Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

*** *BARIKI IYAWA PART 9* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 9* ***
.
Ta kallo fadeela da har ta fara hawaye,, tai murmushi,,sai
da ta dai daici Alhaji zai shigo ta zauna tare da rukunkumo
fadeela,, ta daga murya "Taji ita yar talakwa ce,masu
kwadayin abun Duniya,,Munji mu ya'yan masu da maula
ne,,munji Uban mu baida halin siyan kujera dole ki zage
mu,..da sauri Alhajin ya shigo,," Subhanallah, Sa'a mey ya
faru,,tuni ta tashi,,"yauwa,gwara da kazo,,Yau in kaga na
bar gidan nan toh anyi ta ta kare wlh,,Yace"Sa'a meya faru
ne,,fadeela, me ya faru kike kuka?Sa'a ta kallo Matar
tashi,kan ta nuno ta da hannu, "Matar kace,,samun ta nai a
kanta tana ta Nada,,dake ita kuma doluwa ce ta tsaya ana
dukan ta kamar jaka,, daga rabiya ta dawo kaina,,Wai mu
ya'yan matsiyata,sai fadeela ta bar mata gida,,Dana
tambayi fadeelan sai cewa tayi daga fitowa zata shiga
kitchen ta tare hanya,,Wai ai ba chokalin ta a ciki,,.daga
sake hanya ta hau ta da duka.. Gata nan ta Musa,,tuni ya
hau 90,,yayo kanta zai mare ta ta kauce"Dama na fuskanci
Rabi kullum yarinyar nan rama take,,kwata kwata taki
sakewa da gidan nan,, ina tambaye ta baiwar Allah tace ba
komai,, Ashe gori kike mata harda hadawa da duka?a gida
na? ta kada kai zatai magana tuni ya kara tunxuro,, " karya
na miki kenan??ta girgiza kai,,ya cigaba"kuma da kike kiran
ba chokalin uban ta,ke da na naki uban,, tuni ta kallo Sa'a,
Sa'an ta kanne mata ido daya,,kan ta kallo Alhaji, "ai zance
ya kare,, yau kam zan fadi komai in naje gida,da sauri ya yo
gun Sa'an jiki na bari" aa Qanwata,.kar muyi haka dake,,kar
su dauke ni wanda ban isa da gida na ba,,zan dau mataki
ai,,dole kowa tai hurumin ta,,wlh babu takura a
gidana,,saboda haka Rabi ki kiyaye wlh,,so da kauna yasa
na auro fadeela,,dole tai son ranta a gidan nan da itama
nata ne..ta kallo shi "Toh Alhaji ba komai,,ta kallo Rabin,, "
Aunty ni zan tafi,,Allah kiyaye gaba,ta kallo fadeela da
Alhaji,, "na wuce,dama zan wuce ne na shigo mu gaisa,, ya
wage baki" Atoh toh kin kyauta,,ya zaro kudi a aljihun
shi,,"gashi Haj Sa'a asha mai,,ta kada kai "Alhaji harda
wahala?
.
Ta dan Durkusa" toh na gode,,Yace"mu rakata man fadeela
koh?ta kada kai ya matso ba ko kunya yana goge mata ido,,
Sa'a tai wani murmushin, kai da gani kasan na mugunta
ne,ta kallo Haj Rabi,,tare da daga mata gira,,ta zuge jaka ta
dakko wani katon glass su Alhaji sukai waje,tana kokarin
sawa tace"Yato kika ga??ta dau jakar ta tai hanyar waje"ki
gode Allah da yau banyi wanda zaki yi gida ba,,. Ta daga
mata yatsu 2, "sai gani na 2,wlh ki gyara koh na gyara
ki,..tai waje..Wai Saida ta fita tai yunkurin sha kota,sai sai
kan ta kai kofa har ta fice,ba abin ta bita ba Alhaji na
waje,..Sai yanxu taji hawaye na zubo mata,, lalle Alhaji,
wato sirrin ta karafkaf ya kwasa ya kaiwa dangin amaryar
sa..? Bayan Sunyi sallama da Alhaji ta kallo ta,zan kira
ki,yanxu kibi mijin ki,,saura ki tsaya wannan Dolan cin
naki.. Ta bude kofa ta fita,,fadeela ta bita da murmushi, dan
uwa mai dadi,,Allah yaga tana son mijin ta,duk da badan
Allah bai bashi haihuwa ba da yana da kusan kamar ta.. Ta
kada kai, Ashe hakane abun,.kuka ta samu Haj Rabi nayi
reras,dan Alhaji yace in fadeela ta shigo ta bata hakurin
dukan da ta mata..Wai Alhaji yai mata wulakanci DAN bata
haihu ba..
.
Yace" ke kika ce haka bani ba,abu 1 ne bazan dauka ba,,tuni
fadeela tai ciki,.chan Shima yabi bayan ta ya barta parlour
tana ta rasgar kuka,,gashi ba wanda take sakar wa a dangin
mijin hatta Hajiyan shi ba dadin ta take ji ba bare ta kai
kara. 5:08 tana gidan Ummi,, da gudu ummin ta rukunkume
ta har suna shirin faduwa,, kan ta dago tare da ture ta
kujera,,"Dallah na manta ma munyi fada,, wlh baki m Sa'a,,
ta marai rai ce "yi hakuri, tace" na zata ko lefin ya shafe mu
ne na ran dinner? Tai murmushi, "bar tuna min,ya wuce
ai,.da mamaki ta kallo ta,, ta tashi,meye yake kamshi
haka?kai shegiyar qawa,,ke ai bana shakkun ki,,ba kamar
waccan ba,,tai daki," Wai ina angon ne?ta biyo ta, "yanxu
zaki gansu,.tace" inye, qawata komai yaji,Allah sanya
alkairi, sannan a dage, yanxu BARIKI zatai aiki..
.
suka tafa..sun koma parlour taji wayan ta na kuka,, ta
dauka,fadeela ce,."ya akai auntyn tsoro? Tai murmushi, kai
wlh Sa'a baki da kyau,tai murmushi kan tace"kwarai
kuwa,ko nai wanka ba..tace"ke kinga yadda yazo yana
lallaba ta,harda Durkusawa fa a kasa, Wai shiga in kara
baki hakuri kar ki fada a gida,,tai kwafa"ai kinga illar
nunawa kishiya tsoron ta,, fir ke kenan kullum akaje gidan
ki kina daki,,bazaki ware ki kama mijin ki ba,, bari kiji,idan
har zakina tuna wa da wata a gida bazaki Iya komai ba a
gidan Miji,,tukun ina kayan nan Dana kawo miki? tace"suna
nan,"da fatan kina amfani da su?ta kada kai, gaskiya ban
fara ba..ta kada kai "Toh in kin fara mayi maganar,,.dai dai
nan taji hayaniyar su Aminu,,lokacin tana fadin "nidai ina
fada miki kishiya ba abar tsoro bace,atoh u better wake up
n shine ur eyes,,.ta tsaya da magana ganin da wanda
Aminu ya shigo,.tace" bari inna je gida zan kira ki,da kallo
itama ta bishi,,yayi kyau cikin kana nan kaya,,sai murmushi
yake sakar wa,,fuskar ta ba yabo ba fallasa,,Aminu yace
"Kaga Alalar Geto,, wato BARIKI.. IYAWA,, tuni fara'ar fuskar
Hafeez ta kau.. Maimakon ta kalli Aminun sai ta ke kallon
Hafeez din.
,
Ta maida kallon ta kan Aminu,"Ango kasha kamshi,,ya Dan
bata rai,"au,ai munyi fushi ma Ashe,tai murmushi ta dan
sachi kallon Hafeez din,, duk yai kicin kicin,,tace "ai hakuri
dai,gani nazo,,ya kalli Hafeez, ya sake kallon Sa'a,, yai
murmushi, halin su sai su..tashi yai yabi Matar shi daki..
.
Ya bar kallon wayar ya kallo ta,.duk ranshi ba dadi, suka
hada ido yai mata kirrr,,tana ganin haka itama ta cinkune
fuska,.sun dan jima ba wanda Yace da wani uffan,, chan
dai ya nisa,," Amma kin San BARIKI ba sunan azziki bane
ba koh Sa'a?? Ta kallo shi da mamaki,,baki sake.,yaci
gaba,,"Gaskiya Lamarin duk bai dace da ke ba..ta dallah
mishi harara,.kaga karfin hali,Wai Barawo da
sallama,."Toh,Abba na,,"meye ruwan ka da Lamari na toh??
ganin ta fara daukar zafi yasa ya sakko.. "No,
Sa'adatu,,BARIKIN ne ban son ana fada miki,ina tsananin jin
zafi,..da sauri ta daga mishi hannu.,"Zafi?sai ta zata ko
wani fadan yake nema..cikin fada tace"Ni dauka ta My
professional life was my personal life,,ta hade girar sama
da kasa..da lumana ta karasa fadin" stay out of it..ok?.ta
fara kun kuni a hankali"kaji min mutum da karfin hali..ta
daura kafa 1 kan 1,,yai murmushi,,"Allah ya huci zuciyar ki
yan mata,," my mistake.. Tun daga lokacin bai sake ce
mata komai ba ya dukufa a wayan shi,,ta dan kallo shi, jin
yai shiru,,kanshi kasa,ta dan harare shi,.kan ta
cigaba..lokaci lokaci tana dan Harar shi,kamar wanda laifin
shi ke karuwa..Text taji ya shigo,,tai kamar karta bude tana
chat..
.
Ta dai sauka,.abinda ta gani yasa ta kalle shi,,wai "Meye
kike harara ta??ta murguda baki..taki reply..Chan wani text
din ya shigo, " mey kuma nai na murguda baki??..ta kallo
shi da niyar tace "anyi din,sai kawai taga Shima ya murguda
mata baki,,bata san lokacin da murmushi ya subuce mata
ba,,harda dan dariya mai sauti..ya kallo ta yana
murmushi,.haka suke kallon juna da murmushi, har ta
manta da komai,,tunda take,bata taba kallon Hafeez ba irin
na yau,, Hadadden saurayi ne mai barazanar zama
tunxuru,fari ne,ba chan ba,yana da saje, mai taken Razana
mata,, kyawun shi na Fulani biyu,yana da kwarjini a
fuska,,da dan gashi wajen gemun shi zuwa sage,anyi aski
sai yai mishi dan dass.. Murmushin shi yafi komai tafiya da
hankalin mata,dan baiyanar kyawawan farin hakwaran shi
Tass dasu,,dogo ne,Amma ba chan ba,sannan yana da
kaurin jiki,a dire yake,. Uhmmmm"Aminu ne yai murmushi,,
da sauri ta saukar da kanta kasa cike da jin haushin
kanta.,Hafeez ya harari Aminu,, shikwa murmushi yai tare
da kada kai,. Da halamun hasashen shi ya kusa zama
gaskiya.

No comments

Post a Comment