Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

LABARAN QASA

Babu sabani tsakanin Buhari da Osinbajo -
Gwamnati

Fadar shugaban Najeriya ta ce babu wani sabani tsakanin
Shugaba Muhammadu Buhari da mukaddashinsa, Farfesa
Yemi Osinbajo.
Matakan da Osinbajo ya dauka na gaggawa wurin tunkarar
matsalolin da kasar ke fuskanta tun bayan tafiyar Shugaba
Buhari hutu, sun bai wa masu sharhi mamaki.
Kuma hakan ya sa wasu na ganin ya yi wa mai gidan nasa
zarra a wata dayan da ya shafe yana lura da al'amuran
kasar.
Sai dai fadar gwamnatin kasar ta ce duk wani yunkuri na
nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari "kokari ne na kawo rudani".
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan
harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya ce 'yan adawa
ne kawai suke son kawo rudu ta hanyar kimsa wa mutanen
tunanin akwai rabuwar kai tsakanin shugaban da
mataimakinsa.
Sanata Ojudu ya ce "Kusan a kullum sai [Osinbajo] ya
tuntubi Shugaba BUhari saboda akwai abubuwan da ke
bukatar hakan. Ina nufin yana neman shawararsa wajen
zartar da manyan hukunce-hukunce."
Ya kuma kara da cewa irin ayyukan da Farfesa Osinbajo
yake yi yana yi ne domin ya burge Shugaba Buhari ya kuma
nuna masa cewa zai iya gudanar da al'amuran mulki ko da
shugaban ba ya nan.
Tun dai ranar 19 ga watan Janairu Mista Osinbajo yake
shugabancin Najeriya a matsayin mukaddashi sakamakon
bulaguron da Shugaba Buhari ya yi zuwa Ingila domin ya
huta sannan likitoci su duba lafiyarsa.
Daga lokacin kawo yanzu dai, mukaddashin shugaban ya
zartar da wasu ayyuka da ake ganin sun kawo sauyi a
kasar musamman ta fannin tattalin arziki.
A makon da ya gabata ne ya umarci babban bankin kasar,
CBN da ya zuba miliyoyin daloli a kasuwar hada-hadar
kudade, al'amarin kuma da ya sanya darajar Naira ta dan
farfado.
A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya hana yin hakan
da manufar karfafa darajar kudin kasar.
Har wa yau shugaban ya yi hakan ne domin dakile shigo da
kayayyaki daga kasashen waje wadanda ake ganin za a iya
yinsu a cikin kasar.

No comments

Post a Comment