Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

== RAYUWAR NIHILA 4 ==

== RAYUWAR NIHILA 4 ==
.
Momin hisham ta samu baban shi da batun maganar
hisham yace karma ta fara yasa ta kira hisham yace masa
yama cire rai matan gombe duk sun kare ne da har zaije
abuja neman wata bai yarda ba hisham ya tashi jiki ba laka
ya tafi Dakin sa ya rasa me zaiyi yaji dadi ga nihila is
against him kawai ya tattara kayanshi na sati da duk
abunda zai bukata ya fita iyayen shi basu saniba ya shige
motan sa bai zame ko ina ba sai hanyan Abuja gudu yake
baima ganin gaban shi shi kanshi baisan ina yake dosa ba
kawai saiga wata daf ta doso shi ba birki yana ta mishi
horn amma ina hisham hankalin sa baya jikinsa ji kake
kyarrrrrrrrrr mutane suka yo agaji dan ganin motan basu
zaci mutum zai fito da raiba dama suna kusa da abj kawai
akayi dashi cikin gari.
.
Nihila kuwa tana can abun duniya ya dameta dan kuwa
baban ta ya kawo wani maganan da ta kasa zama a kanta
tsaban girman sa wai zasu kara karfin zumunci da babban
abokin shi Dan haka sun hada yayansu aure shi kuwa nihila
yace ya bada ganin duka sauran sunada samarin su inyaso
sai a hadasu duka at a time.Taci kuka sosai harta gode ma
Allah taso tayi ma babanta maganan tanada wanda take so
amma momin su ya kwabeta karta kuskura taga ma it's of
no use gwara ta hakura ta manta da hisham tayi biyayya
Ga iyayenta.... tana zaune aka zo akace ana neman nihila a
waje tace waye aka ce mata wani da kaman bazata je ba
sai kuma tace bari ta fita ta gani to her suprise wa zata gani
inba jawad mutumin da sukayi kusan shekara basu hadu ba
tun graduation dinsu tayi mamaki kwarai batasan sanda ta
fara daria ba tace jawad kana duniyan nan yace inanan
nuhila ya bayan rabuwa tace lafiya how's your life..
.
Alhamdulillah na dawo skul nace dole inzo in ganki sabida
it's been long tace kaidai jawad bari ta bashi labarin duk
yanda take ciki yace mata nihila kinyi hakuri kiyi biyayya Ga
iyayen ki insha Allah shine alkhairi a rayuwanki tace
shikenan yace shi zai tafi zaizo dubata in ya kara hutawa
sukayi salaam. Hisham kuwa yana can asibiti likitoci suna
kanshi daga karshe dai suka gano yayi loosing memory
dinshi temporarily kuma Ga karaya biyu a kafa.. suka rasa
yanda za'ayi a samu wani nashi sai kawai suka bada
sanarwa a tv da hoton shi da sunan da suka gani jikin wallet
dinshi anata cigiya ko Allah zaisa a gano yan uwanshi...
iyayen hisham kuwa neman duniyan nan sun yi basu ganshi
ba hankali ya tashi sosai ma matuka maman shi har kuka
ta fara ana haka ne aka kirata wata kawarta ta dauka jiki ba
dadi tace ta kunna tv ta na kunnawa saiga sanarwa ana
neman yan uwan wannan bawan Allah mai suna hisham
wanda ya gamu da hatsarin mota kuma yayi loosing
memory dan haka idan yan uwanshi suna kallo su gaggauta
zuwa abuja nan suka ba da address din asibitin ko zaiyi
recognising dinsu ai sai faduwa tayi a wurin baban hankalin
shi ya matukar tashi ta farfado tace Allah fir akama hanya a
tafi a nemo mata danta haka sukayi booking flight washe
gari sukaje Abj basu tsaya no ina ba sai asibitin suka ce
sune iyayenshi aka kaisu har dakin aiko dai hisham bai
ganesu ba yace musu kudin wayene sai maman shi kawai
ta fashe da kuka haka dai likita yayi ta rarrashin ta yace
tayi hakuri irin wannan matsalolin sai a hankali inba mutum
yaga abunda yake tunani last ba ko kuma something very
important in his life nanne in anci sa'a saiya samu
memories dinshi back other wise sai wani ikon Allah.
.
hakadai iyayensa sukayi ta jinya a asibiti har ya farajin
saukin karayan da yayi yana healing amma memory kam
babu... ummm wannan kenan ko yaya amarya NIHILA tayi?
Ga rashin masoyi Ga auran wanda bataso...muje zuwa
Ananan anata shirye shiryen auren su anata gyara amaren..
nihila kuwa ko taba ganin angon nata batayi ba Dan ance
mata baya kasan sai ranan daurin aure zai dawo sunan shi
junaid akazo ranan daurin aure an daura na sausan da
yusuf.. bahijja da anwar sai nihila da junaid.. an daura aure
ana reception ne aka zoma iyayen biki da wani mummunan
sako akan ango nihila sun samu hatsari akan hanyan zuwa
daurin aure inda motansu ta kone kurmus sukayi mutuwan
shahada kowa yaji ba dadi haka aka kwashi jiki akaje aka
kaisu gidan gaskia.. nihila nacan tana shargar kukan ta
batasan meke faruwa ba tana ta inama ace yau da hisham
aka daura mata aure saidai kashh bakin alkalami ya riga ya
bushe.Baban tane ya daure yazo ya sameta yayi ta mata
nasiha mai shiga ciki yace komai yiwuwan ubangiji ne kuma
Allah ba yanda baya abunsa shike bayarwa shike kuma
hanawa a lokacin daya so jikin ta yayi sanyi tasan wani abu
ne ya faru tace daddy ka gayamun ko menene nayi alkawari
zan iya yace mata nihila Allah ya miki albarka biyayyan da
kika mana Allah ya dau ran wanda muka baki sai taji
hawaye a idonta tace Allahu akbar Allahu akbar Allahu
akbar Alhamdulillah ala kulli na dau wannan qaddara hannu
bibbiyu Allah ya musanya mun da mafificin sa uban ya
rungumeta yana kuka tanayi nima na Dan tayasu Dan
tausayi.

No comments

Post a Comment