Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

==RAYUWAR NIHILA 3==

==RAYUWAR NIHILA 3== .
Daddy shi ya dawo da maghrib yaje ya sameshi har parlour
uban ya rungumi dansa sukayi musabaha ya gaisheshi
sunata labari saiga mum dinsa tazo tace ooh yanzu alhaji
da yaron nan ne ka zauna sai hira kake kaman wani sa'an
ka yace haba ke kuwa altine in banyi dashi ba dawa zanyi
shi kadai fa nakeda ai dole in soshi.
.
WANE NE HISHAM? Dane daya tilo ga alhaji jameel pindiga
tunda sukayi auren zumunci da altine yar wajen ummansa
ce shekaran su 5 Allah be basu rabo ba ana shida ta samu
ciki ta haifa da namiji aka sa mishi hisham daganan kuma
shiru ba aihuwa ba labarinshi. son dau son duniya Sun
daura mishi primary kawai yayi a nigeria Amma secondary
da university duk a cyprus yayi. Hisham fari ne ba kuma
fari har can ba yanada kiran maza wanda suka amsa sunan
su dan daga nesa zaka hango abs din da Allah ya masa Ga
faffadan jirgi da tsayi he's just the perfect guy da mata ke
so saidai duka wannan kyan Dan maciji ne dan kuwa
zuwansa Cyprus ya lalace da neman mata da zuwa clubs
sa'a daya dai baya shaye Shaye.Hankalin sa tashi yayi da
yaji fadan da daddyn yake tayi akan wani cousin dinshi yaje
neman aure har sokoto yace shi bazai lamunta in bazai
nema auren a gombe ba ko wani wuri kusa bazaije masa ba
sabida nisa da kuma rashin sanin tushe.wani gumi yaji ya
tsatssafo masa ya ji jikin shi ya mutu ya tuno da nihilan sa
Wanda bazai iya rayuwa babu ita ba gashi yanaso yaje ya
ganta Amma babu hali Dan kuwa daddyn shi ya sashi a
gaba da ayyukan company dinsa atm dinsa gaba daya
suna hanun hisham minti daya biyu zai neme shi yace it's
high time ya zama responsible man. nihila kuwa tana can ta
rasa meke mata dadi idan taga pictures din hisham da
emmata a wayanta saitaji duk ya fara bata haushi tace yau
kam ko mutuwa za'ayi sai sunyi ta ta kare.
.
Ta shiga watsapp dinta saita tura picx din Wa hisham yana
zaune yana tunanin yanda zaiyi da daddyn shi batun nihila
kawai yaga watsapp dinshi ta turo picx baisan sanda ya
tashi tsaye yana zaro ido ba hankalin sa ya balain tashi
tambaya kala kala a ransa ina nihila ta samu pics dinnan
kardai tasan halayen shi wanda yaketa boye mata? Ta ina
zai fara mata bayani gaba daya ya Burkice aiko ana haka
sai ga text dinta hisham ka bani mamaki u disappointed me
I trusted u my whole life Amma da abunda zaka sakamun
kenan? Forget u ever know me in your life. Gud bye. Tashin
hankaliiii!! Ba'a sa maka rana shin kuna ganin hisham zai
hakura kuwa muje zuwa.
.
Hankalin sa a tashe ya kira ta a waya taki dauka missed call
kusan goma sannan ta dauka ana sha dayan tana dauka ya
fara magiya nihila plsss let me explain to you tace ba
abunda zaka gayamun hisham na riga na gani da idona ko
zakace ba kai bane yace nine nihila Amma Dan Allah kiyi
hakuri na miki explaining tace bana bukatan wani
explanation kaban mamaki hisham ashe dama abunda
kakeyi kenan Allah daya halicce ka bakaji tsoron saba mishi
ba baka kuma ji kunyan yana kallon ka saini mutum wanda
ba komai ba baiwar sa ya halicce ni nine zakajin kunyan
idona kar na sani. yace nihila nasan nayi abubuwa da dama
a rayuwa na but wallahi shigowanki rayuwana is a blessing
to me kinsa na daina 70% din abunda nake I have changed
much more than before for u tace ooh sabida nine ma kayi
changing not because kana tsoron abunda zakaje ka tarar
wurin ubangijin ka yayi shuru yana jinta kawai sai hawaye
yaji a idonshi nihila pls dnt leave me without u my life will
be miserable plss nihila tace hisham its too late to cry when
the head has been cut off just leave me alone i adore and
cherish every moment we had together but this has to end
ta fashe da kuka tace goodbye hisham ta kashe wayanta
ma gaba daya tasa favourite waqanta wanda take sawa in
tana bakin ciki wato bhula dena (forget me) na ashiqui ta
kuka har taji ba dadi.Taci kukanta son ranta saiga bahijja ta
tsaya tana tausaya mata duk tasan be wuce kan hisham ba
ta girgiza kai sis meya sameki kawai ta qara fashewa da
kuka ta rungumi beejay he betrayed my trust and life beejay
he lied to me ya zanyi da raina gashi mummy tace na fita
harkanshi bata yarda da soyayyan mu ba i just dont know
what to do beejay ta rarrasheta tace mata tayi hakuri ta
manta da hisham sabida koda ya canja halin sa iyayen su
da kyar ne su yarda sabida nisan garuruwan da suke kuma
basa son auren nesa. idonta duk sun kumbura sunyi ja ta
dawo kaman ba lively nihilan da take da ba ta canja
completely.
.
Hisham kuwa yana kuka ya je ya samu mum dinshi tace
hisham lafiya me haka kake kuka kaman yaro wa nine ya
mutu yace momi aa ba mutuwa bane wata yarinya ce ya
bata labarin nihila amma bai gaya mata dalilin fadan ba
kasancewar suma iyayen basusan tsiyar da yake tafkawa
ba Dan inya dawo nutsuwa yake tace hisham da ka hakura
da yarinyar kasan daddyn ka ba yarda zaiyi ba da kunnen
ka kaji yana fada akan neman auren da cousin dinka yaje
yi a sokoto bazai bari ba yace mommy wlh bazan iyaba kiyi
hakuri ki mishi magana she's my life tace shikenan zan
gwada amma abunda kamar wuya.

No comments

Post a Comment