Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

== RAYUWAR NIHILA 2 ==


== RAYUWAR NIHILA 2 ==
.
Na tsaya kawai ina sake da baki nace beejay yanzu kin
kyauta ma kanki kenan kiji tsoron Allah fa inni na rufa miki
wani ya ganki yaje ya fada fa a gida tace kin fara ko naji
shikenan a haka dai ta gama rawe rawen ta suka koma gida
nihila na jimamun alamari irin na bahijja.Sun koma gida
beejay ta Kara tunatar da ita batun alkwarin rufe sirri tace
da ita tayi shuru tace toh.. wannan kenan! Suna waya ne da
hisham yake kara tunatar da ita irin sonta da yake nihila kin
sauya mun rayuwa kin canja ni gaba daya wasu abubuwan
da nake da yanzu kusan duk na bari tace wasu irin
abubuwa yace hmm bazaki gane ba sai a hankali nidai pls
keep my love I promise I will be the best u ever had n I will
make u my wife! Ummm hisham kenan...
.
Yana can yana tsula tsiyar shi son ranshi a kasar cyprus
wanda shi a ganin shi wayewa ne ya kawo hakan Ga neman
mata ga zuwa clubs kowace rana saiya yi attending ba'a
barin shi a baya shima wai bazai bawa shedan kunya ba...
nihila tace yau kam bari ta shiga account din hisham na
insta tayi bincike tana shiga taga pictures kusan 30 ta shiga
ta fara duba comments duk wani abokin shi da taga yayi
comment shima sai ta shiga account dinsa ta duba hmmm
me zata gani saiga pictures din hisham baja Baja da
emmata a clubs ya kamo wannan ya kamo wancan ta ji
kaman an caka mata wani abu a zuciyanta..
.
Nima daganan saida naji rasssss.. batasan sanda hawaye
ya zubo mata a idonta ba tayi munching picx din duk ta
ajiye.. comments din mata kam kala kala kan pics dinshi
daga wnda yake cema sweetheart sai me my wife da dai
sauransu ta ajiye wayanta ta rasa meke mata dadi tasaka
waqar bhula dena(forget me) na ashiqui ta risgi kuka son
ranta saida idonta sukayi luhu luhu har bacci ya dauketa
anan sausan tazo ta sameta ta dau wayanta ta bude kawai
saitaga picx aiko ta tura taje ta nuna ma momin su waiga
samarin da nihila take so en iska marasa tarbiyya... Ran
momin su da yayi dubu saida ya baci ta sameta a daki ta
mata tas tace tunda taki jin maganan ta bazata bada wayan
ba sai taga canji a tattare da ita..
.
Tayi kuka sosai da taje skul take gaya ma habibaty tayi ta
bata hakuri sannan tace mata itama ta hakura da hisham
din mana tace mata inaa bazata iya ba tasan hisham yana
sonta ita kuma ta dau alkawarin she will change him for
good koda bazata aure shi ba amma bazata barshi a
munanan halayen da yake ba na sabon Ubangiji habibaty
tace shikenan Allah ya baki sa'a... watan ta kusan daya ba
waya har sun gama exams dinsu sannan da kyar da rokon
beejay momi ta bata wayanta hisham kuwa hankalin shi
dayayi dubu saida ya tashi da bai saba jin wayanta a kashe
ba kullun suna waya ko chatting sai yayi tunanin kodai taji
labarin halayen sa shiyasa ta guje shi tanata jimamin abun
a zuciyar shi.. kawai saiga call dinta ya shigo ya dauka
yace haba sweet ina kika shiga for weeks inata nemanki
saita mishi karya tace ai wayanta ne ya fadi saida ta siya
sabo yace kaii har kinsa naji sanyi a raina plss kina sanar
dani irin haka tace to shikenan insha Allah bazata kara ba..
.
Yace yauwa my nihila dats y i love u more n more each day
tace I love you most.. A zuciyanta tana mamaki halin
hisham kaman bashi ta gani da emmata ba abun ma har ta
kasa yarda duk da ta gani da idonta... tace a ranta akwai
ranan tonan asirinka!.Sun gama exams dinsu lafiya aka
fara shirye shiryen candy dinsu murna a wurinsu ba'a
magana dan a kansu ne za'a fara graduation ceremony...
ranan candy sunsha kyau ita da bestyn ta habibaty sunyi
shigen white and black Ga gown dinsu royal blue da white
ya karbesu sosai aka fara gabatarwa inda aka kira Nihila
Muhammad Tahir tazo ta bada opening speech ta fito da
takunta na kasaita kaman gimbiya taje ta bada kaman wata
baturiya nan aka dau tafi raf raf raf sai shewa ake an bada
prizes da dama wanda kusan rabi ita ta dauka tayi kukan
farin ciki bayan taro sun dau pictures sosai da jawad ganin
karshen zaman su yazo yanzu sun bude wani chapter a life
dinsu sunyi kukan rabuwa da jona sabida shi zai tafi
university of

No comments

Post a Comment