Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

*** *BARIKI IYAWA PART 12* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 12* ***
.
Baban ya shiga dashi ciki,yai wa mama magana,,ta fito da
kamalar ta,Ya dan duka ya gaida ta, itama da fara'ar ta ta
amsa,,kan tai dakin Sa'an da ta koma bacci,,. Ido waje take
kallon shi, tunda mama tace tana da bako ta sa hijab,ta
zata Ali ne,dan tama manta da Yace safe,,ido 1 ya kanne
mata,, dai dai Baba ya fito zai tafi,yai mai sallama,, Ya
dawo da kallon shi kanta,,Ta zauna tana mai mamakin jin
sallamar shi da Baba kamar sun San juna,," Ina kwana,, yai
mata wani kallo, ta kauda kai tana murmushi,,A hankali
tace"Allah sa ma kai break irin wannan sammako,,ta dan
harare shi,, yai murmushi,Tare da kama ciki, halamar
yunwa..Ta make kafada,,ya marai rai ce fuska,,"Wajen
Baba nazo,kuma na dace,,harma ya ban auren ki,harda dan
duko kai a hankali kamar mai rada,,Ta kara dukar da
kanta,,kan ta tashi ta debo mishi abinci,,ta zauna,,kunun
gyada ne mai cous cous, yasha madara da lemon tsami,sai
Doya da kwai,,Ya kalle ta yana nuna dakin mama,,yana yin
halamar kar ta fito,,Tai dariya,,Ya dau cup din kunun yakai
baki yana kara kallon dakin mama,ita dai sai dariya take
mishi,,ya rintse ido,dan jin dadin kunun,ita kwa da sauri ta
waro ido, ya bude ido a kanta,fuskar shi ba yabo ba
fallasa,zatan ko bai mishi dadi bane,Yace"Hope ke kika
dama,,ta
.
** *SOME PAGES IS MISSING* **
.
Ta daga mishi kai tana sunne kai,, "Tunda Baba ya sanar
dani zuwan ka da abunda kazo nema wajen shi na amince
maka,,." Hafeez, buri na ka cika a gun Abba,,Ta kallo shi,"
I'm inluv with you than I ever was...I love you too Hafeez,,
Da sauri ta rintse idon ta da murmushin kunya, dan jin wata
kunya da bata San tana da ita ba ta rufe ta,, Kallon ta yake
yana murmushi,, kai shikam baiga abunda Sa'a ta rage shi
ga mace da yake son aure ba.. " Kunya " "Addini: "Class"
Kyauu " Da Iya kwarkwasa.. Shikam ya gode Allah, Sa'a ta
mishi komai da ta so shi.. "Tnks much My Unique,,Yaushe
zan turo a mini Tambaya?? Baki ta fara kunshe wa tana
dariya kadan kadan,Tuni ta so zautar dashi,.. Yau sun buga
luv,tamkar kar su rabu, Dakyar ta samu ta gudu gida dan
magriba tayi,,Ashe haka "So" din yake??..Ashe Haka
masoya suke ji amma a baya take ganin wautar su??..ita
kam indai haka ne,toh itama sai ta sarrafa zuciyar ta, dan
gujewa so mai zafi,,Ji take kamar dama ta girma ne da son
Hafeez,,
.
Mama ma sai da ta gano yau Sa'a na cikin farin ciki
matuka,,Dan komai ta ke sai kaga tana murmushi ita
kadai,,. Shikam daga nan wajen Zahra yaje dan cika
hukuncin Hajiyan shi,Da Tasleem ta sanar mata murna fal
ranta,Wai yau Hafeez ne yazo gidan domin ta??.. Suna
zaune bayan ga gaisuwa ta kasa ce mishi komai,dan jinsu
take wani iri.,Shikam kallon ta yake yaga ta ina ta Gaza,,
sannan mey Sa'a ta fita?..Ya kada kai,, "Amm Zahra
magana nazo muyi ta fahimta,. Ta kallo shi fuska
sake,,.Yace"Nasan kinji maganar ba ke kadai zan aura
ba,,ina fatan tun yanxun ki rike ta yar uwar ki tun kan azo
ga batun zama,,dan Sa'adatu she's simple, baki da
matsalar zama da ita.. Tuni Annurin fuskar ta ya kau,,tai
tsagal ta mike," Ya Hafeez kar muyi haka da kai,,Ban San
wata Sa'adatu ba kai na Sani,,sannan ni kishiya,wallahi
kishiya na dauke ta, ba Wai yar uwa ba..akan mey an gama
magana tashin farko ka watgazan tsari..Kallon ta kawai
yake yana murmushi,, Sa'an shi kawai yake tuno wa,mace
mai Iya lafazi da kawai ci,,Akallah a haihuwar kaji zai haifi
Zahra,amma dan fitsara shi ta tasamma aka tana mishi
haka..Kyale ta yai sai da tai mai Isar ta harda
hawaye,kamin ya taka mata birki.
.
Tuni ya hade rai,, Yace"Bafa shawarar ki nazo nema ba da
zakimin fitsara,aure na da Sa'a kuwa zan Iya cewa shi yafi
zame min dole,,so tun wuri kisan inda kika dosa,dan gaba
bazata mana kyau ba,,.Nan ya barta tana ta kuka,A ganin ta
magana ya fada mata, wato ita auren ta dashi bai zama
dole ba??,,.Mamyn tata ta shigo dakin ganin Ta fito daga
parlour tana kuka,.Lalle yar ta tana da aiki a gaban ta
ja,don tana son tusa kanta a inda bata kwarjini, tasan
tabbas kukan ta bazai rasa nasaba da Hafeez ba,, Gashi ta
nace da sauran dangi sai anyi auren nan,amma tana
tausaya wa rayuwar auren yar tata data ki jinin kishiya
...
Soyayya ake yi tsaftacacciya a tsakanin Hafeez da Sa'a, a
yanxun kam ya maida gidan su Sa'a kamar gidan su, tun
yana jin nauyin zuwa har ya ware,,sai dai abu 1 dake kawo
musu cikas Ali,,Ali ya nace sai Sa'a,, tashin farko yazo da
Baban shi Wai a bashi Sa'a,, kai ranar tai dariya har taji ba
dadi,,sai a ranar ta kara tabbatar da Lalle Ali ba tsaran ta
bane,, duk da Abban yaso tun wuri hakan ta faru,bai rufa
wa mai gidan nashi ba ya sanar shi Sa'a Nada Miji,,sai dai a
bawa Ali hakuri,,dake shi Dattijo ne mai dattako ya amince
da Allah baiyi Matar shi bace,amma shifa Ali fir yaki daina
zuwa,,duk da ko yazo ba kula shi take ba,da yaga baci ya
dawo gori,inda alkawari ai Baba bazai ki bashi auren ta
ba,kodan muhallin da Abban shi ya basu,,Take Sa'an
tace"Indai wannan gidan kake wa toh ka kwantar da
hankalin ka,amma aure ne ka kara lalata shi,dan ka nunan
kai ba na kwarai bane,kuma dole mubar muku gidan Ku...
gori har yaje kunnen Baba,.Tuni ta bawa mutanen da suke
mata haya Notice, ta hau gyaran gida,,shi Baban bai zata ta
dau zafi haka ba,,sai ranar Laraba bayan anyi da wata tazo
Wai gobe zasu tashi,,da fari Baban dariya yake mata,sai dai
ganin ta fara parking yasa ya tsayar ta,,"Sa'adatu ba fa Ali
ya bani gidan nan ba,kinga bai kamata muyi wa Alhaji haka
ba,, tace"Baba ai ko ba gori yaci karan nan ka yarda mu
shiga gidan nan, Ina da gidan zama,amma fur kunki zama
ciki,sai dai nasa haya,Baba chan gashi na zamani,nan na
kasa,ya kamata inn ka samu dama Baba kai amfane
ta,,kawai ce mishi zakai tashi zakai,daga baya ni nasan
abin yi...Duk da haka Abban bai yarda ba,sai dai kamar
yadda ta fada Washegari ta dakko mai katuwar Daf, Baban
baya nan aka fara kwasar kaya,sai gidan Sa'a,, gida ne mai
daki Uku,,biyu kana na,daya katon parlour, duk da baida
wani girma,amma na bulo ne,kuma na zamani,daya dakin
mai bandaki a ciki nan ta jera wa su mama kayan su da
gadon ta,tasa aka sa carpet a pparlourn da manyan
tuntu,,sai fridge da Katuwar TV,,Ita kuma ta hular da katifa
da sauran tariki cen ta..Lalle gaya wa mai zuciya,bamai
Dukiya ba,,,sai da kudin account dinta yai kat..
.
Baki sake su Baba suke kallon Sa'an,basu isa musu ba,dan
har kuka ta sau musu,,Mama ta lallabi Baban,,ta kira
Fadeela ita tazo,Gidan ya musu dai dai,Dan tsakar gida ne
mai dan fadi kadan,anyi mishi siminti,suna da ruwan
su,komai dai dai sauki akwai shi,Fadeela ma tai farin ciki
sosai,,. Da yamma Baba ya sanar da Alhaji cewa sun
tashi,yai hakuri abinne yazo musu a bazata,,yai mishi Allah
sanya alkairi, ai gida kam nashi ne duka,zai yi duk yadda
yaso,sai yazo ganin gida,,.yaji dadin yadda ya fahimce shi
kwarai,yai mishi kwatancen inda suka koma,.kan ya dawo
yana fada ma su mama yadda sukai,Sa'a tace Baban ya
bata mukullin tsohon gidan toh,za ai mishi aiki,zuciya 1 ya
bata,yana mai shi musu albarka. Tai ma Hafeez text, cewa
sun tashi da address, dan tasan zai Iya zuwa bai same su
ba,,5da rabi kuwa yazo, yana ta yiwa mama murna,,da
Allah sanya alkairi,, Nan take sanar shi ai Sa'a ce ta tada
ballin sai sun tashi,ba shiri,,yai murmushi, Yace "Toh ya
kikai da yan hayar cikin??Da mamaki take kallon shi, Ya
akai yasan nata ne?,Sai da suka je parlour yana yaba tsarin
gidan,komai a saukake, amma da kyau,,yadda suka zauna a
Chinese carpet din ma ya kayatar shi,ya jin Gina a tun
tun,kamar wani basarake,,nan ta sanar mishi abinda Ali
Yace, " Shine na basu Notice, bawai kora na musu ba,tana
murmushi, ya kada kai, "Good,kin min dai dai,nan din tunda
ba na uban nashi bane naga kafar mutum,,Tuni ta hau
kunshe baki tana dariya,,Fadeela ta shigo suka gaisa,yana
mata itama Allah sanya alkairi,.. Alhaji yazo daukan Fadeela
yaga gida,,yana ta son barka,,nan yai wa Sa'a zata ga
gudun mawar shi,,. Ko minti 3 ba ai da tafiyar Fadeela
ba,Ali yazo,Baban shi ne Wai Yace yazo yaga gida kan
suzo,,Allah yasa baban baya nan,Sa'a tace ya jira ta a waje
toh,,Da dariya suka fito,da ka gansu kasan suna cikin
nishadi,in ran Ali yai dubu ya baci,,a zuciyar shi yana,,"shifa
kota ya ya sai ya samu Sa'a, atoh, yama ji da kyau,,.
.
Ba ko magana ta mika mishi key, Ya karba yana kallon ta,,.
Hafeez Yace" Ganan keys na gidan naku,,an bar muku shi
sarkin yan gori,,en ya zamo last da zan kara ganin kafar ka
a gidan nan,, dan bazata mana kyau ba,,Suka juya Sa'a na
daga mishi hannu da shakiyanci,,ya kulu Iya kuluwa,,.
Direct Baban shi ya kaima key in,,. Washegari sai gashi
yazo da kanshi ba'asi,, Baban ya kira Sa'a,ba ko dar ta
korowa Alhaji bayani,kan danshi ne ya Goran ta musu,Alhaji
ya girgiza kai, "Sa'a in banda abinki, ai ni nai kyautar nan ba
Ali ba,,Ya ajiye musu kan ya basu hakuri,tare da sanar shi
zai ga Alin. Sa'a sun gama schl,sai Attachment,Zancen aure
sai karfi yake,yayin da Zahra sai baudewa take,Da son abun
Sa'a take attachments din,daga dan wannan sukai sha'awar
daukar ta bayan ta gama.. Ansa bikin su zuwa Hafeez din
ya gama ginin shi,,Duk bangaren kowa na shirye shiryen
biki
.
Matsala 1 da ta fara fuskan ta shine kana nan maganganu
da dangin Hafeez suke a kanta,,dan sau daya da ya taba
kaita ta gano basa yi da ita,,tun daga ranar ta kudiri wani
abu a ranta,burin ta kawai Allah kai Damo ga harawa.
Makarantar zama da Miji mai mata ta bazama nema,,duk
wani wa'azi mai kyau da ma'ana, mai taken mallakar Miji
Sa'a Nada shi a waya,,duk wasu littattafai da tasan tabbas
zata kara Sani akan su ta neme su,, Matakin farko data fara
shine Bincika yanayin kayan Dakin da Hafeez yake da
muradi,cikin wasa sukai abinsu,nan kwa bai son satar amsa
tai ba,,a haka in fira tai dadi a wasa da wasa sai da tasan
mai Hafeez yafi so na daga abinci, sutura,color, best
perfumes da sauran su,,kan ma ta shiga ta gama karantar
daga A har Z.. Tanan tai wa Zahra zarra tun kan su
shiga,ita kullum batta dabara sai ta yaya zatai Hafeez ya
zama nata ita kadai??
.
Duk abinda aka sa mishi lokaci toh tabbas zaizo da
sannu,babu wanda yakai Hafeez da Sa'a farin ciki, duk da
Zahra tana farin ciki, amma Sa'a ce ta tsokane mata
ido,,ganin har yanxun yadda yake rawar kafa a kanta,duk
da tayi nasarar sanya dangi yadda da cewa Lalle Hafeez
zai auro musu karuwa,,kuma tabbas sun yarda,,. Hakan
yasa dai dai da lefen ta a dangin Hafeez din sai yan tsirirai
ne suka kai,,yai kaya na azo a gani,duk dunsu ba
banbanci,,,Ware kunya Sa'a tai ta hau gyaran kanta da
kanta,,.Tsohon gidan su sukutum ta maida gidan gyaran
ta,Tun kamin sati da biki ta kammala duk wasu jeka ka
dawo na hidimar ta,,ta hada nutsuwar ta waje guda,,dan
kwarai tunda taji wa'azin Malama zuwaira ta dau
darasi,,don tabbas itama ta fahimci yawancin amare basa
cikin nutsuwar su ake kaisu gidan Miji,,kenan duk wani
gyara da za'a miki kadan ne zai tasiri a gare ki,dan komai
yana bukatar nutsuwa.. Kaflas din fenti babba tasa aka
nemo mata madarar shanu,dan tasan takamar da za'a
gwada mata kenan su Zahra, dangin Fulani,tasha tai wanka
..,sai da tai ta wankan amare na Lalle kullum a daura Dana
madarar shanu da turaren Durot,,,Wata kwararriya ta
samu,tazo har gidan tana biyan ta,,su fresh Nonon Rakumi,
Su ganyen Tumfafiya,tai,duk wani sirri ta nemo su ta hada
anyi mata,kan satin biki yazo in ka kalli Sa'a tamkar wata
yar black Indian nan masu kyau,sai shining jikin nan
yake,ga wani dan karan kamshi da laushi da fatar ta
take,,kai kace daga Maiduguri ta fito,,Dan tun kan biki tasa
wata Qawar ta yi mata hanyar wani mai hada turarurrukan
mata masu kyau da kamshi,,Dan ita akwai son
kamshi,musamman na turaren wuta.. Yau Juma'a, ta kama
gobe za'a dauro auren su Hafeez da Matan shi,sun shirya
kyatattiyar Dinner,, Kowa ya halatta Sa'a kawai ake jira,,in
kaga ango sai wage baki da ido yake yaga ta ina zata
ratso,,Zahra an hakimce a kusa da Hafeez, an Gaji da kyau
itama,,gashin nan an zubo shi baya,duk da taiwa Hafeez
din kyau amma shi burin shi yaga Sa'an shi,,duk sunyi
waya tace suna wani room ne a hotel din 5 mint's,,
.
Hargowa da fadin MashaAllah shi ya juyar da hankalin
Hafeez da Zahra,,tafi ake mata,ganin gasu Tj yan kanan
Bodyguards dinta na unguwa sunyi wankan bakaken suite,
kowa yasha bakin glass,yaran sunyi kyau matuka,sun
shassha kunu su a dole masu tsaran Aunty Sa'a, sai abin ya
kayatar,Ga nan Qawayen ta yan karya da wanda sukai
Turkish suma sunsha kyau,,sanye take cikin wata doguwar
Riga ta net Golden da ratsin Orange,, sai ta temaka wajen
kara haskaka mata fatar tai wani yellown kyau,,ga wani
arnan Hill Orange da Pose ,,sai dan mayani data rufa a
gefe,,Fuskar nan ta Gaji da kyau,Ko Zahra sai da ta firgita
ba Hafeez, dan tunda biki ya karato ta fara gyara da dogon
hijab da Nikaf take fitowa su gaisa..tayi kyau ainun,,ga
wani tsadadden murmushi da take sakar wa,sabanin Zahra
da ta nemi fara'ar ta ta rasa,,Hafeez ya tafi duka,,A ranshi
fadi yake"Tsarki ya Tabbata ga Allah,, Ya ma manta da
jama'ar hall din kamar an tsikare shi ya tashi,ba ko kunya
yai wajen ta,,tana ganin haka tai saurin dukar da kai tana
murmushi,Tuni aka hau flashes ta ko'ina,, in ran Zahra yai
dubu toh ya baci.., haka suka jera har mazaunin su.

No comments

Post a Comment