Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

LABARAI DA DUMI-DUMI

Rikicin jagorancin jam'iyar PDP bai kare ba

Dangantaka na kara yin tsami tsakanin bangarori biyu da ke
jayayya a kan shugabancin babbar jam`iyyar adawa a
Najeriya, wato PDP.
Bangaren Senata Makarfi ya yi tir da matakin da Senata Ali
Madu Sherif ya dauka na bude hedikwatar jam`iyyar, bayan
wani hukuncin da kotun daukaka kara a kasar ta yanke, har
ma ya zargi jam`iyyar APC da rura wutar rikicin PDPn.
Jam'iyar APC ta musanta cewa ta na da hannu a cikin
rikicin cikin gidan jam'iyar adawar.
Haka ma bangaren Ali Madu Sherif, shi ma ya musanta
zargin banagaren na Makarfi.
Yanzu dai sai kutun koli kawai ce za ta iya yanke hukunci na
karshe kan wannan danbalwar.
To amma kuma 'yan Najeriya da dama na tambayar kansu
ko yaushe ne wannan rikici na jam'iyar adawar zai kawo
karshe?

No comments

Post a Comment