Featured

Own A Blog Like This
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - usamaumarusman1@gmail.com

*** *BARIKI IYAWA PART 10* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 10* ***

.
Sai bayan magriba ta tashi,.har lokacin Shima yana
nan.,tun fitar ta yai musu sallama,,sai dai da mamakin shi
tana ta tada mota taki tashi, sai tsaki take kamar ta rufe
motar da duka,,sai dai ba hali,,yai murmushi kan ya karasa
wajen,,ta dago kai ta kalle shi kan ta cigaba da abinda take,
yace"May I?ta dago,da har zatai gardama, kuma dai sai ta
fito.
.
Shima yai yin Duniya taki fitowa,, ya fito tare da rufe
motar,duk ta wani marai rai ce mata,har magana take mata
kamar mai jinta,shi dariya ma take bashi,,yace"Muje na
sauke ki, ta kallo shi,ta girgiza kai taga yana murmushi,sai
ta kule.tace"No tnks,, kan ta kauda kanta gefe..ana haka
Aminu ya fito za shi wani gu ya dawo,,turus ya tsaya kallon
su,," Ya na ganku anan?Baku tafi bane?ya kallo Hafeez
daya harde hannu kawai yake kallon ta,, tai dan tsaki"taki
tashi ne,,ga dare nayi,.ya kalli Hafeez, "Toh ka sauke ta
man,in yaso gobe na taho miki da ita in an gyara,,ya kallo
ta," ko ya kika ce?sai ta dan sachi kallon Hafeez din,,"Nifa
Aminu da dai..ya katse ta "ki saman a mota,, yai baya kan
ya bude motar, ta kallo Aminu,, ya daga mata kafada
halamun bata choice,. A mota duk ta takura kanta,,ta gyara
gyale, ta murza zobe, da sun hada ido tai saurin dauke
nata,,ganin yadda ya wani seta mirrorn yana facing nata,shi
dai sai murmushi,ya dan kallo ta lokacin da yake kwanar
wani gu,," zan karbi sako pls,, ta kalle shi tare da kada kai,,
Ya karbo suka fito da mutumin,, wanda zai bashi kwangilar
Zane na gini..ya kallo shi, "mutumin kace da amarya kake
tafe?da sauri ta kallo shi, ya wani kashe mata ido.. Yace"
Madam ina wuni,.da yake ta amsa,.tana nanata amarya a
zuciyar ta,, bari ya shigo,,ta kauda kanta gefe,har ya
shigo,.ya kalle ta yana daura belt,"Muje koh? tai mai banza,,
yai murmushi,, ta kallo shi, "Nice amaryar? Ya kallo ta yai
dariya,," no, ta kada kai "yauwa,.ya sake kallo ta" Uwar gida
ce ai,,da sauri ta kallo shi,, ya daga gira,,"yes,.
.
uwar gida ko kinfi son amaryar? Tuni ta hade rai,. "Malam
kaja ni ko ka sauke ni,,uwar gidan wa??Shima ya hade
fuska kamar gaske,,"uwar gida na man,baki ta sake,tama
kasa furta komai,ga ya wani hakimce ya tsare gida,,kawai
ta juyar da kanta,,.sun kusa zuwa wayan ta yai ringing,, ta
duba number ne,sai da ta kusa tsinkewa kan ta daga,a
gadaran ce ciki ciki take maganar,," wane Alin?.. Tai Jim,ta
kallo Hafeez din, Shima ita yake kallo yana kallon titi, sai ta
waske dan ta bashi haushi"Oh,na gane,ya akai toh?..wayar
ya warce dai dai sunxo kwanar daza ta kaisu gida,,ya kai
kunnen shi a kai kai ce,,"Tana tare da mijin auren ta ne,, kai
hakuri ka Adana Tarihin sunan ka,,ya kashe wayar tare da
ajiye wayar bai ko kalle ta ba yai parking,. Lalle man din nan
akwai karfin hali!..baki sake kawai take kallon shi,,wannan
irin tusa kai haka,.jin bata fita ba yasa ya kalle ta, shi take
kallo,yace"na sauya miki ne hala??ta maka mishi harara
kan tai waje,.da sauri yace"wayan ki,.ta warta, zata fita ya
dago glass din.."wannan fa?Shima ta warce,kan tace "ba'a
Sani ba,.sai kuma ta manta jakar ta,. Ya kunshe dariya,,
tuni ta kara kuluwa,.zata shiga gida ya fito yace" Sa'ada,.da
sauri ta juyo da zummar masifa,,jakar ya mika mata yana
murmushi,. Sai kuma dafe kai"Ya salam,.sai kunya ta
kamata,,toh saurin mey take haka??ta tako zata karba tare
da juyar da kai ganin yana murmushi,. Maimakon ya
bata,sai yai baya da ita,ta juyo ta kalle shi, suna hada ido ta
dauke kai,."ban man,.yai shiru,,ta sake kallo jakar ba tare
da ta kalle shi ba,yai murmushi, "Toh yaushe zan dawo?ta
sake kallon shi a kai kai ce,." Kamar ya??da abinda ya rage
kuma?ya kada kai, "kwarai,da abunda suka rage da yawa,.
Ta kallo shi da rashin fahimta ,,ya daga mata girar shi,." Ai
in kinga abubuwa sun kare,toh tabbata uwar gida ta
tare,.gaba daya kamar an kulle mata baki taji,. Ta sake
mika hannu ya kautar, "in kina son na baki ki fadan yaushe
zan dawo??da kaguwa tace" Gobe,.sai kuma tai shiru,.ta
rasa meye dalilin kasa kallon idon Hafeez da tai,.murmushi
yai,kan ya mika mata jaka,.tana karba da sauri ta arche
gida.
.
Harta shiga yana Binta da kallo,ya sauke ajiyar zuciya,.Lalle
ba makawa a kamu da ciwo,wanda yake tunanin koh shine
So din,.ya sake ajiyar zuciya kan ya tada motar shi yana ji
da nishadi. A bangaren ta itama haka,kwance take sai juyi
take a gadon ta,ta rasa dalilin da yasa yanzu ta daina jin
zafin shi kamar kullum,ga wani dan karan kwarjini da ya
fara mata yanzun da da bata gani,, ta furzar da iska kan ta
kara juya wa dayan gefen, buguwar zuciyar ta ya tsanan ta,
lokacin da ta tuno yadda yake mata wani kallo wanda ta
kasa fassara shi,, kai ta girgiza, tana mai rarrashin
kwakwalwar ta da ta daina tunano mata Hafeez,. Tai adu'a
tare da gyara kwanciya. Shima hakan ce ta faru,.sai juyi
yake a katifa, sai yayi kamar ya kira ta,sai kuma yai
murmushi, a yau kam,ya rasa nutsuwar shi, ga wani fara'a
da yake tamkar gonar audiga,ya duba agogo,8 da wani
abu,ai dare bai ba,. Waya ya dauka ya danna kiran
Aminu,.yana dauka ya fara mishi tsiya,"Tsiyar gauro
kenan,bai gane dare yayi,,yai dan karamin tsaki,"Gargadi
zan ma Malam, wallahi BARIKI ya fita a bakin ka,ka kirata
da Sa'adatun ta sak.. Dariyar keta ya fara mishi, har sai da
yaga ya fara kuluwa ya dan sarara, "I knew it,.
.
Dama nasan Biri yai kama da mutum,,kuma ance in kaga
Kare na shinshina Takalmi,toh dauka zai,Lalle Abokina ka
afka da yawa,.ya cigaba da dillika dariya,Hafeez yace" kai
fa dan iskan gari ne,mey na afkawa dayawa? Yace"Son Sa'a
kuwa,da sauri yace"So?yace"kwarai kuwa,tun farkon ganin
Sa'a nasan ka afka son ta,amma ka tsaya a haushin ta ne,.
Shidai Hafeez mamaki yake,tunda ya kashe waya yake
murmushi, Ashe sone hakan?Toh amma ya akai bai San So
ba shi?abu daya ya Sani yana da muradin auren Sa'a,. Tuni
ya dau waya ya fara tsantsara mata Text,a lokacin da itama
bacci ya gagari idon ta, kwakwalwa ta kasa daina turo mata
hoton Hafeez.,Ji shigowar Text yasa Ta bude ido,takai
dube kan wayan,ta mirgina ta dauko,tuni taji bugun zuciyar
ta ya karu, duk da murmushi take yayin karan tawa,
"Hafeez.. A hankali ta furta,,kan tai tsam tana tuna wani
abu,.
.
Washegari kowa ya tashi cikin farin ciki,musamman
Hafeez, duk da bata mishi ko reply ba,amma yasan ta ga
sakon shi, har Hajiya sai da ta kula da hakan,binshi da kallo
kawai take,, ya zauna a kujera.,lokaci lokaci yana dan duba
waya ko zaiji shigo war amsa.."Ni Hafeez, yau ko mafarkin
Aljanna kai ne haka?Yai murmushi, "ko daya Hajiya,.ta
kada kai,. Ana haka su Zahra suka fito ita da Tasleem,suka
gaida shi,ya kallo Zahra,yana tunanin mey yasa bai jin
komai game da Zahra irin na Sa'a??..ya lumshe ido, Sa'a
kam ta daban ce..da sauri ya bude ido jin Tasleem tana ga
abincin shi,.
.
Zahra sai satar kallon shi take,Hajiya na kula dasu,ba tasan
mey aibin Zahra ba a gun Hafeez, duk irin zaman da zatai a
gidan bazai taba kallon ta a Wai wacce zai aura ba sai dai
qanwa,kai shi manta wa ma yake da wani batun auren ta,,
koda kuwa zai aure ta, toh gini ma na mata 2 yai,daya a
sama da turakar shi,daya a kasa da dakin yara,kai da kaga
gidan kaga na zaman mata 2,. Hajiyan ta kalli Zuhra tai
mata halama da hannu suje daki,.ta yafico Zahra sukai
chan,kan ta kallo Hafeez,." Wai ina zancen mu ya tsaya ne
Hafeez??.. Ya kallo ta da rashin fahimta,. Ganin haka yasa
tamai ta gwari gwari,"zancen ka kai da Zahra man,ko har
yanzun baka fahimta ba?? tuni yaji gaban shi ya fadi,sarai
yasan Hajiyan su akwai zafi,musamman akan lamarin
family, yasan bai isa cewa bazai auri Zahra ba yanxu,dan
yana son Sa'adatu,, sai dai yana tsoron hada Zahra da Sa'a
a matsayin Matan shi,.. "Hafeez,. Tunanin mey kake haka
ina magana??..Ya Sosa keya," Am Hajiya,yana nan, sai dai
dama ina da magana..da sauri ta daga mishi hannu,,"idan
har maganar auren nan ne,toh anyi an gama Hafeez,
.
. Ba zaka maida mu ya'yan ka ba fa,.Yace"Bashi bane
Hajiya,.Amm dama wata ce naga, kuma,.kuma..ya kasa
karasa wa, ganin yadda Hajiyan take kwada mai
harara,,."kuma mey? eyeee, nace Kuma mey?kana nufin ka
fasa auren Zahra dan kaga wata bare chan??ko mey kake
nufi??.Da sauri ya girgiza kai, "aa ba haka nake nufi ba,,..
Dama,sai yai shiru ganin Abban su ya sakko,ya sunne kai
yana gaishe shi, da fara'a yake kallon shi,."Mey kuma ya
faru Kaida Umman taka nake jiyo fadan ta tun a sama
haka??Tai kicin kicin da fuska,,"Ka zo dai ka jiye wa kunnen
ka,dama duk kai ne mai daure mishi ai,,toh wallahi karan
nan bai isa kauce wa auren Zahra ba,,yai murmushi, kan ya
kallo Hafeez," Ya akai Hafeez?? Ya kallo Hajiyan da sai
harara take binshi dashi,.ya fada mishi yadda sukai da
Hajiyan, "kuma fa Abba ni duka zan aure su fa,,..A zabure
Hajiyan ta tashi," kana nufin mata 2 zakai??!ya sunkuyar da
kanshi,,ta kalli Alhajin, "ka dai ji da kunnen ka koh?ta nuno
Hafeez," Toh baka isa ba,babu wacce zaka hada da
Zahra,,Abban yai mishi halamar yai shiru,,ta kallo
Alhajin,"kafa sa baki, dan karan nan zamu bata da Hafeez
kwarai..tai sama tana bam bami,.
.
Zahra da tazo jikin kofa tana zatan zancen auren su zatai
mishi Hajiyan ta soma kuka,, Tasleem ta taso,"lfy Aunty
Zahra?Ta zaunar ta akan gado,,"Tasleem mey na rasa da
Ya Hafeez bai sona ne Wai??duk zaman nan dan shi nake
yi,amma banda amsa gaisuwa ba abinda ke shiga tsakanin
mu,,shine yanzu zai ce zai hada ni da wata ya aura dan
tsabar rashin so??.,,,, ta barke da kuka abin
tausayi,Tasleem tace"Kut,,wata kuma?ta daga mata kai,.
Tasleem ta sake matsowa "Kwantar da hankalin ki,ni nasan
Hajiya bama zata soma yadda ba,,Wai mata 2,,kuma kar ki
ji kom,ya Hafeez na son ki,kawai dai miskili ne na karshe,,
ni nasan indai da Hajiya,toh ke kadai ce Matar shi,. Ta
share mata hawaye,.sai lokacin ta dan sararawa kanta..
Shikwa Bayan Abban yace zai ma Hajiyan magana,yai ta
murna,abincin da bai ciba yai daki,,wata zuciyar tace" Toh
kai da kake ta murna, tukun Sa'an ma ka same son ta ne??
sai kuma yai Jim,Toh fa,tanan gizo ke sakar, shifa bai ma
San ya ake cewa a wajen budurwa ba bare in yaje ya tsara
ta taso shi,,yai kamar ya kira Aminu,abokin shi ne ya fado
mishi,wani dan Delhi da sukai school a Hyderabad, ya tuno
yadda yake tsara yan mata,duk mai ji da kanta a school din
tasan da zaman Kunal,.tuni ya kira ya kora mai bayani,,yai
dariya Shima son ran shi, dan jin Wai Hafeez ya fada tarkon
so,,Yace mishi ai ba'a koya zance,sai dai ya dan bashi
wasu formula,.

No comments

Post a Comment