Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

HAUSA NOBLE'S

2.GANGAR JIKINSA NA AURA P2 NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT) Malam
Habu da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo
har ta hau titi ta kure sannan hankalinsu
yadawo kan kayansu. Malam Habu ya kalli
*yarsa Hanne wacce hawaye ya gauraye
idanuwanta dakumatunta, abin ya bashi
mamaki ganin Hanne nakuka alhali kuma ita
take son karatu take murna dazasu taho, ya
sake juyowa sosai ya kalleta yagahawaye ne
ke zubowa daga idanuwanta dayanabin
daya, ya ce "*Yar Baba, kukan me kike yi?
Karki cemin yanzu bakya son makaranta
bayan keaka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kinaso. Ba'a son raina ba
nima na kawo ki makarantarnan ke kika
amsa musu. Shine kuma yanzu kikekuka?
Idan kinsan bakya so to ni a wajena tafinono
fari sai mu juya kafin mu shiga ciki. Kansila da
mai gari su suka tilastamin in kawo ki amma
badanhaka ba nima bazan rabu dake ba na
kawo ki nanuwa duniya, babu wanda kika
sani. Hanne tagirgiza kai cikin shesshekar
kuka ta ce "Baba bamakarantar bace bana so,
rashin kunyar da masumotar can suke yi
maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji
hawaye ya cika masa ido amma sai yajure
yayi murmushin karfin hali ya ce "Allah
Sarki*yar Baba, babu komai duniya ce. Duk
wanda yagagirman tsohon wani, za'a ga
girman nasa. Hakakuma duk wanda ya raina
tsohon wani sai an rainanasa, zamani ne ya
canja babu sanin girman Allah, ko an hada
mutum da Allah kamar an hadashi dasa'ansa,
wani cewa zaiyi daina hadani da Allahkarka
cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da
cewa"goge hawayenki 'yar Baba kizo in dora
mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi min
kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da
taci damara dashi ta goge idanuwanta kana
ta matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora
mata a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a
daya hannun sa'annansuka juya suka doshi
cikin babbar kofar shigamakarantar, yaci
gaba da yi mata nasihohi masuratsa jiki yana
nuna mata wannan abin da aka yi masa a
gabanta ya zama darasi a wajenta
duklalacewar tsoho koma ba tsoho bane na
gaba da itakada tayi masa fitsara. Ta zamana
ko a ina takekuma kome ta zama ta girmama
na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa
mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma
dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi
uku suka iske a bakin kofarshiga cikin
makarantar, suna zazzaune, MalamHabu yayi
musu sallama gami da mimmika musuhannu,
Hanne ma ta duka ta gaishesu, bayan sun
amsa, Malam Habu ya ce "Yarinya na
kawomakarantar nan, ta ina zanbi mu shiga
ciki? Dayadaga cikinsu ya ce "Mikewa zakuyi
sosai zaku tararda ofishin Malamai dana
shugaban makarantar.Malam Habu yayi
godiya suka wuce, har sun danyonisa suka ji
masu gadin nan sun kwalla musu kira bayan
sun dawo, sai daya daga cikinsu ya
kallesusama da kasa ya ce "Dan Allah Malam
muna datambaya sai bayan da ku ka wuce
tambayar ta fadomana. Malam Habu ya gyara
kayan dake hannunsagami da yin murmushi
ya ce "To Allah Yasa na sani.

No comments

Post a Comment