta jujjuyashi
sai kawai ta koma bakin gado ta zauna, ta fara karantawa,
tanayi tana murmushi ita kad'ai, har saida ta karanceshi
tsab sannan ta koma ta kwanta... Bayan ta kwanta sai ta
fara tunanin ina mijinta? Tun ganin da tayi wa wai mijinta
da safe, bata sake ganinshiba, sai ta sauko k'asa, nan ta
zauna palo tana jiran isowarshi domin itafa kanta a d'aure
yake, gata matar aure harda miji uwa uba harda yaya biyu,
tirkashi!!!, dole tayi mashi tambayoyin da in ya bata amsa
zata iya gane ita wacece dan jinta takeyi kamar
TA MANTA KOMAI....
.
Tashin hankali baa sa maka rana,da alama dai Suhaila ta yi
loosing Memory d'inta ne a yanda na fahimta,... Can kuma
Ahmad, sai tunane-tunane yake shin abun nan, pritending
take kamar bata san komai ba, dan yasan kissar mata yawa
gareta, ko kuwa akwai wani abune?? Gani yake kamar ta
amincene ta zauna da shine a matsayin mijin nata, shine
take basarwa, to lallai yana ganin hakanne, ta amince ta
zauna dashine dinne, yayi dan murmushi wanda ya fito da
kyanshi a bayyane, kai mata akwai iyayi, kalli yanda ta
fuske kamar ba itaba a bayyane yace "Mata! Mata!! ya
kada kai ka barsu kawai....." Amincewa tayi dan ya zama
dole, domin kuwa bakin alk'alami ya riga ya bushe, an riga
an d'aura masu Aure shi da ita, kuma ba saki har abada,
Ahmad kenan da masu aikin gidansu suka saka masa suna
Alhaji Rabo..... Na zama mijin Suhaila kenan, yayi
murmushin da bai kai ciki ba, amma azuciyarshi har yanzu
inya tuna wasu abubuwa sai yaji wani baqain ciki da
zuciyarshi ke tafasa, kuma har yanzu ya kasa cire wannan
abu a zuciyar shi, wanda duk sadda ya tuno abin yake jin
zafi har yaji ya tsaneta, amma yayi ma mahaifinta
alk'awarin zai rik'eta amana a matsayin matarshi, amma ya
za'ayi yayi hakan,!? bai saniba har yanzu,!! Shiyasa lokuta
da yawa sai yaji Kamar yacema mahaifinta ya fasa
aurenta,amma kuma sai ya kasa....!!
*************
SHEKARA UKU DA SUKA WUCE
Shekara uku da ta suka wuce,... lokacin da mahaifan
Suhaila suka dawo daga umra, Ahmad tuni ya riga ya koma
k'asar Holland, basu sake haduwa da Ahmad ba, dan bai
sake zuwa Nigeria ba, sai lokacin da ya samu labarin
rasuwar yayan shi da matar yayan shi, sun kuma bar baby
dinsu Surayya Just 2month da haihuwa, yana nan gida
yazo ta'aziyyar yayan shi, sati daya aka yiwa Ahmad waya
aka gaya mashi ya dawo gida, domin matarshi na cikin
mawuyacin hali,rabon suyi sallama, yana isa akayi mata
C.S aka ciro babyn cikin ta, ita kuma ta rasu,ya sama Baby
dinsa Suna Rukayyah...sunanda matarshi takeso take kuma
k'auna kenan shi kuma ya saka mata Rukayyah..
********
Rasuwar yayanshi sunyi magana sosai da Alh Ibrahim
mahaifin Suhaila, inda ya gaya mashi abubuwan da yawa
da bai sani ba, wanda yake zaton shine yayan nashi ke
cewa zai gaya mashi, Amma kuma Allah ya masa cikawa,
asalin samun gonar da suke ciki yanzu kenan wadda da
tana hannun yayan nashi ne kamin ya rasu, duk makircin da
Alh ismail ke k'ullawa,wanda ya janyo accident d'in motar
yayan shi, ya yi sanadin rasuwar yayan nashi da matar
yayan shi, amma har yanzu dai ana kan bincike, dan a gano
gaskiyar abinda ya faru, wannan dalilin yasa Ahmad yasa
ya tattaro ya dawo gida don yaci gaba da harkar bussines
din mahaifinshi da yayan nashi.!! Ba'a dade ba, Alh Ibrahim
ya neme Ahmad da ya auri y'arshi y'ar autarshi Suhaila,
wacce duk cikin yaran shi yafi k'aunarta sabida tsananin
kama da takeyi da mahaifiyarsa. Ahmad kuwa ya kuma
amince da auren Suhaila amma ya amince ne bawai dan
yana sontaba hasalima ya tsaneta tun tana yarinya data
mishi wani abu, kawai dan ya lura Alh Ibrahim mahaifin
Suhaila mutun ne mai mutunci kuma shi kadai ya yadda
dashi a cikin abokan mahaifinsa, bayan an bashi Suhaila
akace kuma an bashi lokaci har sai ya shirya sannan ayi
auren, ************ A ranar a aka aje maganar auren sa da
Suhaila, Ahmad ya samu kanshi dayi ma duk mutanen dake
aiki a gidan su Suhaila, k'ananan ma'aikatan kampanin Alh
Ibrahim kyautar kud'i dubu goma goma, shi kanshi bai san
dalilin yin hakan ba, sai dai kawai ya tsinci kanshi cikin farin
ciki da annashuwa, dukda yasan bayason Suhaila, tun daga
ranar suka sa mashi suna Alhaji Rabo wanda kowa a gidan
da sunan yake kiransa Ita kuma marainiyar y'arshi da da
yar yayanshi, kakarshi da nanny dinsu ne suke kula dasu,
har suka dan girma, suka fara wayo kullun cewa suke
yaushe za'a kawo masu Momy d'insu, hakan yasa Ahmad
ya bijiro da xancen auren Suhaila, amma badan yana
sontaba, Su kuma yaran ganin Suhaila yasa suke tunanin
mamansu ce, ga kuma madam din TA MANTA KOMAI.
Sabida lokacin da zai tafi daurin auren haka yace masu
zaije ya kawo masu Momy dinsu....
**************
Cikin dare Suhaila ta farka cikin bacci amma ta kasa
motsi,gabanta ya fadi ita da ta kwanta a palo, miya kawota
daki, al'amarin ta fa sai d'ad'a jagule mata yake! "Waima
ina mijinta ne!?" Yayanta ne gabanta, Surayya ta rungumeta
a dama Rukayyah a hagu...tayi murmushi ta k'ara
rungumesu, babu shakka y'ay'anta na sonta, ashe suma
sun farka cikin darene suka dawo wajenta, gaskiyayarane
kyawawa babansu kyakykyawane, Itama ba daga baya ba,
ai kuwa dole su bada result mai kyau da haka bacci mai
d'ad'i ya k'ara kwashe ta.....
.
kira da Dady, itace yarinya ta hud'u kuma itace Auta, Dady
yana matuk'ar sonta ne sabida tsananin kama da sukeyi da
mahaifiyarsa. Asalinsu buzaye had'e da fulani, Alhaji
Ibrahim murzajjen d'an boko ne, irin masu tara suma dinnan
aka, yazo birni gun wani aiki na idanu, a k'auyen Tambuwal
cikin birnin Sokoto inda yaga gari ya masa sai ya dawo nan
da zama, anan k'auyen ya hadu da mahaifiyar su Suhaila,
har suka yi aure, ta haifa mishi yara hud'u mata biyu maza
biyu. Rukayyah itace babba, sai kuma Al- Ameen sai Suhaila
da Suhail wayanda su twins ne, sune k'anana. Harkar
gyaran ido ta karbeshi ba kadan ba, inda ya koma birnin
Sokoto da zama, anan ya had'u da Alhaji Isma'el, da kuma
Alhj Sulaiman sai aka koma kasuwanci. Alhaji Sulaiman
shine mahaifin Su Ahmad, yaransa biyar Mahmoud shine
babba, sai Zainab, sai kuma Ahmad da Fatima, sai autarsu
Khadija. Sun shaqu iya shak'uwa su ukunnan, tare suke duk
wata harka ta kasuwanci.
.
*********
Wata rana Ahmad ya dawo daga makaranta sai ya hango
kamar ana butsul-butsul a ruwa, har ya wuce sai kawai ya
dawo yana lek'awa sai yaga abin yayi yawa, koda ya matso
sai yaga mutum ne, baisan lokacin da ya fada cikiba ya
tsamota. Yarinya ce 'yar kimanin shekara 8, ya kwantar da
ita ya rik'a matsa mata cikinta a hankali tana fitar da
ruwanda tasha baki hanci, har ta fara tari, ta bude ido a
hankali, sai ta sake rufewa, Ahmad dai yaga abin ba nashi
bane sai ya d'auketa ya kaita gidansu, mamarshi na ganinta
ta fara salati, da yake ita tasan ta, "ina ka samo Suhaila ?? "
Yama Ammi bayani, " ai banga ta zama ba" ta dauko mayafi
ta yafa ta sungumi Suhailah sai gidan Alhaji Ibrahim ta
maida musu bayanin komai, Anata godiya, bayan kwana
biyu Suhaila ta ware waras, Mama ta kirata, "Ke wai garin
ya kika fad'a ruwa?" "Ba wannan ne ya turaniba!" Cikin
rashin fahimta Mama ta k'ara tambayarta, "wanene
wannan?" Suhaila kuwa ta tsaya kai da fata akan Ahmad ne
ya jefata ruwa, Mama cike da mamaki, take jimamin
lamarin, sai da Dady yazo ta mishi bayani abin da Suhailah
ta gaya mata, shikan bai yardaba sam, dan yasan halin
Ahmad tsab, dan haka bai d'auki maganar da mihimmanci
ba, mama ta yafa taje ta sami Hajiya Sa'adatu mahaifiyar
Ahmad ta bata labarin da Suhaila ta gaya mata, tace kawai
a jawa Ahmad kunne kada ya k'ara aikata irin haka, an
kuwa yi sa'a Ahmad yana gida, "kai Ahmady" na'am ya fito
d'akin su, cikin girmamawa ya gaida Mama, ta amsa a
sake, "dama Suhaila ce tace wai kai ka jefata ruwa ranar "
"waye Suhaila Ammi!?" Ya tambaya "yarinyar da ka kawo
shekaran jiya kace ta fad'a ruwa mana, har ka fito da ita"
shiru yayi chan kuma yace "akan me zan jefata ruwa
Ammi? Mi ta mini da zan jefata ruwa?" " mudai yanzu ba
wannan ne gaban mu ba, kawai ka fita harkar yarinyar nan
idan ba zaka taimaketa a matsayin k'anwarka ba, to kuwa
ka rabu da ita" Mama tace "kai tashi ka tafi abinka, kilama
shiririta ce irin ta Suhaila" cike da mamaki ya wuce d'akin
shi, lokacin Ahmad yanada shekara sha biyar, amma akwai
natsuwa gun shi, gashi komai nashi a tsare, iyayen sukaci
gaba da hirar su. Tun daga wannan rana Ahmad ya d'auki
tsanar duniya ya d'aurawa Suhaila, gashi ba wani saninta
yayiba dan ko ganinta yayi bazai ganeta ba, amma ko
sunan ta bayason ji wannan kenan....
.
***********
Da yake su uku suke kasuwancin su komai yana tafiya
yanda ya kamata duk da cewa Alhj Sulaiman shine
shugaba, dan kusan 50%(rabin dukiyar kaauwanci) dukiyar
shi ce, sauran rabin kuma na Alhaji Isma'el da Alhaji
Ibrahim ne. Alhaji Isma'el ya d'auki ki'yayyar duniya ya
d'aura musu ba tare da sun saniba, anan ne yayi nasarar
lik'awa Alhj Ibrahim satar kudin company kusan M.200,
kuma akayi bincike akaga kudin gurin Alhj Ibrahim, wanda
duk sharrin Alhj Isma'el ne, ba tare da wani dogon bincike
ba suka cireshi a shikinsu, suka dawo su biyu. Abin yama
Alhaji Ibrahim zafi ba kad'an ba, sharri harma na sata,
gashi da zuciya kamar me, bak'in cikin haka yasa yabar
Sokoto ya dawo Katsina da kasuwancin sa.
.
******************
BAYAN SHEKARA DAYA.
Alhaji Ibrahim yazo Sokoto ganin gida da iyalinsa anan ne
Suhaila ta sami accident ta fito daga gidan yayar ta
Rukayyah itada Suhail mota ta kad'e ta, shima Ahmad ya
fito gun wani cafe yaga mutane, yana zuwa yaga taro, ba
abinda akayi mata gata kwance, shida wani bawan Allah
suka samo taxi da police aka kaita asibiti, duk da ko lokacin
bai ganeta ba kuma bai kiyaye fuskar taba, wannan bawan
Allah ya gano iyayenta da taimakon suhail. Dady ya riga ya
koma Katsina, yace Rukayyah ta kula da ita dan ayyuka sun
masa yawa, an mata duk abinda ya dace.
.
Kullum Ahmad yana zuwa dubata, duk da baisan wacece
itaba, ranar ta tashi ta mik'e zaune yana zaune yana
karanta wasu takardu Anti Ruky na sak'a, dan mayyar sak'a
ce, tayita kallonsa, suna hada ido, sai ta masa murmushi,
tace " inasonka kaji " shima ya mata murmushi, yace " nima
inasonki" ta k'ara murmushi har haqoranta da take 6an6ara
suke bayyana "to zaka aureni idan na girma irin na Anti
Rukayyah da uncle?" Yace "Eh mana" yeeeee tace sannan
taci gaba, " to kaga Anti Rukayyah tana cema uncle Honey,
ni mi zaka cemini!?" "Aike kyakyawa ce so zan rik'a kiranki
da beautiful" ta zunburo baki "ni banason sunan, ko Dady
Some times (wani likaci yana cemin beauty, fadi wani mai
d'ad'i" ta ya mutsa fuska a yangace irin na yarinta, "kina
son Dear" a haf, ta d'auke kai gefe, tace "ai ko mama
tsohuwa dear take cema Dady" dariya yayi sosai har fararen
hak'oransa suka bayyana.....

No comments

Post a Comment