Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

*** *BARIKI IYAWA PART 11* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 11* ***
.
Dakyar Abba yasha kan Hajiyan,ita sai fadi take batace
haramun bane,,kawai Zahra take so ita daya..sai da ya
burkice mata kan suka dai dai ta,,Zahra ai zabin ta ce,.Da
Zahra taji tuni kuka ya karu,,shikenan kuma. Da Yamma
Zahra ta tartara inata ina ta zatai gida,,ta kudiri kuma ba ita
ba kara zama gidan su Hafeez Wai dan shi,,lokacin da suka
fito baya nan, kuma sarai tasan dan su ya bar gidan dan kar
ya kaita,,ga Drivern Abba sun fita,kawai suka je a tsayar da
Taxi,,itama da kyar suka samu da mace a ciki.,,Yace zai
kaita kan ya kaisu,,a rashin babu suka shiga,,har akaje
unguwar da za'a ajiye wacce suka tarar a Taxin,sun zo
zasu wuce wata a tsaye da wani da yai musu kama da
Hafeez a tsaye sai murmushi yake,,ta motar ta daga wa ta
tsayen yatsu tana kiran "BARIKI Ba..Zahra ta kalli Tasleem,"
Ba ya Hafeez bane wannan kuwa??..da sauri suka kara
juyawa,akai Sa'a dai dai itama Sa'a ta daga wa ta motar
yatsu,ya dan juyo ganin Taxin da ta wuce,sai dai baiga na
ciki ba,,Tasleem tace"La,wallahi shine Aunty Zahra,, tuni ta
cika ta batse dan gane da wa yake tsaye,wato itace wacce
zai gama su tare??mai Taxi na yin kwana ya sauke dayar
suma suka sauka,Zahra zatai kwanar Da sauri Tasleem ta
ruko ta,,"mey zakiyi Aunty Zahra?? Ki bari man muji wacece
tukun mu karasa tunda wannan ta San ta,.sai a sannan ta
dawo hankalin ta, mai Taxi Yace in bazasu tafi ba su bashi
kudin shi, da sauri suka sallame shi suka bi bayan Kaltum
da zata shiga gida,,. "Baiwar Allah,, ta juyo da fara'ar ta"
Aa,Baku tafi ba?sukai yake, "eh, tambaya muke pls?ta
gyara tsayuwa," toh muje daga ciki,Zahra ta kada kai,
"Aa,muyi anan,." Dan Allah wace wacce muka wuce yanzu
da wani a tsaye kika daga mata hannu?tai murmushi, "au
Wai BARIKI?? Yar Duniya ake fada miki,badai saurayin ki
bane ba koh?Tasleem ta kalli Zahra da ke mai maita sunan
BARIKI.
.
Dake uwar surutu ce tuni ta hau fadi ba'a tambaye ki ba,."
Ai in saurayin ki ne toh wallahi ki hakura dashi,dan ba mai
Iya ja da BARIKI a fagen nan,,indai har ya shiga hannun
BARIKI toh sunan saurayin ki "Sorry ",nan ta hau basu
labarin irin kasa wasu da tai da samarin su,Ku harda Matan
aure bata bari ba,,campaign na siyasa tai kadai aka mallaka
mata dankareriyar mota da katon gida,tuni suka waro
ido,,.ta cigaba" wallahi ina baki shawara ki ma bar
mata,duk da batta gwani ita..haka tai ta basu karya da
gaskiya,tuni Zahra ta tsure,Tasleen kira take "Shikenan yaya
ya hadu da karuwa,.ji yadda yake wage mata baki,.bata
Ankara ba sai gani tai Zahra na hawaye..tai Dede kwanar
tana leken su,, a dai lokacin da Sa'an ta miko wa Hafeez
waya,sai wani yauki take irin na yan Duniya.. Yayin da
gogan baki tamkar gonar audiga,,dan ko bata furta ba a
formular da Kunal ya bashi ya gano da son shi a tattare da
ita,,dan yau ba hade rai, mai makon haka ma sai murmushi
take mai dan cike da kunya,. Ina,Zahra in ta cigaba da
tsayuwa a tana kallon su zata Iya hawan ruwa,tuni ta juya
Tasleem ta daura bayan ta tana waiwayen wannan
BARIKIN, kai ko ita ta tafi da imanin ta wallahi,, duk ba Wai
kyau tafi Zahran ba amma da gani ta fita sanin kan ta
Duniya..sai dai ba yadda za ai Yayan su ya kaso musu yar
BARIKI.. Tab, bari suje gidan. Gidan su zahran da ba'a je ba
kenan sukai gida,in banda hawaye ba abinda Zahra take,
Tasleem tayi tayi ta kasa dai nawa,. A parlour suka tarar da
Hajiya,itama ta tsunduma tunanin Wai Hafeez da mata
2,,kukan Zahra ne ya dawo da ita,,tuni ta hau tambaya,, kan
Tasleem tace komai Zahran ta amshe,tana kuka tana
tsarawa Hajiyan. " Kuma Wai yar BARIKI fa Hajiya?da sauri
ta waro ido waje,,tace "wallahi Hajiya Wai ma sunan ta"
BARIKI,Tasleem tace"Hajiya kinga yadda yake mata dariya,
tamkar wacce ta mishi ishara da Aljanna.."Ni ya ishe ni
haka,,ni dama nasan yaron nan ba haka kawai yake
ba,,Ashe yana chan an dauke hankalin shi, kuma Wai
Karuwa yar BARIKI?? Ta kallo Zahra,"yi shirun ki,bari baban
naku yazo,,bazata sabu ba Sam,,da hankali na bazaa auro
min sirika yar BARIKI ba wallahi..
.
Hafeez na dira gida Hajiya ta fara sauke mishi,,da tsananin
mamaki ya sauke kai kasa,yasan bai isa wanke kanshi da
Sa'a ba yau a wajen Hajiya,.."Saboda ta dauke maka
hankali har ka gagara ban bance tsakanin Aya da
Tsakuwa,,Yace"Hajiya Wallahi ba haka Sa'a take
ba,,wannan sunan daban,kuma.."Rufe min baki shashasha
kawai,, in baka Sani ba toh ka Sani yanzun,Zahra kawai na
Sani,ba ruwana da da wata BARIKI,Macen kwarai ce za'a
kirata da sunan BARIKI ta amsa??. Mita take har Abba ya
ritsa ta bayan ya dawo,,yana hawa ta bi bayan shi. Hafeez
ya juyo yana hararar Zahra da Tasleem,,"Yaushe na zama
abin wasan Ku da har zaku Bini a baya?? Sukai
tsurutsuru,ya nuno Zahra da yatsa, "Bari ma kiji,wannan
abun bazai hanani auren Sa'a ba,sannan Gobe kisan nayi ki
tattara ki koma gidan Ku,,.Ya tashi yai daki,,ta bishi da
ido,Tuni ta fara hawaye,abun harda gori? Ita kwa mita
tsinana a zaman gidan banda takaici?Bari taje gida,har
gidan Aunty salma zata,karya ne a gama ta zaman aure da
wata,,. Shikwa yana shiga daki ya jawo waya,ita kanta
Sa'ar haushi take bashi,,dan dazun suna tsaye Ali yazo,,
saboda tsabar rashin so Wai tace mishi " Excuse me"?,.
.
Tai wajen Ali,duk da bai ji mey suke cewa ba,amma ya
gano wanda suke waya dazu ne,tuni koh ta kanta bai bi ba
ya shiga mota..shine kuma yana zuwa Hajiya ma ta sauke
mishi,.Yai dan tsaki, Lalle sai ya dage,,Ashe da gaske take
Wai Bai karbi soyayyar taba? Toh ya take so yayi??Ya fidda
zuciyar shi kan Yace"Sa'adatu I luv u,komai??ya sake
tsaki,,a hankali ya furta "Sa'a matsala,.. Ita kuwa tunda taga
Hafeez ya zuciya ta rasa sukuni,gashi ta kasa kiran shi, a
nata tunanin ajin ta zai zube,. Tai kwafa,amma Alin nan sai
ta sa kafar wando daya dashi zai ki yayi zuwa wajen ta, in
takamar sa gidan na uban shi ne,toh itama tana da gidan
daya taka wannan na bulo ma..ta kara tsaki,,ta juya ta dau
waya kan ta tashi zaune..tai dailing numbern Hafeez din,da
sauri ta katse,," Oh God,,ta rike kai,"Wai Sa'a mey ke damun
ki ne akan Hafeez??Tun farkon haduwar su da Hafeez
shine kadai Namijin da ta taba mafarki,,shine kadai wanda
ta taba chachar baki dashi dan Dabarar ta takare, shine
kadai ke sawa ta bata lokacin ta wajen tunanin shi, Shine
kadai a yanzun in suna tare take jin wani nishadi kadan
kadan na shigar ta..Sannan yanxun yayi fushi ta damu,ji
yadda take gwara kan maza,manya da kana nan su,,yau 1
wanda taki jini ya hana ta sukuni.." Ya Ilahiii", "Mey kenan
hakan yake nufi?? Ta kalli agogo 9,kwanciya tai kamin ta
hau Mishi text da bata San ma ta fara ba..Da sauri ta goge
na ban hakuri ta rubuta. " Shine ka tafi ba koh sallama??
Tasa halamar shagwaba.. Tai murmushi, kan ta kishingida.
Text yaji ya shigo wayan ya kara tsaki kan ya kwanta,chan
ya jawo wayan,dan yana zata koh Alert ne na contact na
Zane da aka bashi,,da mamakin shi yaga Sa'ada,.yai
murmushi, take yaji kuncin shi ya yaye,tuni yai reply.. Taji
text itama,tai murmushi dan tasan shine,."Munyi fada ai,, tai
murmushi da har hakwaran ta suka fito, tai rufda ciki kan ta
mishi Reply.. "Ai bama fada..Triple sorry" .
.
Shima yai rubda cikin yana karanta wa,,yai murmushi,,"No
banyi ba..ban Aron minti 5 naji muryan ki sai nai sorryn..ya
tura..chan itama ta bude,,tai murmushi tana duba sling,,
kan ta kada kai tai reply"An baka. Ringing 5 tai kan ta katse
ta dauka da sallama,,yai Jim,,tace"koh ba'a yafe ni ba??ya
sauke wata ajiyar zuciya,, kan Yace"u know what?? Kina da
dadin muryar sosai,,Tai murmushin jin dadi,. Kan tace
"kaima haka?..sai kuma ta datse harshen ta da hakorin
ta,bata ma San ta furta ba,,yai murmushi,." No,ke ai ta
daban ce,,Tace"Koh,? Yai shiru,"Sa'ada waye Ali nan ne??tai
dan murmushi,, "Dan mai gidan Baba ne,,Yace" ehm,sai mey
kuma??ta kada kai "shikenan, Yace" Ba So??tai Jim, kan
tace"akwai,.tuni ya mike zaune,,sai ta kara da"Shi yake
kayan shi amma,,ya sauke wata ajiyar zuciya da taji ta,,
Yace"Toh Ni fa Sa'a?? Tai shiru tana,tace"Hafeez ne
kai,Yace"ehm?Toh ana son Hafeez din?? Tai Jim,gaban shi
ya fara faduwa,,ita kwa murmushi take a hankali,. Sai da ya
kara magana,"Ko har yanzu ban karbi Son ba Sa'adatu??
Wallahi believe me,I am madly, deeply in love with you
...Sa'a I really Love you, en u know?? Tun farkon haduwar
mu na kamu da son ki,sai dai a wancen lokacin ban San so
bane Sa'ada, nasan dai ina tsananin kishi na ganki da gyale
shara shara,,sai naji zuciya ta na tafasa,,in na tabo ki
mukai ne kawai nake samun relief.. Tunowa take da lokacin,
tabbas tun ganin Hafeez na farko ta ji sauyi a tare da ita.
.
Ya cigaba, "Kin tuna ranar da na watsa miki lemon
strawberries a jiki??? Tuni ta rintse ido dan tuna wa da
wannan rana,ba zata manta ba har kuka tai,,.ya katse ta"
nasan ke a zatan ki dan tsokana nai,,Ya girgiza kai, "Ganin
mai shagon nan fa nai yana ta kallon ki sai ga kin dame
Riga,ga nan gyale a kafada,,shine yasa na tashi na harare
shi yana sosa kai,kan na baki baya na watsa miki,nasan
Ummi ta gani,en dole ki nemi agaji,sai kwa gashi ta baki kin
suturce jikin ki da abayar ta,,.Jin shi kawai take..ta katse
shi da" Mey zakace da Marin da kamin kuma??Ya sauke
ajiyar zuciya,, "Sa'adatu.. Taji kiran har kwakwalwar ta,.,"
Naga shigo war ki kina ta wani yauki,,ga kayan sun dame
ki,ga wani Wai shi gyale da kika dakko kin maka shi a
kafada,baki sa maraba da wacce ta fito haka,,ga duk kusan
ke ake kallo,,amma ke na fuskan ci baya ma damun
ki,haka kika kutso taron nan kika shigo fa,,da zaki kula,da
zaki gano tsabar haushin da nake ji, hararar ki nake tayi ko
zan samu saukin zugin raina,,ina fa jin wani a yan uwan su
Ummin yana cewa wani "Woow,,she's Beautiful!! Kamar na
cire babbar Rigar Aminu na rufa miki naji,.sai dai nasan ba
laifin shi bane,,naki ne,. Dan na rage zugin dake raina na
koma baya,,juyo war da zanyi naji ki kusa dani,kuma kamar
ki shige min jiki,,bazan boye miki ba,a lokacin nan ji nan
kamar ma na rufe ki da duka,,dan na tsani mace mai
chudanya da maza,.ban Ankara ba naji saukar sanyi a jiki
na,,...Yai shiru tare da rintse ido,,." Sa'ada ban so tuno
Marin nan da na miki,, duk da har gobe kowa yana kallon
kece kika mare ni in kika cire Ummi da Aminu,tanan kawai
na gode Allah. Tai ajiyar zuciya,, Lalle sai yanxu ta kula da
kishin da Hafeez ke nuna wa,,ya katse ta,, "Da fatan kin
gamsu zaki yafen,..yaji shiru,, Ashe kudin ya kare.. Shi
yana ta zuba ko warning din bai jiba,,ya dau wayan Glo ya
kira..dai dai zata kira..
,
Yace" kiban dama gobe nazo gida da safe,yanxun dare
yayi,. Ta kada mishi kai,,"Ok.. Yace"Mey toh zan samu??tai
Jim,dan bata gane nufin shi ba,,sai tace*Sai dai kazo
gobe,,Yace"Promise?,, ta kada kai "Promise.. Haka suka
sallamar kowa ya kwanta da tunanin Dan uwan shi..barin
Sa'a yau da taji duk wwani haushi ta daina ji na Hafeez,, a
ganin ta ko a haka ya barta ta gamsu da Lalle So ne ya
Jawo Haka.
.
Tun safe Zahra tai niyar gida,.ko jiran Tasleem batai ba,,
tana zuwa ta zube a tsakar dakin Mamyn nasu,, Aunty
Sadiya ta kallo ta,"Lfyr ki kuwa??Kinzo kin wani zube min
ba koh sallama??Tuni ta marai rai cewa Mamyn tasu tana
hawaye,, "Mamy,,Na shiga 3 wallahi,,.sai ta barke mata da
kuka,,Da jin haka ta waro ido waje,, Ta tashi ta kamo yar ta
ta,tasan dai tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Amma sai ta
tambaye ta" Meye kin shiga 3??
.
Nifa ban son wautar nan taki ta yan fari?? Ta lafe jikin shi
tana kuka,,"Mamy Wai Fa Hafeez mu 2 zai aura,, kuma ya
rasa da wacce zai hadani sai yar BARIKI mamy,, Mamyn tai
Jim,ita dai dama wannan hadin na Zahra da Hafeez kwata
kwata bai mata ba,,duk da Hafeez da yake a gurin ta,amma
tasan ba abunda yar tata zata tsinta a gidan shi sai ciwan
rai, toh amma ita batta da wani power a gidan,tunda itace
auta a cikin gidan su kakanin Hafeez din,, haka itama aka
mata wannan auren hadin,, gashi za'a sake da yarta tilo
mace,dan duk sauran kannen Zahra maza ne,,. Rarrashi ta
fara,,"Toh meye ne abun kuka anan Zahra?Ta sake magana
cikin kuka"Mamy Abban su fa Wai ya yarda,,Hajiya ce kawai
tace bata yarda ba,, Dan Allah mamy ki Taimaken ki samu
Fodio da maganar,tunda Abban yana jin maganar shi,,.
.
Ta sake fashe wa da kuka"wlh mamy ban son zama da
kishiya.. Da sauri ta kwade mata baki,,ta rike bakin tana
cigaba da hawaye "Wato kaddarar ki a hannun ki take koh
Zahra?Ta hade fuska mamyn,,"Da hankalin ki kike furta irin
kalaman da wanda basuyi makaranta ba kadai ke fadan
shi??tai kwafa,"Sannu autar mata,,Toh ki sata a
ranki,,sannan ki daura damarar zama da ita tun yau,.Da
sauri ta kalli Mamyn nasu,, "Anya mamy kuwa tana son
ta??,,Bari Abban yazo,shi zata tsara mishi komai ya shige
mata gaba,,.kamar tasan tunanin yar tata,,sai ta dawo mata
Nasiha,,kan tana saukaka kishi,dan duk yadda ka dauki
Kishiya toh fa a haka take zuwa maka,," Ki duba ni da
auntyn Ku,da yawa mutane basa gane kishiya tace,dan
tsabar muna zaman mutunci da girma ma juna..ki cire
wanna akidar taki tun wuri Zahra,,Dan kin fini sanin halin
Hafeez, bare akan abinda yake so,,sannan duk Family nan
suna matukar yaba dashi,hakan yasa suka zaba mishi ke
suna ga da hankalin Ku zai zama daya..kar ki fara bata
rawar ki da tsalle tun yanzun,, tai ta mata,amma ina,ita
gani take Mamyn bazata gane ba,. Karfe 9 da rabi yana
gidan su Sa'a,, ita duk daukan ta wasa yake,yai katari kuwa
Baban su yana waje,,Har kasa ya gaida shi cikin girma
mawa,. Da fara'a Baban ya amsa,,Take yaji Hafeez ya
kwanta mishi,dan ba kasafai yaran yanzun suka Iya girma
ma manya ba haka..Ya kalle shi da fara'a, "Hala ka wani
kake nema??Ya sunkuyar da kai kasa cikin girma mawa,, Da
halamar kunya Yace"Baba dama wajen ka nazo,,Yace" Toh
mu shiga daga ciki,Ya Sosa kai,Daga zaure ya cire musu
farar kujera,suka zauna,sai leken cikin gidan yake ko zai
hango sahibar shi,,Baban ya dan kula da hakan,"Allah dai
yasa lfy?Ya sunne kai kasa cikin kunya,"Amm Baba sunan
Hafeez, muna chan kasa daku kadan, dama,Amm,Sa'adatu
na gani Baba,shine nake Neman izinin fara Neman auren ta
a gun ka.
.
Baban yai murmushi, a ranshi yana ambaton "Allahu
Akbar,,Lalle zabin shi Dana Sa'an shi Yazo,,Dan duk wanda
zai cika sharudan mulunci na Neman aure Hafeez ya
fara,.Bai manta zancen shi da Sa'a ba akan Tara samari ba
na aura,,bai manta amsar da ta bashi a lokacin ba,," Baba
duk saurayin da ya fara zuwa Neman aure na wajen ka toh
ya cika sharuddan aure na,,ka shaida hakan Baba,,nasan
zaka fini sanin dawa na dace Baba..Da irin kalaman nan
Sa'an take kara shiga ranshi,, ga daga gani daga gidan
mutunci Hafeez din ya fito,,Ya kada kai, "Tabbas kayi
abinda ya dace Hafeez, hakan ya nunan daga gidan da ka
fito,,Allah yasa alkairi a ciki,,.Tuni ya fadada fara'ar shi
yana sunne kai,, Baban ya tambaye shi iyayen shi,ya dai
gamsu da duk bayanan shi,sai kuma bincike ya rage.
.

No comments

Post a Comment