Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

== RAYUWAR NIHILA 5 ==

== RAYUWAR NIHILA 5 ==
.
An kai sauran amaren gidajensu Wanda suka sha jere kudi
ya barnatu kam ba laifi saidai fatan alkhairi.. Nihila kuwa
duk ta rame ta zama so silent kullun tana addua Allah ya
jikan mijinta yakai haske kabarin sa.. ranan baban ta yaga
duk ta zama wani iri saiya shirya musu fita picnic dan ta
Dan samu walwala sunyi inviting hardasu beejay da sausan
da mazajen su sukaje lake view Ana zaune Ana Dan ciye
ciye kawai sai baban nihila ya tashi daga ganin wani
mutumi shima mutumin daga ganin shi ta zo wurin da
fiskan mamaki yace jameel kana rayuwan nan ashe zamu
kara haduwa its been ages frnd yace hmm kaidai bari
Muhammad feels good to see old faces again yaranka
nawa yanzu yace gasunan family na ku gaisa ya masa
introducing duka yaransa sannan yace kaifa yace shima
tare da family dinsa yazo bari ya kirasu yaje ya taho dasu
tun daga nesa nihika keji gabanta na fadi wani abu ke yawo
a ranta aikuwaa suna matsowa wa zata gani inba hisham
ba hisham kuwa ji yayi kanshi na sarawa wani flashes yake
gani a idonshi nan ya fadi sumamme aiko nihila da gudu ta
tashi bata ma san tayi ba tana kuka tana girgiza hisham pls
dnt leave me hisham Dan Allah ka tashi I can't live without
u. iyaye dai abu ya kulle musu kai Dan haka kowa da
tambaya fal a ransa amma dai akayi asibiti Dan ceto ran
hisham koma meye ayi bayan nan!!!!
.
Nan dai suka garzaya sai asibiti doctors suka shige dashi
ciki sun fito suke cewa yayi regaining memory dinshi za'a
iya ganin shi inya tashi daga bacci suna shiga dakin ya fara
motsi bude idon da zaiyi ya fara da nihila ta matso kusa da
gadon akace gatanan nan dai iyayen sa suka yi hamdala..
ranan a gidansu nihila aka taru Dan jin bakin kowa nan ne
suke gaya ma iyayen nasu ai sune wanda suke fada musu
tun da can da suke cewa bazai yiwu ba su auri juna baban
nihila yace kaji jameelu Allah mai iko ba yanda baya abunsa
ashe Dan gida nema ni ban sani baban hisham yace ai Allah
ba ta yanda baya abunsa in dai ya rubuta zai faru magana
ta kare.
.
HISHAM ne tambayan daddyn yanda yasan baban nihila
yace mishi tare suka tashi neighbors ne tun suna yara kuma
abokai makaranta daya sukaje tafiyan shi university ya
dawo ya samu muhammad bayanan da en gidan su wai sun
kaura sun bar garin kuma ba wanda ya barwa sallahun inda
suka kaura yaji ba dadi Dan sun saba sosai tun yarinta tare
suke komai farat daya ya neme shi ya rasa sai gashi su
zasu hadasu suke neman hana alkhairi amma da ke Allah
yayi gashi sun hadu da juna. sai musan yanda za'ayi kan
maganan yarannan a turo manya ayi magana tunda dama
suna son junansu baban nihila ya basu labarin auren da tayi
hisham har yaji wani abu ya tokare shi ya zaci an Dan dana
amaryar sa nima na Dan dara aka ce masa ai ran auren
Allah ya dau ran abunsa ya ji sa'ida a ransa Saura sati
daurin auren nihila da hisham sai shirye shirye suke kowa
ransa kal amma nihila ta dau alwashin saita yi maganin
gogan ladan karyan da ya mata yazo gida Dan tambayanta
abunda take bukata taci kwalliyan ta cikin wani lace
turquoise blue mai ratsin pink Ga daurin nan an kafa shi
tasa powder kawai da lip gloss ta fito da Dan gelenta kan ta
iso ma turaren ta yayi sallama ta zauna kujera kusa da shi
gogan naku fa bakin sa yaki rufuwa sai kallo yake ya saki
baki tace da dai ka kulle bakin naga kuda zai fada ya
kwashe da daria yace kaii madam bakida dama aike din kin
tafi mun da hankali tace ahh kai Dan Allah dai yace wallahi
kuwa wai mene ake ta Shan kunu tace hakan nake muradi
yace umm ran gimbiya shi dade ai yanda kikeso haka za'ayi
ta Dan murmusa ta juya ido nan dai suka tattauna kan
abubuwan da zasuyi da kuma abunda zata bukata ya bata
kudi ya tafi.
.
Ranar jumm'a daurin aure nima nace zan gayyaci su
halyma qawata da erta amna er disin sidin bayan ludayi A
yau ne aka daura auren NIHILA Muhammad da HISHAM
jameel bil adama sun taru a wurin kam ba'a magana anyi
reception na gani na fada da dare kuwa dinner aka tafi
tasha kyau sosai ma mutane an hallara a wurin dinner
nagano su marwanatu su phary su maryamah sai hange
suke ko zasu Ga ango da amaryanace inaaa bazan bari a
gansu ba tukunna kowa yana zaune ango ya doso hall rike
da hannun amaryarsa sun balain yin kyau sun kuma dace
da juna hisham baki har kunne sai daukan su picx ake tayi
har suka zauna anyi barnan kudi an ci ansha an hantse
nima dai nace rana daya na mai gayya ne shiyasa na dan
taka rawa aka gama dinner aka watse hisham ne ya Maida
amaryarsa gida suna mota yayi parking yace mata u look
so beautiful my beloved wife kanta na kasa tana wasa da
yatsunta wani sabon kunyan shi takeji ya kama hannayenta
ya rike tayi ta sake amma ta kasa nan ta fara masa
shagwaba yayi hakuri ya barta ta shige ciki yace shi ina
ruwansa shida matar sa ina ruwan wani da kyar dai ya
yarda ya barta ta fita ta shige washe gari aka kai amarya
gombawa diban fari ba'a kwan damu ba an tashi damu
mudin kenan amarya tasha kukan rabuwa da dangin ta
washe gari kowa ya koma inda ya fito daga amarya sai
ango .

No comments

Post a Comment